Chapter 53
Chapter 53
har da sabon hijab ta k'araso tana bin ta da murmushin dae, seda ta ajje kan gadon sannan tace "Bari na kawo miki abinci" ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa "Na k'oshi ni" tayi maganar a cunkushe, kallan ta Hameedah tayi ganin yanda ta wani d'auke kae ya sanya ta girgiza kae kawae ta fice daga d'akin, seda ta fita sannan Ayrah ta d'auki doguwar rigar abayar ta zura kana ta d'ora hijab d'in akae sannan tayi sallah ta mik'e ta cigaba da tsayuwa tana jiran dawowar sa, tun tana tsayen har ta gaji da tsayawar seta nemi gefen gadon ta d'an zauna tana share k'walla, yanzu kam idan har ya k'ara awa 1 bezo ba zata tashi ta tafi gidan su ne, ita kuma takaddar ya rik'e ta karya bayar, se yayi ta zama da auren shi kad'ae, ita ba abinda ya dame ta. ... A kujerun da suke ajje a compound d'in gidan suke zaune kowanne kan kujera d'aya, kallan sa Yaseer yake sosae yana nazarin yanayin sa, daga d'azu zuwa yanzu se yake ganin kamar ya sake chanjawa "Wae me yake faruwa ne Rk?" d'an murmushin yak'e Rk yayi sannan yace bayan ya yatsina fuskar sa "Yaseer, ina cikin matsala fa" "Matsala kuma? Wace iriyar matsala? Ko da yake da farko dae ya kamata koma wacece waccan yarinyar ka maeda ta gida tunda kaga dare na sake yi" kallan sa Rk yayi sannan ya d'auke kan sa bayan ya sauke ajiyar zuciya yace a nutse kamar babu abinda ke damunsa "Mata ta ce!" cigaba da kallan sa Yaseer yayi yana so ya gano ko dae abokin nasa ya fara shan k'waya ne? A iya sanin sa abokin nasa baya shaye shaye amma se gashi yau yayi magana irin ta en shaye shaye, se kuma ya saka wata dariya kana yayi shiru yana cigaba da kallan sa "Tsaya mana pls, ni fa wallahi ba maganar raenin hankali nake maka ba" murmushi Rk yayi yana kallan Yaseer dake magana da iya gaskiyar sa, seda ya d'an lumshe idanun sa kad'an sannan ya bud'e a lokaci guda kana yace "Am serious fah, mata ta ce ta sunnah" yayi maganar yanzu ma a nutse "Look Friend, don Allah joke apart.." yayi saurin katse shi, dan kuwa ya gaji da jin wannan tatsuniyar tasa, gyara zama Rk yayi sannan ya fara da "Nima ba wasa nake ba Yaseer, auren ne ya kasance kamar shirin film, ni kuma nayi kasada nayi aure ba tare da izinin su Abbu ba" daga nan ya shiga labartawa Yaseer d'in yadda auren nasu ya kasance, har ya k'are labarin Yaseer bece dashi uffan ba kawae kallan sa yake cike da mamaki, shima kansa daya gama bada labarin be d'aga ido ya kalli Yaseer d'in ba, sun kae wajen minti 2 a haka kafin Yaseer ya sauke ajiyar zuciya yace "Lallae Rk, aure ba tare da izinin su Abbu ba? Baka tunanin wannan wani babban kuskure ne ka aekata?" "Ya zanyi Yaseer? Ina kallo wani ya aure ta a gaba na? Ko kuma na maeda ta gida su aura mata wani bani ba?" ya fad'a yana kallan Yaseer da har lokacin mamaki yak'i barin sa, cike da mamaki Yaseer yace "A'ah na kasa gane duk wannan abin, meyasa iyayen ta zasu ce baza ka aure ta ba? Idan ma akwae wani dalilin ina ganin kamar Abbu ne zece baza ka aure ta ba saboda wannan dalilin koh?" ya k'are maganar da sigar tambaya, ta6e baki Rk yayi, shi kan sa a wannan wajen be san abinda zece ba, be san dalilin hakan ba, da farko kamar Ayrahn na bayan sa duk da yadda iyayen su kace baze aure ta ba, se kuma daga k'arshe gaba d'aya ta juya masa baya "Amma meyasa ba zaka tambaye ta dalilin ta na juya maka baya ba?" Yaseer ya katse masa tunanin da yake yi kamar yasan abinda yake sak'awa a ransa, ajiye numfashi yayi kafin yace "Tak'i bani wannan damar Yaseer, tun farko abinda naso inji kenan a lokacin ne kuma ta birkice min, yanzu kuma bani da k'warin gwuiwar tambayar ta dalilin hakan tunda ga abinda ya faru" jinjina kae Yaseer ya shiga yi cike da gamsuwa da maganar Rk d'in amma duk da haka yace "Amma yaushe zaka sanar dasu Abbun?" seda ya d'aga ido ya kalli Yaseer d'in sannan yace bayan ya girgiza kae "Ba yanzu ba Yaseer, maganar da nake maka aure na da Muneerah rana ita yau ne, me kake tunanin ze faru idan na fad'awa Abbu maganar nan?" ya k'are maganar yana d'an ajje numfashi, shima Yaseer sauke ajiyar zuciya yayi sannan yace "Hakane kuma" ya fad'a yana jinjina kae cike da tunani a zuciyar sa ko ze samowa Abokin nasa mafita. ... Tana zaune cikin d'akin a ranta tana k'iyasta adadin lokacin da take jira ya cika ta tashi ta fita daga d'akin, wani irin bacci me dad'i ke ta sakad'ar ta tun d'azun, se yakice shi take yi ta k'arfi da yaji amma se dad'a lumshe idanu take yi kamar wadda tasha kayan maye, ko cikakken minti 1 bata k'ara ba ta 6ingire kan gadon se bacci. Sosae Rk yaji dad'i lokacin da Hameedah ke sanar dashi Ayrahn bacci take yi, dan haka ya d'an samu relief, hatta maganin ta ma bebi takan a tashe ta tasha a daren ba, a cewar sa goben seta sha tunda dae yanzu ta samu bacci, ko ba komae ze d'an samu nutsuwar zuciya kafin goben daya san me raba shi da ita se Allah. A hankali ta shiga bud'e narkakkun idanun ta da suka mata nauyi, har ta gama bud'e su tarr cikin d'akin, da sauri ta mik'e zaune tana cigaba da kallan d'akin, kallan agogon dake manne a jikin bangon d'akin wanda ya harba k'arfe 6:00 tayi, seta sake kallan agogon kamar me k'aryata abinda ta gani, se dae ga mamakin ta hakan dae ya sake nuna mata, wannan wane irin bacci ne? Bata san sanda hawaye ya soma sintiri akan kuncin ta ba, ta mik'e da wani irin sauri ta dirga daga kan gadon, sabon brush d'in data gani akan gadon ta d'auka ta fad'a toilet d'in tayi alwala tayi brush sannan ta fito tayi sallah tana istigfari cikin ran ta, bata san wane irin nannauyan bacci ne haka ya d'auke ta cikin k'ank'anin lokaci irin wannan ba, seda ta idar da Sallahr sannan ta sake fad'awa toilet d'in tayi wanka kana ta shirya yanzu ma cikin abayar data gani akan gadon ta maeda hijab d'in jikin ta ba tare data shafa komae akan fuskar ta ba ko ta shafa wani abu me kama da mae ba ta k'arasa ta ta6a k'ofar d'akin, cikin sa'a kuwa se taji ta a bud'e, sauke ajiyar zuciya tayi sannan ta k'arasa fitowa daga cikin d'akin, ba tare data kalli ko'ina ba kawae tayi hanyar fita daga cikin d'akin, daga inda yake zaune kan dinning shi da Yaseer ya mik'e da sauri dan tunda ta fito yake ankare da ita, bece da ita komae ba kawae ya k'arasa a nutse zuwa gaban ta, dakatawa tayi da sauri ganin yanda ya tsaya d'in dab da ita, Yaseer dake zaune shima ya mik'e ya bar parlourn gaba d'aya, se a lokacin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70