Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

yi?" ita dae bama taji shi ba suka k'arasa inda suke zaune sannan tace tana Kallan Ayrah "Yawwah ki zauna, nan ne kusan permanent seat namu dan tunda muka zo anan muke zama" murmushin yak'e Ayrah tayi dan har ga Allah wajen be mata ba, dan kuwa a baya ne bench d'in nasu yake, se dae ta nemi waje ta zauna kawae. Basu suka koma hostel ba a ranar se wajen k'arfe 6, dan haka suna komawa Ayrah ce ta fara fad'awa toilet tayi wanka dan sosae ta gaji tana fitowa ta zira doguwar riga mara nauyi ta maeda hijab d'in ta tayi sallah kana ta nemi waje ta zauna still dae da hijab d'in , dan haka kawae tunda tazo d'in tafi jin ta comfortable idan ta saka hijab d'in. "Toh mu dae kinga had'a girkin mu muke, kawae kowaccen mu zata kawo abincin tane duk abinda muke so se mu dafa muci, kema ayi hakan dake?" Ruks ce me maganar tana kallan Ayrah, seda ta d'an yi jimm, saboda haka kawae taji basu wani kwanta mata can ba musamman daya kasance hirar su gaba d'aya rabin ta ta samari ce, tun jiyan kuma da tazo ba taji wata a cikin su tayi maganar karatu ba, amma kuma suna da kirki yadda suka tarbetan kawae ma ya mata dad'i dan haka se tace "Tohm.." "Ohk guys..me zamu dafa?" Ruks ta fad'a tana kallan su su duka, ta6e baki Jidda tayi kana tace "Kawae mu dafa indomie, dan ni yunwa nake ji" "Nima dae kam" Bahijja ta fad'a itama, mik'ewa Ruks tayi ta nufi inda kayan abincin nasu ke ajiye cikin d'an k'ank'anin lokaci ta d'ora musu Indomien, sanda take zuba Maggi a ciki ne ta jiyo muryar Jidda na fad'in "Ke ni tun d'azu nake so mu tattauna akan shigar Doctor RK ta yau, amma wannan Abeedar ta mana k'erere, don Allah befi wancan satin kyau ba?" ajiye maggin hannun ta Ruks tayi sannan ta juyo tana rik'e ha6a kana tace tana murmushi "Umhum wallahi ke kam ki bari kawae.., shi fa kowacce shiga yayi naga alama kyau take masa, wallahi guy d'in ya had'u iya had'uwa" ta fad'a tana jan baki kamar wadda taci abu me yaji, daga nan fa hirar tasu ta soma, maganar tasan nan dae da kullum ita suke yau ma dae ta san suke, da alama basa gajiya da hirar tasa kamar wani abinci "Wae Bahijja meye haka naji kinyi shiru?" Jidda ta fad'a tana jefa mata harara, seta yamutse fuska kana tace "Ke kam ki bari kawae, kae na ke ciwo" itama tayi maganar tana yamutse ta ta fuskar "Toh Allah ya sawwak'e.. Ayrah ki sauko muci abinci" Ruks ta fad'a tana kallan Ayrah dake kwance kamar me bacci, se a lokacin ta tashi dan daga inda take zaune tun d'azu ji take kamar ta tashi ta musu duka, tana jin kamar tace musu sun ishe ta da maganar wannan mugun mutumin, haka dae ta mik'e ta sauko suka ci abincin. ...... Washe_gari k'arfe 7:40 dukan su suka gama shiryawa har da Ayrah, yau ma cikin hijab d'in dae ta shirya kamar jiyan, suka fito tare suna tafiya su Jidda na hira yayin da ita dae tayi shiru kawae, a dae_dae inda ze sada su da ajin nasu dukkan su suka ji wata murya na fad'in "Ayrah Ibraheem Khaleel.." kusan a tare dukan su suka juya, se duk suka tsaya suna kallan mutumin daya kira sunan nata kafin suka kalli Ayrah, itama da kallan rashin sani take bin sa dan tunda take bata ta6a ganin fuskar ba "Sak'o aka bani na kawo miki.." yayi maganar yana kallan ta "Sak'o kuma? Ni ban sanka ba" ta fad'a cike da sakarcin nan nata, se yayi murmushi kana yace "Ehh Hajiya, dama nasan baki sanni ba ae amma daga makarantar ku ne aka turo ni" seta d'an samu relief amma duk da haka tace "Toh mene?" "K'awa ta zo mu tafi 8 ta kusa, kuma kin san yau yana da first period a farko" Ruks ta fad'a tana jan hannun Ayrah, seta d'an maraeraece fuska sannan tace "Uhmm daga makaranta ne fa.." "Kinsan yadda za'ayi? Mu bari muyi gaba ke kuma kiyi sauri kiji abinda ze fad'a, but u should make sure dat kin shigo class before 8" seta jinjina kae tana bin su da kallo sanda suke wucewa ajin kana ita kuma ta dawo da duban ta inda mutumin yake, kafin tace komae yace "Kayan abinci ne dana sakawa Hajiya akace mu kawo miki daga makaranta" seta tsaya ta cigaba da kallan sa kamar me tunani se kuma tace "Kaya kuma?" yace "Ehh.." "A'ah Abba ya siya min" ta fad'a tana girgiza kae, seya sake yin murmushi kafin yace "Ehh wannan ae daban yake Hajiya, kuma kinga daga makaranta ne" seta d'an yi jimm kafin tace "Toh zan kira Yah Sadeeq na fad'a masa tukunna" mutumin ya sauke ajiyar zuciya yana mamakin wannan yarinya haka amma gudun kada ya takura ta shinshino wani abun ya sanya shi fad'in "Toh kira shi" "Ae ba yanzu ba.." tayi maganar cikin turo baki duk da bata san tayi hakan ba "Meyasa?" "Sauri nake" ta fad'a tana gyara tsayuwar ta, seya fesar da iska daga bakin sa kafin yace "Toh shikenan, bari na jira ki" ba tace komae ba ta juya zuwa ajin nasu, dae_dae lokacin da wani d'alibi yayi sauri ya shige cikin ajin, seta ji dad'i hakan na nufin 8 ba tayi ba kenan, dan haka da confidence d'in ta ta sanya k'afa cikin ajin, tayi wajen taku 5 a cikin ajin tana jin dad'in yadda yau ta samu class d'in, se dae ga mamakin ta seta jiyo kamilalliyar muryar sa na fad'in "Go out.." seta ta6e baki a ranta tana sak'a may be tana shigowa k'arfe 8 d'in ta cika, gashi nan har ze kori wata ko wani, dan haka ta cigaba da tafiya har zuwa sanda ta samu waje ta zauna tana lumshe idanun ta kana ta bud'e, abinda ya bata mamaki yadda taga kusan idon kowa na cikin ajin akan ta yake, seta sake kallan wani 6angaren taga still dae ita suke kalla, a hankali tabi jikin ta da kallo zuciyar ta na bugawa tana fatan ba wani abun ne ta manta bata saka ba, ta kalli jikin ta hijab d'in ta gashi nan har kusan k'asa, ita kanta kawae dae ta duba d'in ne amma tasan da akwae abinda beyi ba a jikin ta su Jidda zasu fad'a mata, inda taga kuma sun maeda hankali suna kalla itama ta d'aga raunannun idanun ta da suka cika taff da k'walla saboda wannan kallan da suke mata duk ya rikita ta, a hankali idanun ta suka sauka akan kamilalliya kuma nutsatsiyar fuskar sa me cike da wani irin zati, da kwarjini na musamman har bata san sanda ta d'auke idanun ta da sauri ba tana dafe k'irjin ta daya wani irin buga a lokaci guda "Kurma ce?" yayi maganar kamar baya so kuma ba tare daya kalli en ajin ba "Dake fa yake.. Ki tashi ki fita kin makara.." wata dake kusa da ita ta ankarar da ita, seta d'aga kae cikin rashin fahimta ta kalle shi dae_dae sanda shima ya d'ago nasa firgitattun idanun

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70