Skip to content

Chapter 47

Chapter 47

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

ilahirin jikin sa lokacin da yaji zancen d'aurin auren, a hankali ya lumshe idanun sa, se dae ga mamakin sa sosae bugun zuciyar sa ya k'aru, seya dakata yana tuna kasadar da yayi da kuma k'alubalen da yasan dole seya tunkaro shi, amma tunda dae ya gama da wannan koma wanne k'alubale ne yana ganin me sauk'i ne, a hankali kuma se yaji wani rauni na son shigar sa, cikin sakannin da basu gaza 2 ba ya bud'e manyan idanun sa da hakan yasa zaka iya fahimtar yadda yanayin fuskar sa take, sosae annuri ke fita daga kyakykyawar fuskar sa, seya fesar da iska daga bakin sa sannan ya cigaba da kar6ar hannun mutane dake mik'a masa suna gaesawa, wasu da gasken dan taya murna ne suke mik'a masa hannun su gaesa yayin da wasu suna so ne kawae su gaesa da shi d'in saboda yadda yake, d'an birni, had'ad'd'e kuma kyakykyawa, kwata kwata baya lura da yanayin mutum kawae ze mik'a tattausan hannun sa ne su gaesa duk da ba kallan fuskar mutanen yake ba. ... Ayrah na cikin gida sam bata san abinda ke faruwa ba, ita gaba d'aya tana jin komae ne kamar a mafarki ko kuma wani wasan film, dan haka ta gaza amincewa kan ta wannan abinda yake faruwa gaskiya ne, a yanda tafi d'auka wani mummunan mafarki ne take yi wanda yake nuni da tana neman bijirewa maganar Abban ta, dan haka take fatan tayi maza ta farka daga baccin, se dae me? Har yanzun tak'i farkawa, tun tana cigaba da yadda mafarkin ne har tazo ta fara tunanin shin ko gasken ne? Duk abinda ke faruwa a yanzun da gaske ne? Ba ita ta tashi daga kwancen da take ba seda taji ana kiran sallah, a hankali ta fara k'ok'arin mik'ewa se dae jirin daya kwashe ta ta sanya ta saurin komawa ta kwanta tana sakin wani kuka, ita kad'ae tasan abinda take ji a jikin ta, ita kad'ae tasan yanda take jin kan ta da gangar jikin ta, gaba d'aya jin kan ta take yi ya mata wani gingirin kamar ba'a jikin ta yake ba, ga jikin ta da gaba d'aya ta rasa gane a wane yanayi ma zata saka shi, ta kae wajen minti 1 a kwancen seda jirin ya d'an yi sauk'i sannan ta mik'e duk da yanda take kallan abinci da ruwa a ajiye hakan be sanya tabi ta kan su ba, kae tsaye ta fice daga cikin d'akin zuwa ban d'akin dake kusa da d'akin da take ciki, alwala kawae tayi ta dawo cikin d'akin ta tada sallah. ... "Toh kae Allah ya baku zaman lafiya, Alhaji Mato kuma Allah ya baka hak'uri, dama kasan ance ba komae ne idan aka rasa ake kuma samun sa ba, Allah ya musanya maka da wadda ta fi ta" Me gari ya fad'a yana kallan su su duka "Ameen ranka ya dad'e, Allah ya k'ara girma" Rk ya fad'a ba tare daya d'aga ido ya kalli Alhaji Mato dake jifan sa da wani kallo na gargad'i da kallan nan irin na zaka sani, Alhaji Mato be iya cewa komae ba saboda yasan idan ya bud'e baki komae ka iya fitowa daga bakin sa, k'ila ma yayi maganar da zata iya tona masa asiri a cikin k'auyen, dan haka yaga shirun nasa yafi masa alkhaeri "Ayi mata magana ta fito se ku tafi koh?" Me gari ya fad'a yana kallan Rk, jinjina kae Rk yayi lokaci d'aya yana lumshe idanun sa se kuma ya bud'e bakin sa a nutse ya furta "Ehh" babu 6ata lokaci Me gari ya aeka wani daga cikin yaran sa zuwa cikin gidan cewar a fito da Ayrah. ... Lokacin da matar nan ta sake shigowa cikin d'akin da k'yar take iya bud'e narkakkun idanun ta da suke wani lumshewa da kan su kamar er maye, sanyi sosae take ji a jikin ta wanda hakan ya sanya ta takurewa cikin hijab d'in ta tana jin kamar k'asusuwan ta zasu tsage, ciwon da kan ta yake yi kuwa se abinda yayi gaba, gaba d'aya jikin ta yayi wani irin tsami "Ki taso zaku tafi" maganar da taji matar tayi ya sanya tilas ta bud'e lumsassun idanun ta ta jefa su kan matar da take gani biyu biyu, ta d'auka ma ba taji abinda tace ba dan haka ta sake maemaetawa a karo na biyu, a hankali ta zura k'afar ta daga kan gadon da take, tilas ta sake runtse idanun ta saboda yadda taji kamar ginin gidan gaba d'aya ze fad'o a kan ta, bata so ma wasu su fahimci bata da lafiyar ballantana ace za'a d'aga tafiyar tasu, burin ta d'aya kawae ta bud'e idanun ta ta gan ta cikin gidan su, gata ga Umman ta, ga Abban ta ga kuma Yah Sadeeq d'in ta, seda matar tayi gaba sannan ta mik'e tabi bayan ta a nutse tana tafiya tana dafa bango saboda kada ta fad'i, sosae tayi da gaske dan kada ta zube kafin ta isa wajen, cike da k'arfin hali ta cigaba da takawa har zuwa wajen Me garin. Bin ta yayi da kallo sanda ta zube a k'asa idanun ta a lumshe, daga yanayin yadda ta zauna d'in kawae zaka fahimci ba'a lafiyar ta take ba "Toh yanzu dae zamu damk'aki hannun mijin ki, Allah ya bada zaman lafiya" shine abinda ta tsinto Me garin na fad'a, ta sake lumshe idanun ta a karo na barkatae tana jin wani irin yanayi, kenan da gaske an d'aura mata aure da Raj? da Me gari yasan tashin hankalin da take ciki tabbas da baze ambaci Rk a matsayin mijin ta ba, daga lokacin da aka fad'i hakan tana sake jin kan ta ne dumu_dumu a mae laefi, wadda ta bijirewa umarnin iyayen ta, se dae tasan wannan d'in bame yiwuwa bane, kwangila ce suka k'ulla tsakanin ta da Rk d'in kuma nan da anjima zata k'are, dan haka wannan d'in kamar wani wasan kwaekwayo ne aka gabatar dashi cikin k'auyen. Sosae Rk yayi wa Me gari godiya sannan ya mik'e yana kallan er rigimar tasa, be san yanda zasu k'arke ba, be san kuma meze faru anan gaba ba "A'ah ba dae tafiya ba?" Me gari ya fad'a yana kallan Alhaji Mato daya mik'e shima, dan so yake ya fara yin gaba kafin Rk ya riga shi, dan kuwa tun kafin ya isa gida yake so ya gama dashi, se dae da alama Me garin na son jik'a masa aeki "Ehh.. A'ah.." Alhajin Maton ya fad'a cikin inda inda yana komawa ya zauna "Yawwah koda naji, ae ka zauna muyi hira koh?" bece komae ba dan a yadda yake ji ze iya sussurfawa Me garin zagi ne "Allah ya tsare" Me gari ya sake bin Rk da addu'ar sanda ya k'arasa dab da ita, ya rasa yanda zeyi ya mata magana, mik'ewar da tayi ne ya sanya shi d'an lumshe idanun sa sannan yayi gaba yayinda ta bishi a baya hannun ta rik'e da kan ta da har lokacin be bar sara mata ba, hannu ya saka ya bud'e mata k'ofar wajen me zaman banza, zata iya cewa ta fishi k'aguwa su bar k'auyen nan ko dan a warware wannan auren wasan sannan ta tafi gidan su,

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70