Skip to content

Chapter 63

Chapter 63

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

hankali, kae tsaye ta ta6a k'ofar fita se ta ji ta a rufe, dan haka ba tare data kalle shi ba ta furta "Ka bud'e min na fita" shiru yayi yana bin ta da kallo duk da baya iya hangen fuskar ta "Don Allah ki tsaya ki saurare ni" kamar jira take seta juyo tana kallan sa, kafin ta fara magana fuskar nan ta ta tayi jajur haka zalika sassanyar muryar ta ta sake rusuna "Babu abinda zaka fad'a min Raj, ka bud'e min na koma gidan mu, kaje kayi rayuwa da wadda kake so nima yanzu bana son ka.." ta fad'a tana jin wani irin zafi da bata ta6a jin sa ba cikin zuciyar ta, zazzafar iska ya fesar daga bakin sa kana ya d'an lumshe idanun sa yace "Ayrah, wallahi Abbu ne ya aura min ita, akwae maganar auren dama tun kafin sake had'uwar mu, don Allah kiyi shiru ki dena wannan kukan wallahi yana nakasta min zuciya" hannu ta saka ta toshe kunnuwan ta, tana ji a ran ta kamar wad'annan d'in kalaman yaudara ne kawae yake fad'a mata, meyasa zeyi mata haka? Meyasa ta yadda dashi shi kuma yaci amanar ta? Meyasa ze had'a ta da wata bayan ita tunda take bata ta6a had'a shi da wani ba, tana cigaba da tare sabon kukan daya taho mata ta furta "Ni ka bud'e min k'ofa na fita.." yanzu kam babu musu ya bud'e mata k'ofar, da sauri ta saka hannu ta bud'e murfin motar sannan ta fad'a cikin gidan nasu, a tsakar gida ta taradda Umma babu 6ata lokaci ta fad'a jikin Umman tana sake sakin wani sabon kukan "Subhanallahi Ayrah.. Meya faru?" Umma ta fad'a tana rik'o Ayrahn dake cigaba da kuka kamar wadda akama mutuwa, bata iya cewa komae ba saboda yanda zuciyar ta ke cigaba da tafasa, haushi da kuma takaeci suna sake cika ta, seda ta gama kukan tsaf sannan ta d'ago tana kallan Umma da zuwa lokacin ta gama rud'ewa da yanda taga d'iyar ta ta na kuka haka "Umma wae aure yaje yayi! Umma ya yaudare ni bansan yadda zanyi ba zuciya ta na dab da bugawa" ta fad'a tama manta Umman ta take fad'awa maganar, da mamaki Umma take kallan Ayrahn kafin cikin k'arfin hali ta furta "Ay..." sallamar da Abba yayi cikin gidan itace ta katsewa Umma maganar da take k'ok'arin fad'a, seta d'aga kae ta kalli Abban, ga mamakin ta seta gan shi sun shigo tare da Rk, maganar sa da Ayrah ta jiyo ne ya sanya ta shirin mik'ewa a fusace tana shirin shigewa cikin d'aki Umma ta rik'o ta "Ki tsaya tukunnah" ba dan taso ba haka ta zauna d'in har lokacin kan ta na kan cinyar Umma kuma har zuwa lokacin zafin da zuciyar ta ke mata be ragu ba, haka zalika ji take kamar tayi ta kukan kar ta dena, sam bata san kuma meya shigo dashi cikin gidan ba, me yake nufin zece mata ta yadda dashi? "Ina jin ka Allah yasa lafiya" Abba ya fad'a bayan ya zauna akan tabarmar dake shimfid'e a tsakar gidan, seda ya d'an yi shiru kad'an kana ya saci kallan inda Ayrah ke zaune sannan yace "Abba dama akan maganar aure ne da nayi yau d'in nan, naso na yiwa Ayrah bayani se dae tak'i fahimta ta, Abbu be san da maganar aure na da ita ba shiyasa, kuma dama tun farko yana da burin aura min ita kasancewar er k'anin sa ce, se kuma yanzu Allah yayi za'a yi auren amma sam bani da laefi Abba" ya k'are maganar a maraeraece dan yana da tabbacin Ayrahn na jin sa, ajiye numfashi Abba yayi sannan yace "Ikon Allah, dama namiji ba dan mace d'aya akayi shi ba, kuma hakan ya sake nuna min kae d'in yaro ne me biyayya, dan haka ka tashi kaje Allah yayi maka albarka.. Ke kuma Ayrah ki tashi ki bi mijin ki dan banga amfanin zaman naki cikin gida bayan da auren ki ba" ya k'are maganar yana kallan Ayrah, da sauri ta d'aga narkakkun idanun ta ta sauke su kan Abban da yayi magana, ita kan ta Umma tayi mamakin maganar Abban, amma shi kam da yayi maganar da alama ko a jikin sa "Abban su.." Umma ta fad'a tana cigaba da kallan sa "Babu damuwa, ta tashi ta bishi d'in" shine abinda Abban ya sake fad'a, ajiyar zuciya Umma ta sauke sannan ta kalli Ayrah dake girgiza kae kamar k'adangaruwa cikin kuka tace "Abba don Allah ka bar ni a gidan nan kaaji" dama saboda hakan Abban yace tabi mijin ta, dan kuwa yasan idan ba yanzun ba nan gaba ma se gwagwarmayar tafi hakan dan haka ya kalle ta yace "Babu komae kinji, ki tashi kije.. Zamu yi komae daga baya" ita sam ba fahimtar Abban take yi ba dan kuwa kishi ya riga ya gama rufe mata ido, duk kuwa da irin bayanin da yayi ita har yanzun bata gamsu ba, kawae ji take yi kamar yaudarar ta yayi. Umma ce ta mik'e ta fad'a cikin d'aki ta shiga had'awa Autar ta ta kayan da tasan zata yi amfani dasu ko kuma ta buk'ata kafin komae ya daedaeta sannan ta fito har ran ta tana jin babu dad'i, a yadda ta bar ta a tsakar gidan a haka ta same ta, zaune ta d'ora kan ta akan k'afar ta tana sheshshek'ar kuka, seda ta fito d'in sannan Abba ya kalli Rk "Ku tashi kuje Allah yayi muku albarka, In Sha Allah zan neme ka ko ta layin Sadeeq ne" sosae yaji dad'in abinda Abban yayi dan haka yace "Nagode sosae Abba, Allah ya k'ara girma" "Ameen" d'ago da fuskar Ayrah Umma tayi tana kallan yanda fuskar ta tayi kace_kace da hawaye, seta girgiza kae tana jin tun yanzu har kewa ta fara kama ta "Kukan ya isa haka Ayrah, ki tashi kije zamu yi waya Uhmm?" Umma ta fad'a cikin rarrashi, tausayin Ayrahn na kamata yanda take yarinya da ita amma yanzu haka tana da kishiya wadda za'a kira da Amaryar mijin ta, d'aga ido tayi ta kalli Umma, tana shirin fara magana Umma ta girgiza kae tana murmushin yak'e "Ya isa haka ki tashi ki je kin ji?" sam bata so wani 6acin ran ya sake shiga tsakanin ta da iyayen nata dan haka ta mik'e tana jin jiri na d'ibar ta "Allah ya tsare Auta" shine abinda Abba ya fad'a sanda take shirin gifta inda yake zaune, bata iya amsawa ba dan ita kad'ae tasan yadda take ji a cikin zuciyar ta, shine ya d'auki kayan sannan yayi gaba ita kuma ta rufa masa baya, suna fita kuwa Umma ta mik'e da sauri ta shige cikin d'aki saboda kukan da taji ya taho mata, bin ta da kallo Abba yayi sannan ya dawo da kallan sa tsakar gidan da murmushi kan fuskar sa gami da girgiza kae. A hankali take takawa kamar mara laka zuwa wajen motar tasa, shi ya saka hannu ya bud'e mata, yanzu kam babu musu ta shiga sannan ya zagaya driver seat ya shiga ya zauna, kallan ta yayi yanda yaga tana ta curewa waje d'aya kamar me jin sanyi lokaci d'aya kuma tana matsar k'walla, lumshe idanun sa yayi a ran

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70