Skip to content

Chapter 54

Chapter 54

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

ya d'aga hannayen sa ya sak'ale su a k'irjin sa sannan ya zuba mata idanun sa gaba d'aya, k'ok'arin komawa gefe ta soma yi ba tare data kalle shi ba har lokacin fuskar ta a had'e "Ina zaki je?" ya fad'a a nutse har lokacin idanun sa na kan ta, bata dae kalle shin ba se d'aga kae da tayi kawae ta kalli gefen sa sannan ta sake had'e fuska tace k'irjin ta na d'an bugawa saboda yadda ya tsare ta da idanun sa "Gidan mu zan tafi!" ta fad'a lokacin da wasu ruwan hawaye suka taru a cikin idanun ta, cike da fatan kada ya kawo wata maganar dake nuni da k'in zuwan ta "Gidan ku kuma?" ya tambaya yana d'an d'age girar sa guda d'aya yana cigaba da bin ta da wani irin kallo saboda yadda yaga ta masa wani shahararren kyau kamar ba cikin tashin hankali take ba, ba tace komae ba tunda tasan ae yaji abinda ta fad'a d'in dan haka ta sake k'ok'arin tafiya "Toh ya zakiyi da aure na kuma da yake kan ki?" "Zan fad'awa Abba na abinda ya faru, nasan zasu warware auren gaba d'aya.." ta fad'a har lokacin fuskar ta a had'e, murmushi ya saki daga inda yake tsaye sannan ya d'an lumshe idanun sa kad'an kana yace "Ohk je ki.." bata sake cewa komae ba ta sauke ajiyar zuciya sannan tabi gefen sa ta fice daga d'akin, bin ta yayi da kallo yana mamakin ta, sosae yake mamakin ta musamman idan ya tuna yanda suka fara soyayyar su hankali kwance amma rana d'aya ta sauya kamar ba ita ba, be ta6a tunanin zata ta6a juya masa baya ba, ya d'auka zata taya shi fafutuka ne da kuma nemo hanyar da zesa iyayen su su amince da auren su, se yanzu yaji inama kafin ta fita ya tambaye ta dalilin sauyawar ta? Koda yake yana da 80% sure cewar maganar iyayen ta kawae tabi yasa ta chanja masa, yasan tana k'aunar sa fiye da zaton sa, amma kuma soyayyar iyayen ta ta danne tashi, amma meyasa tun farko bata chanja ba se daga baya? Meyasa haka? Shi kad'ae yake tunanin sa kuma yasan babu me amsa masa dan haka kawae ya sauke hannayen sa sannan ya fita daga cikin d'akin, yana hango ta sanda ta fita zuwa k'ofar gidan, seda ta fita d'in sannan ya k'arasa ya hau motar sa ya jata shima ya fice daga gidan, a nutse kuma cike da takatsantsan yake bin ta a baya, baya so ta fahimci bin ta yake dan haka yake bin ta a hankali, itama a hankali take tafiya kamar wadda k'wae ya fashewa a ciki, se dae hakan na da nasaba ne da jikin ta da har lokacin take ji be koma mata dae_dae ba, a haka har ta fita titi ta tsaya tana kallan motocin da suke wucewa, se a lokacin ta tuna babu ko sisi a tare da ita, amma koma menene gwara taje gidan idan yaso seta kar6a ta bawa me Napep d'in, dan haka babu 6ata lokaci ta shiga tsare adaedaeta, daga cikin layin ya dakata da motar tasa yana ganin ta har zuwa sanda wata k'atuwar mota me kyau ta dawo da baya tayi parking a gaban Ayrah, d'an runtse idanun sa yayi yana jiran ganin abinda ze faru next, dae_dae lokacin da mutumin cikin motar ke k'ok'arin fitowa ita kuma ta gama fad'awa me Napep d'in data tara inda zata je, babu 6ata lokaci ta fad'a ciki dae_dae lokacin da mutumin ya gama fitowa daga cikin motar, wani banzan kallo Rk yabi shi da shi yana jin yanda zuciyar sa ta fara tafasa lokaci d'aya, tana shiga kuma me Napep d'in yaja, mutumin na shirin yin magana yaga yaja adaedaetar sa "Kashhh!" ya furta yana bin adaedaetar da kallo sanda suka wuce shi, se a lokacin Rk yaja motar sa ya fito daga cikin layin har lokacin yana d'an kallan mutumin yaga ko zeyi wani abun bayan nan, se dae yaga beyi ko k'ok'arin bin su ba, se a lokacin ya d'an ji sanyi sannan ya cigaba da bin ta, yana cikin driving d'in wayar sa ta soma ringing, kamar baze kalli me kiran ba se kuma ya kalla "Muneerah" shine abinda ya bayyana akan screen d'in wayar, runtse idanun sa yayi zuciyar sa na cigaba da wani irin zafi, kawae seya kae hannun sa ya kashe wayar gaba d'aya sannan ya jefa ta kan kujerar me zaman banza ya cigaba da driving d'in sa yana jin yadda ran sa ke kuma 6aci. Har cikin layin su ya shigar da ita seda suka kusa kaewa k'ofar gidan su sannan tace "Ya isa" babu 6ata lokaci ya tsaya ta sauka, se kuma ta d'an yi shiru tana tunanin yadda zata shaeda masa seta shiga gida ta kar6o kud'i, a ranta tana fatan Allah yasa me mutunci ne, ganin dae babu wata mafita ya sanya ta fad'in "Bari na kar6o kud'in don Allah.." kallan ta yayi sannan yace "Toh shikenan amma kiyi sauri don Allah" sauke ajiyar zuciya tayi kana a hankali ta juya, a hankali ta sauke idanun ta akan gidan nasu, se ta shiga kallan sa kamar yau ta fara ganin sa, a hankali ta lumshe idanun ta sannan ta taka k'afar ta cikin soron gidan nasu tana jin yadda bugun zuciyar ta ya k'aru lokaci guda.. Mhiz Innocent..... ✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 035 ___A hankali ta cigaba da takawa zuwa cikin gidan har zuwa sanda ta k'arasa cikin tsakar gidan, Abba da Yah Sadeeq suna zaune a tsakar gidan, yayin da Umma ke fitowa daga cikin kitchen hannun ta d'auke da tea flask ta k'araso ta ajje a gaban su Abba "Sannu da k'ok'ari" Abba ya fad'a, seta d'an yi murmurshi sannan ta fara k'ok'arin mik'ewa, dae_dae lokacin data d'ago d'in yayi dae_dae da lokacin da Ayrah ta shigo cikin gidan kuma idanun ta suka fara sauka akan Umma, da gudu ta k'arasa bata yi wata wata ba ta rungume ta tana fashewa da wani kuka me tsuma zuciyar me sauraro, lumshe idanu Umma tayi sanda Ayrahn ta rungume ta, lokaci d'aya taji zuciyar ta ta wani irin karyewa, babu 6ata lokaci itama ta rungume d'iyar ta ta, tana hana kan ta yin kuka kada su had'u su zama su biyu, Abba da Yah Sadeeq kallan su kawae suke yi babu wanda ya iya cewa komae har zuwa sanda Ayrah ta gaji da kukan ta soma durk'ushewa akan k'afafun ta, rik'o ta Umma tayi kafin ta kae k'asan se suka k'arasa zubewa a k'asan, a hankali taja sheshshek'ar kuka sannan tace "Umma!!" kallan ta Umma tayi kamar me son gano gaskiyar al'amari daga cikin idanun Ayrahn, idan ta tuna yanda Ayrahn ta fice daga gidan ba tare da izinin su ba se taji kamar ta sake ta ta tashi tayi tafiyar ta, amma kuma ta rasa dalilin da yasa ta kasa aekata hakan, bata amsa kiran da Ayrahn ta mata ba har zuwa sanda Ayrahn ta kalli Abba da har lokacin kallan ta yake tace "Abba na!" "Daga ina kike?" shine abinda ya fara fitowa daga bakin Abba yana tsare ta da idanu, seda ta d'an lumshe idanu nan take

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70