Chapter 18
Chapter 18
sa da yanayin fitar sa ya sauya cikin k'ank'anin lokaci "Wacece wannan yarinyar?" ya fad'a sanda wani malami a cikin makarantar ya k'araso yana gaeda shi, amma shi sam be lura ba hankalin sa na kan Ayrah ne, da mamaki malamin ya kalli inda ya nuna da hannun sa yace yana kallan Alhajin "Wa kenan yalla6ae?" "Wata farar yarinya data shiga Office d'in nan yanzu ita da wata.." "Ohk wae Ayrah Ibraheem Khaleel?" "Ayrah!" ya ambata a fili, "kamar yadda sunan ke da dad'i haka mamallakiyar sunan ke da kyau" ya ayyana a ransa kafin a fili yace "K'warae wacece ita?" "D'aliba ce a makarantar nan.." malamin ya fad'a yana mamakin jin tambayoyin dake fitowa daga bakin Alhajin "K'arin bayani.." Alhajin ya fad'a yana kafe Malamin nan da jajayen idanun sa da suka kasance na halitta, seda yaja numfashi kad'an sannan ya furta "Hadda ita dae a cikin wad'anda suka ci qualifying, so yanzu akwae wani important issue ne yasa principal kiran su" ganin dae baze samu wani cikkaken information daga wajen sa ba ya sanya shi fad'in "Ohk ya yanayin k'wakwalwar ta yake?" seda ya d'an yi shiru sannan yace yana murmushi "Gifted, a cikin ajin su ita ke d'aukar first position koda yaushe" "Thank u" Alhajin ya fad'a yana mik'awa Malamin hannu suka gaesa sannan yayi gaba, drivern Alhajin ne ya matso kusa dashi kansa a k'asa yace "Yalla6ae kana buk'atar wani abu ne?" "A'ah.." ya fad'a yana kallan wanda ya fito daga cikin motar yana maeda waya cikin aljihu, da alama waya ya gama yi a cikin motar, shima kamar Alhajin zasu yi shekaru kusan d'aya se dae banbancin kamanni, dae_dae lokacin da Ayrah ke fitowa daga cikin Office d'in se dae wannan karon ita kad'ae ce, Alhajin ya kalli abokin sa Alhaji Baba yace "Wannan yarinyar ta min" bin Ayrah Alhaji Baba yayi da kallo kana ya dawo da duban sa kan Alhaji yace "Wannan abar?" jinjina kae yayi yana cigaba da binta da kallo harta 6acewa ganin sa "Wannan ae se dae ka raene ta yalla6ae.." Alhaji Baba ya fad'a yana kallan sa "Babu damuwa zan raene tan, daga yanzu zuwa sanda zata gama Secondary School, zan kashe ko nawa ne a kanta nasan ka gane abinda nake nufi.." murmushi Alhaji Baba yayi kana yace "Kana tunanin wannan yarinyar zata aure ka?" "Meze hana? Ina da wani aebun da 'ya mace zata guje ni ne? Musamman ma irin wannan da take zuwa makarantar talakawa irin wannan?" Alhajin ya fad'a yana kallan Alhaji Baba "Iyayen ta fa?" "Me kud'i suke yi? Ina tunanin ka manta nace zan kashe ko nawa ne a kanta koh?" Alhaji ya katse shi da fad'in hakan "A nemo min wace ce ita, su waye iyayen ta, menene burin su na rayuwa, dukka zan cika musu shi komae girman sa.." ya fad'a yana kallan drivern sa.... *_Doctor RK is coming...._*😌🌚 Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 011_012 ___"Sir mun binciko maka wacece ita" cewar wani d'an matashi daya shigo cikin wani hamshak'in parlour daya gaji da had'uwa, murmushi Alhajin yayi yana kallan sa sannan yace "Good job Muttala, wacece ita? Menene burin nasu? Yaya iyayen ta suke?" gyara zama matashin saurayin da aka kira da Muttala yayi kana yace "Kamar yadda muka tsammata talakawa ne futuk yalla6ae, kuma idan iyayen nata nada buri toh be wuce na d'iyar tasu tayi karatu ba" "Sure? Kuma kana nufin ka bincika da kyau?" Alhajin ya fad'a "Sosae kuwa ranka ya dad'e, idan da k'ari dae toh se dae ko a bawa baban nata jari, dan wallahi ranka ya dad'e da gani yana shan kebula" ya fad'a yana wani maraeraece fuska kamar wanda yaga wani abun mara dad'i, se kuma ya sake gyara zama yace "Amma wani hanzari ba gudu ba yalla6ae, ina ga da zan iya bada shawara da nace kar ka fara tarar abin daka haka, a fara da ita yarinyar saboda gudun matsala" jinjina kae Alhajin yayi cike da gamsuwa da maganar Muttalan yace "Hakane, yanzu abinda nake so, ayi duk abinda ya dace akan karatun yarinyar, kome take buk'ata zan samar mata shi, kada ayi sanya akan wannan al'amari kuma bana so a samu matsala" "Babu damuwa Alhaji..". Muttala na fita daga d'akin kae tsaye makarantar su Ayrah ya wuce direct ya tafi wajen Principal ya sanar dashi sak'on Alhaji, sosae shi kansa Principal yayi mamakin jin wannan lamari amma tunda abin na manya ne seya dena ganin laefin sa, ya maeda hankali wajen sanar dasu abinda Ayrahn ke buk'ata daya danganci makaranta.. Da sallama ya shigo cikin gidan, duka suka amsa masa sanda yake k'arasowa cikin tsakar gidan da suke zaune, Ayrah dake kwance kan cinyar Umma tana kalmashe mata dogon gashin kan ta me santsi, Umman ta mik'e ta k'arasa wajen Abba kafin ya gama shigowa, ta masa sannu da zuwa sannan suka k'araso suka zauna a tsakar gidan "Matso ina zaune na k'arasa miki kalbar.." Umma ta fad'a tana kallan Ayrah data d'auki mayafi ta yafa a kanta, seta kwa6e bakin ta sannan tace kamar za tayi kuka "Don Allah Umma a bari haka nan" harara Umma ta jefa mata, Abba dake kallan su yayi murmushi sannan yace "A'ah abar Auta ta huta haka nan, kinga ma nazo miki da wani albishir.." ya fad'a yana sanya hannun sa cikin aljihu ya d'auko kud'i sannan ya mik'a mata yace "Ga kud'in nan sun samu" ya fad'a yana murmushi, hannu biyu Ayrah ta saka ta kar6a sannan tana murmushi ta kalli Umma kana ta maeda duban ta kan Abba tace "Abba Albishirin ka.." Seya kalle su su duka kafin yace "Albishir kuma? Ikon Allah... Toh goro.." yayi maganar duka a lokaci d'aya, Ayrahn ta cigaba da fad'in "Abba PC da kansa yasa aka kira ni ya fad'a min wae an biya min kud'in ma saboda k'ok'ari na" ta k'arasa fad'a da k'ayataccen murmushi akan fuskar ta, shiru na wasu en sakanni kafin Abba yace "Ikon Allah, toh Masha Allah Auta, Allah ya k'ara miki k'ok'ari Uhmm?" "Ameen Abba" ta fad'a tana mik'a masa kud'in hannun ta, seya sanya hannu ya maeda kud'in cikin hannun ta sannan yace "Ki rik'e su a wajen ki bana so na kashe, in case koda wata matsalar zata taso, duk da bama fata ma" seta mik'awa Umma kud'in tace tana Kallan Abba "Allah ya k'ara arzik'i Abba.." ..... A cikin en tsukun su Ayrah suka zana NECO, sun shafe satittika suna gabatarwa, sosae Ayrah ta dage wajen yin karatu ko dan ta cika burin iyayen nata na son tayi karatu, a kwanakin sau da dama takan hana kanta bacci dan dae tayi karatun, har wani lokacin se Umma ta saka ta tayi bacci sannan take hak'ura da karatun tayi baccin.. .. Tun d'azu bacci ke ta barazanar d'aukar ta amma take ta basarwa dan jira take Abba ya dawo saboda tun d'azu ya fita a dalilin rasuwa da akayi a cikin layin nasu, bata k'ara minti 5 a zaune ba kuwa ta jiyo sallamar sa daga tsakar gida, seta tashi zaune tana janyo d'an kwalin ta daya sa6ule daga kanta ta yafa shi ta zubo dashi gaba sannan ta fito tsakar gidan "Abba sannu da zuwa.." ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70