Chapter 3
Chapter 3
yabi Abbun sannan ya maeda duban sa kan Ummee yana jin yanda k'irjin sa ke bugawa "Ummee.." ya fad'a yana kallan ta, seta mik'e kawae tabi bayan Abbun a ranta tana sak'a yadda zasu 6illowa al'amarin, lallae idan ba suyi wasa ba suna cikin matsala.. Runtse idanun sa yayi har lokacin yana jin yadda bugun zuciyar sa ke k'aruwa, me yake faruwa ne? Yakae wajen minti 5 zaune a wajen yana sak'awa da warwarewa sannan ya d'auki wayar sa ya lalubo number ta ya danna kira. A 6angaren ta kuwa har lokacin tana kwance kan madaedaecin gadon d'akin, kanta d'ore akan pillow hawayen da suka k'i tsayawa se zuba suke akan pillown, kanta babu d'an kwali hakan ya bawa sumar kanta damar bajewa akan pillown, dae_dae lokacin da kiran wayar tasa ya shigo wayar ta yayi dae_dae da lokacin da Umma ta yaye labulen d'akin ta shigo, ringing d'in da taji ya sanya ta kallan wayar, Ayrah ta tashi zaune tana kallan Umman lokaci guda tana maeda duban ta kan wayar "Mik'omin wayar.." Umma ta fad'a tana mik'a hannun ta, lumshe manyan idanun ta tayi wasu hawaye masu d'umi suna zubowa akan kuncin ta, ganin bata da niyyar mik'o mata wayar ne yasa Umman ta k'arasa da kanta ta d'auki wayar ta kashe ta gaba d'ayan ta sannan ta kalli Ayrah data fashe da wani irin kuka tace "Kiyi shiru ki dena kuka, ki tsaya ki saurare ni, base kin tada hankalin mu muma mun tayar da naki ba.." kafin Umman ta kae k'arshen zancen ta Ayrah tace cikin kuka tana girgiza kae "Umma meyasa haka? Shin baku san wanene Raj ba? Baku san halin sa ba? Ko kuwa iyayen sane baku sani ba.." K'arasawa Umma tayi ta zauna akan gadon kana ta kamo Ayrahn cikin jikin ta, bata fara magana ba seda taji ta fara sauke ajiyar zuciya, sannan ta kama dogon gashin Ayrahn ta d'aure a tsakiyar kanta kana ta fara magana a nutse tana jin zuciyar ta na mata wani irin zafi... B'angaren sa kuwa runtse idanun sa yayi bayan ya sake kiran layin Ayrah yaji shi a kashe, yaja wani dogon numfashi sannan ya mik'e akan k'afafun sa yana daedaeta nutsuwar sa a ransa yana jin ya zama dole yasan aenahin abinda yake faruwa kafin k'wak'walwar sa ta tarwatse, dan kuwa tabbas akwae rina a kaba, me yake faruwa haka?..... _*TUSHEN LABARI*_ ZARAH AUTA (Mhiz Innocent) ✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page_002 ____kyakykyawa ce fara sol me manyan idanuwa, haka zalika kuma me k'aramin jiki da dogon hanci, a kallan farko zaka iya k'iyasta shekarun ta, san haka baza ta wuce shekaru 4 ba, tana sanye cikin Uniform dake a goge fes fes dasu, hannun ta d'auke da basket d'in ta dake d'auke da flask d'in abinci na yara en makaranta da kuma rubber ruwa, da d'an gudun ta take fitowa daga cikin d'akin daya kasance mallakin ta, fuskar ta d'auke da murmushi, seda tazo dab da Abban nata sannan tace cikin muryar ta da bata gama fita sosae ba "Abba na shirya.." "Yawwah..Ayrah" Abba ya fad'a yana jan kumatun ta kafin ya d'ora da fad'in "Ina yayan naki?" d'an k'aramin bakin ta ta tura gaba kad'an kana tace "Abba Yah Sadeeq fa be shirya ba" kafin Abban ya sake cewa komae sega Sadeeq d'in ya fito, fari ne se dae ba can ba, amma kamar su d'aya da Ayrahn, wanda hakan ze alamta maka da cewar yayan tane, shima yana sanye cikin Uniform d'in kamar nata, sedae akwae d'an banbanci a Uniform d'in nasu wanda hakan ke nuni da ita a primary take yayin da shi kuma yake a secondary, shima nasan a wanke suke tass kuma a goge hannun sa rik'e da jaka yana k'ok'arin goyawa a bayan sa yace sanda yazo kusa da Abba bayan ya watsawa Ayrah harara "Abba ka ganni fa a shirye nake.." mik'ewa Abba yayi yana rik'e da hannun Ayrah dae_dae lokacin da Umma ta fito daga kitchen tana kallan Sadeeq tace "Ba zakayi break bane?" kallan Umman yayi kafin ya saci kallan Abba "Wato so kake ka janyowa kan ka wata cutar koh?" sosa kansa yayi kana yace har lokacin kan nasa a k'asa "A'ah fa Abba, ae ina siyar wani abun a school.." "Toh yayi kyau, amma ko tea ne ka dinga sha ko ka samu hanjin ka ya warware" "Toh Abba.." ya amsa a hankali "Toh Allah ya tsare, ya bada sa'a.." Umma ta fad'a tana binsu da kallo su duka, suka amsa da "Ameen" sannan suka fice daga d'akin... Kae tsaye fire service suka wuce inda Abban ke ajiye motar sa k'irar Civic Honda, suka jira shi a bakin wajen, ya shiga ya d'auko sannan suka shiga ya wuce dasu zuwa makarantar kamar koda yaushe, a bakin makarantar ya ajiye su bayan ya sallami kowannen su sannan shi kuma ya wuce wata makarantar government da yake koyarwa a cikin garin nasu.. Hannun Ayrah cikin na Yah Sadeeq har suka k'arasa bakin ajin su Ayrahn, sannan ya sakar mata hannun yace yana kallan ta "Ayi karatu sosae, banda k'iriniya" "Toh" ta fad'a kawae tana yin cikin ajin nasu, seda yaga ta shiga sannan ya wuce nasu ajin.. Wajen k'arfe 10 aka fito break, kamar koda yaushe ita da k'awayen ta kan fito harabar makarantar suyi wasa bayan sun gama cin abincin, yau ma hakan ce ta kasance, dan kuwa suna gama cin abincin suka fito wajen suka fara wasan su irin na yara.. A hankali idanun ta suka sauka akan sa kamar koda yaushe yana zaune akan wani d'an dandamalin dake k'ofar wani aji, yayi shiru wani lokacin yana d'an kallan abinda ke faruwa a cikin makarantar, wani lokacin kuma idanun sa na kallan k'asa ko wani wajen, cigaba tayi da wasan ta sedae lokaci zuwa lokaci takan juya ta kalle shi har zuwa lokacin da aka koma break d'in suka koma aji bayan sunyi butu butu da Uniform d'in nasu. Suna zaune cikin ajin wani malami na musu karatu, seta d'an saci kallan tagar su da take kallan k'ofar ajin, kamar yadda ta tsammata kuwa seta hange shi d'an nesa kad'an yana lek'owa cikin ajin yana kallan malamin, cigaba tayi da kallan sa ba tare da ta cigaba da saurarar malamin ba "Ayrah!!" taji malamin ya ambata, seta juyo da sauri tana gyara zaman ta, idanun ta da suka yi rau rau akan malamin, maeda duban sa yayi kan inda take kalla, ganin haka ya sanya yaron saurin yin k'asa da kansa dan kar a gansa, hakan yasa malamin bega komae ba, da mamaki ya tako zuwa inda take yace yana kallan ta "Me kike kalla acan?" kamar zata fashe da kuka tace "Ba komae.." ta fad'a d'an k'aramin bakin ta a gaba, sake kallan wajen malamin yayi sannan ya dawo da duban sa kanta yace "Ohk toh me muke cewa?" ita sam bama ta gane tambayar da yake mata ba dan haka kawae ta bishi da kallo, ya girgiza kae kawae sannan ya koma ya cigaba da abinda yake yi, bata sake kallan wajen ba ta bada hankalin ta wajen karatun da ake musu, dan kullum ne idan ta koma gida se Yah Sadeeq ya sanya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70