Skip to content

Chapter 70

Chapter 70

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 990 words 0 views Progress saved
Download Book

nutse "Ya kamata ka koma bakin aekin ka haka nan likita.. Kasan bana son zama haka nan, ko kuma dae kada wannan satin ya cinye baka koma ba.." "In Sha Allah" Rk ya fad'a, a ran sa yana sak'a ta yadda ze fara yiwa Abbu zancen Abba, sam be san ta inda ze fara ba, ko ya sak'a ga ta inda ze fara d'in se yaga beyi ba seya bar shi, ya kuma tsarawa yaga beyi ba ya kuma barin sa. Wayar Abbu ce tayi k'ara, ya kalli me kiran nasa sannan yace sanda wayar ke hannun sa yana shirin amsawa "Bari na amsa kira.." yayi maganar yana kara wayar a kunnen sa, be san me suke tattaunawa cikin wayar ba se dae kawae yana jin Abbun na magana da alama akan kud'i ne suke magana, magana ta k'arshe da Abbun yayi itace taja hankalin sa "What? Me kake nufi? Wallahi baze ta6a yiwuwa ba, idan ma makirci kake k'ok'arin shiryawa ka fasa yi, dan kuwa ni ba shashasha bane, 50 millions wasa ne?" yayi maganar cikin d'aga murya kuma cikin 6acin rae, lokaci d'aya kuma yana jefar da wayar gefe sannan ya koma ya zauna kan kujerar da6ass zuciyar sa na bugawa "Abbu lafiya kuwa?" shine abinda ya iya furtawa yana kallan Abbun da gumi ke tsatstsafowa akan fuskar sa duk da yadda sanyin A.C ke ratsa gaba d'aya parlourn, kamar jira yake yi ae kuwa ya soma fad'in "Ni Mukhtar ze yiwa shashanci? Tunda nake ban ta6a yadda da kowa ba bayan kae da d'an uwa na, ta yaya ma zan yadda da wani inje yaci amana ta, ban san kuma wane tsautsayin ne ya sanya na bawa Mukhtar har 50 millions ba, se gashi mutumin banzan nan na fad'a min wae an masa kutse cikin Account d'in an kwashe duka kud'in, shin wannan maganar kamawa ce? Ni ze mayar mutumin banza? Toh wallahi seya fito dasu, k'arya yake yi so yake ya cuce ni Allah ya kama shi, nayi dana sanin shigar da bare cikin harkar kud'i na, toh wallahi se yayi kashin kud'in nan ko zeyi mene, millions 50 fa?" Abbu ya k'arashe maganar yana mik'ewa har lokacin yana jin zafi cikin k'irjin sa, sam ya kasa zama se safa da marwa yake cikin d'akin daga k'arshe ma seya haye sama kawae ya bar Rk da tunda ya fara magana bece masa uffan ba a zaune. Bin sa yayi da kallo sanda ya ida hayewa saman kana ya dawo da duban sa cikin parlourn, lumshe idanun sa yayi cike da takaecin halin mahaefin nasa, be so haka halin sa yake ba, amma duk da haka zeyi k'ok'arin chanja shi, se dae wannan kad'ae ya isa ya nuna maka Abbun na tsoron kada a aekata masa abinda yayi wa Abba shiyasa tun farko yak'i yadda ya shigar da bare cikin harkokin kud'in sa, se dae yau gashi ya shigar kuma an samu akasi, amma da yake shi ga abinda ya aekata sanda aka yadda dashi se yake ganin kowa ma haka ne, cutar sa akayi aka ci amanar sa ba tsautsayi bane. Sosae zuciyar Rk ke zafi, daze iya da yau d'in ze sanar da Abbu yasan komae game da zancen su shi da Abba, da irin abinda ya aekata masa, daze iya daya tsaya gaban Abbun ya fad'a masa abubuwan dake ta yawo a cikin kan sa, se dae baze iya ba, har lokacin Abbun na matsayin uban sa ne shiyasa yake neman hanya mafi sauk'i daze isar da sak'on sa wajen Abbun, koda hakan ze saka Abbun yayi nadama ya nemi yafiyar Abba akan abinda yayi masa shi da iyalin sa, ya tarwatsa musu farin ciki da rayuwar jin dad'i zuwa ta k'unci, baya so ya bar Abbun se ranar al_k'iyama sa had'e da Abba, sam baya fata hakan ya kasance. Mik'ewa yayi a hankali dae_dae lokacin da yake lumshe idanun sa lokaci d'aya ya fesar da huci daga bakin sa, be san me ze cewa Abbun ba koya shiga cikin d'akin, be san da wane baki ze yiwa Abbun magana ba, dan ze ga kamar idan yayi maganar zata zama kamar magana ce a fakaece yake fad'awa Abbun, hakan ne ya sanya shi jan k'afafun sa ya bar d'akin.. .... Da mamaki Abba ke kallan Alhaji Mato dake tsaye k'ofar gidan nasa jikin wata hamshak'iyar mota er uban su, lokaci d'aya annurin fuskar sa ya gushe, kamar ya juya ya koma se kuma ya kalle shi yace a nutse "Me ya kawo ka k'ofar gida na?" wani murmushin gefen baki Alhaji Mato ya saki kana ya sanya hannu ya gyara zaman babbar rigar jikin sa, hannu ya mik'awa Abba bayan ya matsa kusa dashi sosae yace "Ae ka bari mu gaesa koh?" ya fad'a da murmushin da Abba ya kasa gane manufar yin sa "Kaaga zaka fad'i abinda ya kawo ka ko kuma nayi tafiya ta?" "A'ah ae bata kae ga nan ba Alhaji Kabeeru.." ya k'are maganar yana sakin wata dariya kafin ya d'ora da "Wannan zuwan ae ba nawa bane naka ne" ya k'arasa maganar yana nuna Abban, da mamaki Abba ya cigaba da kallan sa dan yau d'in gaba d'aya Alhaji Maton ya chanja kamar bashi ba yana wasu abubuwa a juye wad'anda ya kasa gane su, jin Abban bece komae ba ya sanya shi fad'in "Zuwa nayi a bani kud'in da nayi asara akan d'iyar ka, dubban kud'ad'en dana kashe akan karatun ta, dubban kud'ad'en dana kashe dan naga ta zama wata amma saboda bak'in ciki irin naka wanda har d'iyar ka ma bakya k'yale ba ka saka k'afa kayi fatali dani d'in dae dazan rufa muku asiri.. Saboda haka yanzu base gobe ba ka shiga gida ka fito min da kud'i na gaba d'aya kada ko naira 5 tayi ciwo, dan kuwa babu inda zan je se kud'i na sun fito.." Alhaji Mato ya fad'a yana cigaba da kallan yanayin Abban daya chanja lokaci guda.. Mhiz Innocent....✍️

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70