Chapter 69
Chapter 69
k'arfe 10 ya isa Hotel d'in yayi parking motar sa sannan ya sauka kae tsaye ya wuce d'akin, a nutse ya saka mukullin hannun sa ya bud'e sannan ya tura k'ofar d'akin kana ya tura jikin sa cikin d'akin, acan tsakiyar gadon ya hango ta ta lullu6e jikin ta da bargo kan ta akan gwuiwar ta tayi shiru idanun ta akan k'ofar, ganin sa da tayi ya sanya zuciyar ta saurin karyewa bata san sanda wasu hawaye masu d'umi suka fara sintiri akan kuncin ta ba lokaci d'aya kuma tana cusa kan ta cikin k'afafun ta, runtse idanun sa yayi yana jin wani irin tausayin ta na ratsa shi, cike da sassarfa ya k'arasa cikin d'akin, kae tsaye ya haye kan gadon beyi wata wata ba ya jata cikin jikin sa yayi mata wata kyakykyawar runguma, dae_dae lokacin data fashe da kuka kenan me cin rae tana sake jin wani irin rauni a tare da ita, sake rungume ta yayi yana jin yadda bugun zuciyar ta ke fita da sauri da sauri, a hankali ya d'ora kan sa akan ta dake kan k'irjin sa sannan ya shiga shafa bayan ta a hankali lokaci d'aya wani tausayin ta na sake lullu6e shi, sosae take yin kuka wanda ke fita tun daga k'asan zuciyar ta, shi kuma be hana ta ba se dae har lokacin be dena shafa bayan nata ba, a hankali cikin rarrashi ya furta sanda ya kae bakin sa cikin kunnen ta "Kukan ya isa haka plsss.." ya k'arasa yana jan k'arshen maganar tare da hura mata iska a cikin kunnen na ta lokaci d'aya kuma yana sake shigar da ita cikin jikin sa, a hankali ta shiga rage sautin kukan na ta, har zuwa sanda ta koma sauke ajiyar zuciya, se a lokacin ya saki k'atuwar ajiyar zuciya sannan yace a hankali "Am sorry, am deeply sorry pls.." ba tace komae ba har lokacin kuma be sake ta ba dan sosae yake jin nutsuwa da take cikin jikin na sa "Plss Babe.." ya sake fad'a nan ma dae a hankali kamar me rad'a, kamar jira take suma kuma hawayen kamar jira suke se suka zubo kan fuskar ta sannan ta fara maganar cikin raunanniyar murya "Don Allah kada ka sake tafiya ka bar ni anan kaaji?" tausayin ta ne ya sake kama shi, shi kan sa baya son barin ta amma babu yadda zeyi dole se dae ya raba kwanan ko da d'ad'd'aya ne, yau idan ya kwana anan gobe ya kwana acan "Toh In Sha Allah" ya fad'a sannan ya d'ora da "Nan d'in ne bakya so?" "Tsoro nake ji ni dae, bana son nan gaba d'aya" tayi maganar tana k'ok'arin tashi daga jikin na sa, kamar kada ya sake ta amma seya sake ta d'in a hankali, se kuma a lokacin ya fahimci yanda ilahirin jikin sa yayi wani mugun sanyi, wata iriyar kasala ta gama rufe shi kamar kada ya motsa daga inda yake "Shikenan.. Zan fita na samo gidan da zamu zauna kafin komae ya daedaeta.." da sauri ta d'aga narkakkun idanun ta ta kalle shi jin da tayi yayi zancen fita, ya fahimci abinda ya sanya ta kallan na sa ba tare da ta shirya ba dan haka ya d'an yi murmushi kana yace "Kar ki damu da rana zan fita, dama Abbu na nema na, sena biya ta wajen su Abba ma mu gaesa" "Don Allah zan bi ka.." ta fad'a da sauri bayan ta rik'o hannun sa, hannun nasu yabi da kallo saboda yanda ya sake jin tsigar jikin sa ta tashi, ganin inda yake kalla ya sanya itama ta kalla, da sauri ta saki hannun nasa tana tura k'aramin cute lips d'in ta, nan ma seya sake bin bakin nata da kallo lokaci d'aya yana lumshe lumsassun idanun sa, ya kae wajen second 30 a haka sannan ya bud'e yana kokawa da zuciyar sa yace "Muje kici abinci" "Na ci kafin ka shigo!" ta fad'a ba tare da ta kalle shi ba "Kin ci?" ya fad'a yana kallan ta sosae, seta jinjina kae kawae tana sake kaucewa kallan daya ke bin ta da shi, jin bece komae ba ya sanya ta sake fad'in "Allah kuwa kuma ka duba ka gani idan ban ci ba" ta fad'a tana nuna masa abincin da ke ajje, seda yabi wajen da kallo sannan ya dawo da duban sa kan ta yace "Matso kiyi bacci kafin na dawo.." yayi maganar yana kishingid'a akan gadon lokaci d'aya yana mik'a mata hannun sa d'aya, tura bakin ta gaba tayi kafin tace "A'ah.." ta fad'a tana d'ora kan ta akan kafad'ar ta, tilas abinda tayi d'in ya sanya shi lumshe idanun sa yana sakin murmushi, hannun sa ya kae kawae ya janyo ta se gata cikin jikin sa, ya gyara kwanciyar sa sannan itama ya gyara mata ta ta kwanciyar cikin jikin sa duk da yanda take ta neman k'wacewa daga jikin nasa, wanda hakan ya bawa ma6allan rigar jikin sa na sama damar 6allewa, hakan ne ya bawa kyakykyawar farar fatar sa me d'auke da bak'a sid'ik d'in gargasa bayyana, ba tare daya lura ba ya sake manna ta da k'irjin sa, hakan ne ya bawa kan ta damar kwanciya akan zallahr fatar sa dake ta tashin wani sassanyan k'amshi, k'atuwar ajiyar zuciya ya sauke sanda hakan ya faru, ya lumshe idanun sa bugun zuciyar sa na k'aruwa "Kiyi bacci" yayi k'ok'arin lalubo kalmomin biyu ya had'a ya fad'e su, ita kan ta sosae zuciyar ta ke bugawa musamman ma jikin ta dake ta rawa kamar mazari, amma duk da haka be sake ta ba, ganin bashi da alamar sakin ta ne ya sanya ta hak'ura ta runtse idanun ta tana jiran zuwan bacci, cikin ikon Allah kuma babu dad'ewa baccin ya d'auke ta seta koma tana sauke numfashi akan k'irjin sa, wanda hakan ya sanya shi saurin lumshe idanu gami da janye ta daga jikin sa a hankali yana jin yanda bugun zuciyar sa ke cigaba da k'aruwa fiye da d'azun, ba zeso wani abun ya shiga tsakanin sa da Ayrahn a Hotel ba, ba dan haka ba yau yadda yake jin sa babu abinda ze hana shi bin abinda zuciyar sa ke raya masa duk da yadda ita kan ta Ayrahn har yanzu bata koma asalin Ayrahn ta ba. Seda ya shiga toilet ya watsa ruwa sannan ya fito har lokacin tana baccin ta a nutse babu hayaniya, da alama dama baccin jiyan be wani wadace ta ba, hakan ne ya sanya shi saurin shiryawa ya fice yana fatan har ya dawo bata farka daga baccin ba, kafin nan ya samo musu mafita. ... Sanda ya isa gidan kae tsaye parlourn Abbu ya wuce dan yana da tabbacin yana nan, da sallama ya shiga d'akin, Abbu dake zaune kan kujera hannun sa d'auke da laptop yana aeki ya amsa sallamar har lokacin be d'auke idanun sa daga kan laptop d'in ba, a nutse ya k'arasa cikin parlourn ya zauna a k'asan had'ad'd'en carpet d'in dake malale a tsakiyar d'akin "Barka da safiya.." ya fad'a yana kallan Abbun, se a lokacin Abbu ya sauke ajiyar zuciya sannan ya rufe laptop d'in ya ajje ta gefe kana yace "Barka dae doctor ya Muneerahn?" "Alhamdulillah.." ya fad'a a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70