Skip to content

Chapter 62

Chapter 62

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

ta fad'a tana kallan Autar ta ta dake ta sussunne kae "Toh tashi ki shirya ki je.." "Kae Umma!" ta fad'a bayan ta d'ago kan ta ta kalli Umman, girgiza kae Umma tayi tana murmushi sannan ta mik'e tana fad'in "Idan kin gama jin kunyar seki tashi ki je" daga haka ta fice daga d'akin, bin Umman tayi da kallo har ta gama ficewa daga d'akin sannan ta dawo da duban ta jikin mudubin d'akin nata ta kalli fuskar ta, babu komae akan fuskar ta ta, kuma itama bata buk'atar wani abun, se kwae ta mik'e ta ciro wani gogaggen hijab d'in ta a cikin wardrobe ta zura sannan ta fito tana kallan tsakar gidan nasu, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu kowa sannan ta fice daga cikin gidan. Tunda ya hango ta yaji wani irin sanyi na ratsa shi, wannan bak'in cikin da yazo dashi ya shiga kwaranyewa yana yin nasa waje, be san sanda ya saki murmushi ba lokacin data dakata daga inda take tsaye ba, bud'e murfin motar yayi ya fita sannan ya k'arasa ya bud'e wajen me zaman banza kana yace yana kallan ta "Bismillah gimbiya.." wata kunyar ce ta sake lullu6e ta dan haka da er sassarfa ta k'arasa ta shiga cikin motar, se da ta shiga sannan ya zagaya ya koma mazaunin driver har lokacin yana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa musamman daya tsinci murmushi akan kyakykyawar fuskar ta daya dad'e be gani ba, koda ya shiga motar ma juyowa yayi gaba d'aya yana kallan ta kamar ze cinye ta, hannu ta kae taja hijab d'in jikin ta tana rufe fuska da shi sannan tace "Kae don Allah!" wani k'ayataccen murmushi ne ya su6uce masa sannan yace "A'ah ki bar ni na kalla ni kam, kin san kuwa yanda na zak'u da ganin fuskar ki, nayi missing naki irin sosae d'in nan" ya fad'a yana ji kamar ya janyo ta ya rungume ta, se dae yasan halin abarsa dan haka ya d'an lumshe idanun sa dae_dae lokacin data d'ago kan ta "Ina fatan an yafe min abinda na aekata, kae na bisa wuya na" ya fad'a yana d'an rank'wafar da kan sa, bin sa tayi da kallo sanda ya rank'wafar da kan nasa, dae_dae lokacin da idanun ta suka sauka kan wasu jerin gwanon invitation card dake ajje a waje guda, haka kawae taji sun d'auki hankalin ta saboda yanda taga kamar idanun ta sun hangi sunan da take da tabbacin babu me irin shi a yankin su, dan haka babu 6ata lokaci ta d'auki katin sannan ta sauke manyan kyawawan idanun ta kan katin ta shiga karantawa, katin gayyatar d'aurin auren Raj Kabeer ne da kuma Muneerah Abubakar, idan har bata manta ba ko kuma kamar yanda ta sani sunan sa ne wannan, take kuma a lokaci guda k'afafun ta suka fara rawa kamar wad'anda ake kad'asu, tun kuma lokacin data karanta sunan wata mace tare da sunan Rk taji kamar wani abu ya gifta ta wajen idanun ta ne dan haka bata sake ganin wani abu dake a cikin katin ba, k'irjin ta ya shiga bugawa da k'arfin gasken gaske hannun ta kuma dake d'auke da katin ya shiga rawa shima dan haka cikin k'ank'anin lokaci katin yayi nasa wajen saboda yanda hannun ta ya gaza rik'e shi, gaba d'aya kan ta ya kulle, k'wak'walwar ta ta toshe haka zalika idanun ta sun makance kunnuwan ta kuma sun kurumce, babu abinda take iya tunani da hangowa se sunan sa dake jikin katin tare da sunan wata mace... Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 038 ___Jin da yayi shiru har lokacin ba tace komae ba ko tayi wani abun da zesa ya fahimci tana wajen ba ya sanya shi d'ago da kan sa a nutse ya sauke su a kan ta lokacin da jajayen idanun ta da k'walla ta gama cika su taff ke kan sa, abu kad'an ne ze sanya su zubowa, kallan sa kawae take yi kamar me son gano gaskiyar abinda ta gani a cikin katin nan daga cikin fuskar sa, da mamaki yake kallan ta ganin tana masa wani kallan tuhuma ga kuma kyawawan narkakkun idanun ta da suke cigaba da bin sa da kallo, a hankali ya kae hannun sa yana shirin rik'o ta lokaci guda kuma yake fad'i a nutse "Meya faru?" ya fad'a cikin damuwa, dae_dae kuma lokacin daya ida kae hannun sa jikin ta, se a lokacin ta soma dawowa hayyacin ta, ta kautar da jikin ta daga k'ok'arin rik'o ta daya ke yi, sannan cikin sake k'arya ta zuciyar ta da abinda ta gani tace "Aure kayi?" ta k'are maganar lokacin da hawayen da suka taru a cikin idanun ta suka samu damar zubowa akan fuskar ta, runtse idanun sa yayi lokaci d'aya k'irjin sa ya d'an buga "Ya akayi ta sani?" tambayar data fara zuwa masa a cikin kae kenan, kamar ta san me yake tunani seta saka hannu ta d'auko katin daya fad'i daga hannun ta d'azun duk da har lokacin jikin ta be bar rawa ba "Wannan katin auren waye?" iska ya fesar daga bakin sa sannan ya dafe kan sa daya sara masa, a hankali ya sake d'aga idanun sa ya zuba su a kan ta sannan yace "Ayrah pls ki tsaya zan miki bayani kin san.." "Na auren waye?" ta sake katse masa maganar daya fara yi, dan haka kawae taji jikin ta ya sake yin sanyi, seda ya sake lumshe idanun sa sannan yace "Nawa ne amma.." kukan data keta rik'ewa ne ya k'wace mata gaba d'aya, bata da k'arfin da zata iya ficewa ta shige gida tayi kukan ta dan haka ta d'ora kan ta akan cinyar ta ta shiga rera shi tana jin yanda wani irin takaeci, bak'in ciki da kuma k'unar zuci ke addabar ta "Yah ilahee.." ya ambata akan la66an sa, shi kam yau yaga ta kan sa, hannun sa duka biyun ya saka ya janyo ta cikin jikin sa har zuwa lokacin kuma kukan take har da sheshshek'a, fuzge jikin ta ta shiga yi amma ya k'arasa shigar da ita sannan ya zagaye ta da duka hannayen nasa yana lumshe idanun sa, har lokacin bata hak'ura ba ta cigaba da k'ok'arin tashi lokaci d'aya kuma tana furta "Ni ka sake ni, bana son ka, bana son ka" be san sanda murmushi ya k'wace masa ba yana girgiza kae, ban da abin Ayrah idan bata son shi mene na kishin sa haka? Sake rungume ta yayi tsam cikin jikin sa kamar ze maeda ta cikin sa, sannan ya d'ora kan sa akan ta dake kan k'irjin sa, da dae ta gaji da k'ok'arin tashin se kawae ta sake fashewa da wani kukan tana komawa jikin nasa gaba d'aya, hakan ne ya sake bashi damar rik'e ta sosae, be hana ta kukan ba dan yasan dole ne se tayi kukan musamman wannan abu data gan shi kawae daga sama, ta d'auki wajen minti 2 tana cigaba da rera kukan se kuma daga baya ta koma tayi lak'was tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya cike da jin haushin sa, se kuma a lokacin ta cigaba da kicin_kicin tashi, a wannan karon be hana ta tashin ba ya sake ta a

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70