Chapter 52
Chapter 52
masa kyau akan fuskar sa "Lafiya k'alau Alhamdulillah, da alama dae wannan ce sirikar tamu?" ta fad'a tana kallan Ayrahn, da kallan farko ta mata ta hango zallar kyan da take dashi, wani kallo Ayrah ta d'aga narkakkun idanun ta ta watsawa Hameeda, ita kan ta Hameedan seta gaza gane wane irin kallo ne wannan? Murmushin yak'e yayi dan baya so su sake 6allo masa wani aekin yace yana mik'ewa "Amm Madam.. Pls ga sister nan zata d'an yi wanka ta shirya pls, zuwa anjima zan zo na d'auke ta" duka kallan sa suke yi cike da mamaki, Yaseer yayi k'arfin halin fad'in "Bangane ba?" lumshe idanun sa yayi yana fesar da iska daga bakin sa sannan ya bud'e idanun nasa yana kallan Yaseer yace "Plsss idan na dawo zamu yi maganar, Abbu na jira na" ya fad'a yana fara yin gaba, mik'ewa tayi itama dae_dae lokacin da hawayen da suka dad'e cikin idanun ta suka samu damar zubowa akan fuskar ta, lura da hakan ya sanya shi d'an dakatawa kana yace a hankali yana kallan ta "Ki shirya, ina dawowa se mu wuce.." ya fad'a cikin taushi, ita dae ba tace komae ba se sake share hawayen da tayi yayin da shi kuma ya fice daga d'akin cike da fatan kada ta tubure masa, Yaseer da Hameeda suka kalli junan su cike da mamakin wannan abu, sauke numfashi Yaseer yayi kana yabi bayan Rk daya fita "Malam nifa bangane abinda kake nufi ba, ya zaka tafi kuma ka barmu cikin duhu? Ka fara warware mana wacece waccan d'in kafin ka bar gidan nan" numfashi ya sake fesarwa daga bakin sa sannan yace "Sorry Friend, zance ne me tsayi amma ina gamawa da Abbu nan zan dawo pls" yayi maganar sanda ya bud'e murfin driver seat "Shikenan karka d'au lokaci pls" "In Sha Allah" Rk ya fad'a yana shigewa cikin motar "Ammm pls kada a barta taje ko'ina kamin na dawo" Rk ya fad'a yana kallan Yaseer, yanzu kam kan Yaseer ya sake kullewa da al'amarin abokin nasa, dan haka bece komae ba ya bishi da kallo kawae, shi kuma Rk tunda yasan Yaseer d'in yaji abinda ya fad'a d'in ya sanya shi jan motar, bin sa da kallo Yaseer ya sake yi har ya fice daga cikin layin sannan ya sauke ajiyar zuciya yana komawa cikin gidan, "lallae akwae wani abun" ya fad'a a k'asan ran sa. ... Kae tsaye gida ya wuce zuciyar sa cike da sak'e_sak'e kala_kala, ya k'arasa yayi parking motar sa sannan ya fita ya shige cikin gidan, parlourn Abbu ya wuce da sallama d'auke a bakin sa ya shiga, Abbun na zaune akan kujera yana shan lemo gefe guda kuma yana kallo cikin k'atuwar T.Vn dake manne a jikin bango, seda ya d'auki remote ya rage volume d'in T.Vn sannan ya amsa sallamar Rk daya k'arasa shigowa cikin d'akin, murmushi ne ya su6uce akan fuskar Abbu sanda Rk yace "Barka da wannan lokacin Abbu" "Barka dae likita ya kamata ka samu bacci haka nan" jinjina kae Rk yayi yana yin d'an murmushin kana yace "In Sha Allah Abbu" gyara zama Abbu yayi daga inda yake zaune sannan yace bayan yayi gyaran murya "Wato maganar da nake so nayi da kae ita kan ta tana buk'atar nutsuwa, dan haka da zarar ka gama samun baccin da baka samu ba seka fara shirye_shirye saboda rashin ishashshen lokaci" Abbu ya fad'a yana d'an dakatawa, duk da Rk be fahimci maganar Abbun ba amma hakan be sanya shi cewa komae ba, yayi shiru yana cigaba da saurarar Abbun dan yasan ze warware masa komae ne "Dama magana ce akan auren ka da Muneerah da za'a gabatar dashi nan da sati d'aya" Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 034 ___Seda ya d'au wajen minti 1 bece komae ba yana ta kokawa da zuciyar sa akan zafin da take masa kada kuma 6acin rae yasa ya furta abinda be dace ba sannan a hankali ya d'aga idanun sa da suka sauya kala ya kalli Abbu "Abbu aure ka nemar min hadda tsaeda rana ba tare da sani na ba?" ya fad'a ba tare dama yana sanin abinda ke fita daga bakin sa ba saboda tsananin 6acin rae, da mamaki Abbu ya kalle shi na tsawon sakanni, sosae yayi mamakin jin abinda ke fitowa daga bakin Rk d'in amma seya sake gyara zama sannan yace har lokacin yana kallan sa "Toh ko ban isa bane?" se a lokacin Rk ya tuna abinda ya fad'a d'in a hankali ya d'an lumshe idanun sa sannan ya bud'e a nutse kuma a hankali ya furta "Abbu ka isa.." daga haka ya mik'e cike da sassarfa ya fice daga d'akin, bin sa da kallo Abbu yayi har zuwa lokacin daya gama ficewa daga d'akin sannan ya dawo da duban sa cikin d'akin yana jinjina kae. ... A hankali ya nemi waje ya zauna akan gadon sa idanun sa a lumshe, a karo na barkatae ya sake fidda iska daga bakin sa, hannu ya kae ya dafe kan sa daya cigaba da sara masa, ya kae wajen minti 5 a hakan yana sauke numfashi a jere a jere saboda yanda zuciyar sa ke cigaba da tafasa sannan ya mik'e kamar me tunanin wani abun se kuma ya koma ya zauna, tabbas Abbu na neman sakawa zuciyar sa ta buga, ta yaya ze iya kallan wata matar a matsayin matar sa bayan Ayrah? Be san ta yaya hakan ze kasance ba, son da yakewa Ayrah yana da yawa baya tunanin ko da ya auri wata ze iya adalci a tsakanin ku, toh ta yaya ma ze auri wata? Koda be auri Ayrah ba baya tunanin ze iya auren wata matar ballantana kuma yanzun daya same ta, se dae ga Abbu na neman saka shi auren wata bayan ita, baya so kuma ya d'auki zunubi akan hakan, amma ta yaya ze kalli Abbun ya fad'a masa baya son Muneerah saboda yana da wata matar daya aura ba tare da sanin su ba? Hannun sa ya kae ya cusa cikin kwantacciyar sumar kan sa nan take kuwa ta hargitse seya koma ya kwanta kawae cikin rashin sanin abinyi. ... A 6angaren Ayrah kuwa sanda Rk ya fita daga cikin d'akin seta cigaba kawae da kallan k'ofar kamar me tunani "Muje na kae ki d'akin koh?" Hameedah ta fad'a tana murmushi, kamar ta mata banza se kuma taga gwara kawae ayi komae a yanzu a gama a wuce wajen, dan haka se kawae tayi gaba ta fara tafiya a hankali, Hameedahn seta wuce ta ta k'arasa zuwa bakin wani d'aki tace tana kallan ta "Ki shiga kiyi wankan zan kawo miki kaya seki saka" se a lokacin ta iya bud'e baki tace "Toh" sannan ta shige cikin d'akin, madaedaecin d'aki ne me d'auke da gado, wardrobe da kuma toilet, bata tsaya tabi ta kan d'akin ba kawae ta fad'a toilet d'in, anan d'in ma ba wani dad'ewa tayi ba dan haka ko minti 15 ba tayi ba ta fito sanye da hijab d'in, se a lokacin ta tsaya tana k'arewa d'akin kallo kafin ta d'auke kan ta ta maeda shi zuwa k'ofar d'akin da aka turo, Hameedah ce ta shigo yanzu hannun ta d'auke da riga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70