Chapter 60
Chapter 60
sannan ya dawo da duban sa cikin d'akin yana girgiza kae. Kae tsaye d'akin sa ya wuce, babu 6ata lokaci ya jefar da envelope d'in hannun sa sannan ya nemi kan side drawer ya zauna, gaba d'aya kan sa ya matuk'ar kulle, ashe maganar Yah Sadeeq gaskiya ce? Ashe iyayen Ayrah basu yi laefi ba da suka hana shi auren ta? Tabbas Abbu ya shammace su ya yaudare su sannan ya saka k'afa yayi fatali da yaddar da Abba yayi masa bayan irin tarin hallacin da Abban yayi musu su duka, meyasa Abbun yayi haka? Abba mutum ne me kirki wanda ya d'akko su daga rana zuwa inuwa, amma Abbun daya tashi se ya d'auki Abban ya maeda shi cikin ranar shi kuma ya koma cikin inuwar "Yah Allah! Why Abbu? Why?" ya fad'a a hankali yana cusa hannayen sa duka cikin sumar kan sa, gaba d'aya ji yake inama ace wannan abun ba gaskiya bane ba? Inama ace mafarki ne kawae yake yi, idan kuwa gaske ne ya zama dole ya nemowa kan sa da kuma shi kan sa Abbun mafita kamin lokaci ya k'ure musu, ranar gaba d'aya sukuku ya wuni, ko bacci be iya yi ba saboda wannan al'amari daya hargitsa masa kwanya. .... A d'aya 6angaren kuwa kwanakin da suka biyo baya seya zamana wata kulawa ta musamman iyayen ke bawa Ayrah, kamar ma k'ara musu soyayyar ta akayi dan hatta kulawar data ke samu a yanzun tafi ta da, ita kam farin ciki take ji kamar tayi mene, tana kuma iya bakin k'ok'arin ta wajen ganin ta faranta musu ran su ba tare data 6ata musu ba. .. Suna zaune su duka a tsakar gidan suna hira cikin farin ciki da k'aunar junan su, Ayrah na daga gefen Umman ta cikin doguwar rigar wani yadi me matsakaecin kyau fuskar ta yanzun babu laefi ta d'an samu albarkacin kwalli data saka, dan haka ya 6oye kaso da yawa daga yanda tayi zuru zuru, tayi kyau sosae duk da bayan kwallin babu wani abu data k'ara a fuskar ta, se kuma mayafi data yafa shi a kan ta ta zubo dashi kan kafad'ar ta, kallan Yah Sadeeq daya d'an rik'e k'afar sa tayi kana tace "Yah Sadeeq k'afar ce?" murmushi yayi sannan ya girgiza kae kana yace "A'ah Auta, ba k'afar bace ba.." "Ayrah.. Je ki d'auko masa maganin nan ya shafa, kin san halin sa dae.." babu musu ta mik'e zuwa cikin d'akin dan d'akko masa maganin, dae_dae lokacin da wani yaro yayi sallama cikin gidan, dukan su suka amsa masa sallamar "Wae a waje wani yace ayi masa iso.." Abba ya kalli yaron kana yace "Waye?" "Yace wae Raj sunan sa.." tana shirin fitowa taji sunan da aka ambata, seta dakata da sauri tana jin yanda bugun zuciyar ta ya k'aru, ko taku d'aya ta kasa k'arawa daga inda take kamar me tunani. Kallan Umma Abba yayi sannan ya maeda kan yaron yace "Fad'a masa ya shigo" fita yaron yayi, ita kuma Umma ta koma d'akin ta ta d'auko babban mayafin ta ta yafa sannan ta fito ta nemi waje ta zauna, tunda taji Ayrahn shiru tak'i fitowa tasan taji wanda akace ze shigo, Ayrahn har mamaki take bata a kwanakin nan, duk irin yadda take k'aunar Raj d'in amma tun dawowar ta gida bata sake maganar sa ba, bata sake koda maganar abinda ya shafe shi ba, kuma duk Umman tasan hakan ya ta'allak'a ne da tun farko data fahimci basa k'aunar sa, toh amma yanzu kam yaya zasuyi tunda har igiyar aure ta ratsa tsakanin su?. Da sallama ya shigo cikin gidan sanye cikin bluen shadda jamfa da wando wad'anda suka matuk'ar yi masa kyau, se dae yanzu ma babu hula a kansa, kusan tare suka amsa masa sallamar sanda yake k'arasowa cikin gidan, a nutse ya tsuguna daga gefen tabarmar da Yah Sadeeq ke kae kan sa a k'asa ya furta "Barkan ku da wannan lokaci.." cigaba da kallan sa Umma tayi, da alama har yanzu nutsuwar sa tun ta yarinta tana nan, haka zalika kamannin sa suna nan se dae kamar ma yanzun an k'ara masa kyau ne "Barka dae.." Abba ya fad'a "Ka zauna mana" Yah Sadeeq ya fad'a ganin har lokacin be zauna ba, shiru ya d'an yi yana jiran jin ta bakin wani daga cikin Abba ko Umma, kamar sun san me yake nufi kuwa se Umma tace "Ka zauna mana" se a lokacin ya zame takalmin k'afar sa sannan ya zauna har kuma lokacin be kalle su ba, ya ajje envelope d'in dake hannun sa a gefen sa, seda ya d'an numfasa sannan ya fara magana a nutse "Abba.. Zuwa nayi in rok'i alfarmar ka don Allah.. Sannan kuma in baka hak'uri akan abinda ya faru.. bazan 6oye maka ba Abba a lokacin da naga wani na na neman auren Ayrah hankali na ya matuk'ar tashi, nasan abinda ya kamata inyi shine in d'auko ta in dawo muku da ita, toh amma bani da tabbacin idan na dawo da ita zaku aura min ita, ko kuma ita ta amince da aure na saboda yadda ta nuna a lokacin kwata kwata itama ba zata ta6a aure na ba, kuma a lokacin bansan dalilin ta na hakan ba Abba yasa kawae na yanke shawarar neman auren ta acan d'in idan yaso idan muka dawo na shirya kar6ar koma wane irin hukunci ne, duk da banyi la'akari da ku yaya zaku d'auki al'amarin ba, amma don Allah kuyi hak'uri Abba, ku min afuwa don Allah.." ya k'are maganar yana sauke numfashi kamar baze d'ora ba se kuma ya janyo envelope d'in gefen sa ya cigaba da fad'in "A yanzu na gano dalilin da yasa kuka hanani auren Ayrah Abba, ku dubi girman Allah ku yafe mana mu masu laefi ne, kuma yanzu haka gashi na dawo maka da takaddun ka badan mu biya ka abinda muka yi maka ba, a'ah inaso ne na fara warware wannan matsalar kamin inje gata gaba.." kallan envelope d'in Abba yayi sannan ya girgiza kae yana murmushi "Shi Kabeerun ne ya aeko ka?" seda ya d'an yi shiru sannan ya girgiza kae cike da takaeci kana yace "A'ah Abba.." sake girgiza kae Abba yayi dama yasan za'a rina "Ka d'auki takaddun ka maeda su inda ka gan su, duk lokacin da Kabeeru ya gane yayi laefi kuma yana neman yafiya ta seya d'auko yazo ya bani, kada ka sake saka kan ka cikin wannan maganar.. Zancen aure kuma dani da mahaefiyar ta duk bamu so ba, ba kuma mu ta6a tunanin hakan ze kasance ba saboda abinda mahaefin ka yayi, se dae ya zamuyi? Allah ya riga ya rubuta ita matar ka ce, ko da ba ta hakan ba in dae Allah ya nufa se anyi auren nan se kaga dukan mu ma mun mutu kuma a d'aura muku auren, dan haka ni na yafe maka daga kae har Ayrahn in dae akan auren nan ne, na san iyayen ka ma basu sani ba saboda haka wannan ya rage naka kaje kayi musu bayani da kan ka, ku sasanta da kan ku.." a hankali ya lumshe idanun sa yana jin wani nauyi na raguwa daga cikin k'irjin sa, ko babu komae ya samu matsala d'aya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70