Chapter 33
Chapter 33
a fuskar sa dan bega sanda ta fito ba se maganar ta kawae yaji, sannan yace bayan ya ida mik'ewa tsaye "A'ah Umma me kika gani? Kawae gajiya ce" ya fad'a cikin k'arfin hali, seta saki ajiyar zuciya sannan tace "Toh jeka kwanta ka huta haka nan Uhmm?" jinjina kae yayi kawae yana juyawa ya koma cikin d'akin a hankali, ya baje kan gado yana jin yadda k'irjin sa ke masa wani irin zafi kamar ze rabu da jikin sa. Komawa Umma tayi ta zauna tana d'ora hannun ta akan kuncin ta, lamarin duniyar nan sosae yake bata tsoro musamman a en kwanakin nan da abinda zasu ci yake gagarar su, dae_dae lokacin da Abba yayi sallama cikin gidan, Umma ta mik'e cikin son kawar da damuwar dake shimfid'e kan fuskar ta tace "Sannu da zuwa" "Yawwah sannu ka dae" ya fad'a yana son karantar yanayin ta, seta riga shi yin gaba dan bata so ya karanto raunin dake tattare da ita ballantana har shima yaji ya sake karaya "Wallahi ban samu komae ba" Abba ya fad'a muryar sa a raunane gwanin ban tausayi bayan ya zauna, ajiyar zuciya Umma tayi sannan tace "Babu komae, Allah ze kawo ko zuwa gobe ne In Sha Allah" seya jinjina kae kana yace "Ina wannan yaron? Allah yasa yaci wani abun ko dan rashin lafiyar sa" kallan d'akin da Yah Sadeeq ke ciki Umma tayi sannan tace "Ehh toh yaci zance, amma kasan halin sa ba son cin abincin nan yake ba, yanzu haka ma yayi bacci" "Bacci kuma? Lafiya dae koh?" Abba yayi tambayar cike da fatan lafiyar ce, ba tare da tunanin komae ba Umma tace "Ehh lafiya k'alau" "Toh madallah, bari na kira mana Ayrah" Abba ya fad'a yana fiddo wayar sa daga aljihu, da sauri Umma ta kalle shi tace "A'ah Abban su kada ka kira ta, bana so ta fahimci ko da akwae wata matsala daga nan wajen mu, kasan halin yarinyar nan" shiru Abba yayi cikin na'am da zancen nata kafin yace "Toh shikenan.." daga haka yayi shiru yana cigaba da tunanin rayuwar su ta baya data yanzu, shida yake ajiye abincin wata a gidan sa tafi tafi ya koma siya kad'an kad'an, yanzu kuma da yanayin rayuwar ya sake juyawa se gashi wataran a cikin gidan sa an tashi babu ma abincin da za'a ci, ya riga yayi na'am da k'addara, ya yadda da ita kuma yasan Allah ne ya k'addaro masa ita amma ta sanadin Abbu, Abbu yayi musu wani gi6i a rayuwar su da baza su ta6a mantawa ba, ta dalilin sa abubuwa da dama sun faru kuma suna kan faruwa ma, baya tunanin ze iya yafewa Abbu abinda ya masa koda kuwa basu sake had'uwa a duniyar nan ba, yana jin koda yace zeyi hakan ma toh kuwa wani 6angaren nashi baze ta6a yafewa kan sa ba, abinda ma baya tunanin ze faru kenan, wanda shi a gare shi ma baya fatan sake had'uwa da koda me irin halin Abbu ne ballantana kuma shi kan sa Abbun...... Mhiz Innocent...... ✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 025_026 ___Kae tsaye Hostel suka wuce su biyun har lokacin suna tattauna maganar da tak'i k'arewa, dukan su mamaki yak'i sakin su, a haka har suka k'arasa d'akin su Jidda, ko sallama babu wadda ta iya a cikin su saboda yadda suka k'agu su isar da labarin nan, Jidda dake facing k'ofar d'akin tace "Kae jama'a lafiya kuwa?" bud'a hanci Abeeda ta shiga yi ita a dole ta kawo musu abu me muhimmaci "Jarida na kawo muku me tsada!" tayi maganar sanda take neman waje ta zauna, sakkowa Ruks tayi daga kan gadon ta sannan ta k'araso tana kallan Abeeda tace "Kinga kawae ki fad'a mana meya faru?" "A'ah wallahi nawa zaku siya?" Abeeda ta fad'a tana sake gyara zaman ta, k'aramin tsaki Bahijja ta saki kafin tace "Don girman Allah ki fad'a mana, haba mana" dariya Abeeda tayi kana ta sakko da jakar ta dake mak'ale a kafad'ar ta ta sanya hannu ta d'akko wayar ta tace lokaci guda kuma tana danna wayar "Ke kam Bahijja Allah ya shirye ki da son gulma wallahi" "Oho dae, mu dae fad'a mana kawae" "A'ah an shiga 3" Abeeda ta fad'a tana d'an bud'e ido ganin da tayi wayar ta ta sam tak'i dannuwa, ga dae ta ta kawo amma kwata kwata tak'i dannuwa "Kashhh! Shegiyar waya seda ta kwafsa min wallahi" ta fad'a tana dafe kan ta, Bahijja ce ta d'auki wayar itama ta ta6a, ganin da tayi babu abinda ke motsi a wayar ya sanya ta fad'in "Kinga fad'a mana da baki kawae pls" Khadeejah da ta gama k'uluwa dan takaeci da haushi tace bayan ta ja k'aramin tsaki sannan ta maeda duban ta kan su Bahijja "Doctor Rk" sunan sa suka ji ta ambata ne ya sanya dukan su kallan ta, Abeeda ta d'ago ba tare da ta kalli Khadeejah ba tace, dan gaba d'aya ita kan ta seda taji ta muzanta da abinda wayar ta mata bayan cika bakin da ta gama yi "Ina Ayrah ta cikin d'akin kun nan? Toh soyayya suke da Doctor.." dukan su suka cigaba da kallan ta kowannen su na ganin kamar zarewa tayi yasa take wannan maganar, Jidda tayi k'arfin halin fad'in "Wait mana hajiya! Wane Doctorn kike magana kuma wace Ayrahn kike magana akae?" tayi maganar cikin tsare ta da idanu, murmushi Abeeda ta saki sannan tace "Dama nasan ba yadda za kuyi ba shiyasa na d'auko muku hoto, amma kada ku damu zan kae a duba min wayar, idan ta gyaru zan dawo na nuna muku hoton dana d'auka na shi shi da ita yau da suka fita.." daga haka ta mik'e ta fice Khadeejah tabi bayan ta, kusan a tare suka bita da kallo kamar wasu dolaye, ta bar su da tunani kala kala, sun kae wajen minti 1 a hakan sannan Bahijja tayi k'arfin halin fad'in bayan ta kalle su "Kada fa ace da gaske Abeeda take" wani murmushi Ruks tayi sannan tace "Haba Bahijja kada ki zama shashasha mana, Doctor Rk fa take magana wae yana soyayya da wannan yarinyar? Dududu ma nawa take?" shiru Bahijja tayi na d'an wani lokaci kafin can tace "Ke wallahi ba tun yau nake zargin yarinyar nan ba, dama na dad'e ina tsoron kada kyawun ta ya rinjaye shi mu shiga 3" se a lokacin Jidda tace "Hmmm, kuna tunanin kyawu ze rud'i kyakykyawa ne? Bana tunanin haka gaskiya" tayi maganar tana d'an k'ank'ance idanun ta kamar me tunani "Toh koma dae menene akwae wata a k'asa" Bahijja ta fad'a, kafin wata a cikin su tace komae sallamar Ayrah ta ratso cikin d'akin, babu wanda ya iya amsa mata se bin ta da suka yi da kallo dukan su, kallo irin na tuhuma, ganin irin kallan da suke mata ne ya sanya ta sake had'e kyakykyawar fuskar ta ta k'araso cikin d'akin "Daga ina kike?" Bahijja tayi k'arfin halin fad'in hakan, kallan ta Ayrah tayi da mamakin jin furucin ta, kafin Bahijja ta gama fahimtar irin kallan da Ayrahn ke mata ta jiyo k'aramar muryar ta tana fad'in "Toh ina ruwan ki?" ta fad'a tana hararar gefe gami da murgud'a baki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70