Skip to content

Chapter 45

Chapter 45

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

yi shiru bayan ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da fad'in "Wannan mutumin ya d'auko ki ne dan a d'aura muku aure dashi na dindindin, shiyasa ni kuma zan k'wace ki daga tarkon sa da kike k'ok'arin fad'awa..." da ya kae k'arshen maganar seya sake dakatawa yana cigaba da nazarin ta, sanda ta dena kukan se sheshshek'a da take yi kan ta har lokacin na kan gwuiwar ta, se a lokacin ta saka hannun ta ta share hawayen da suka k'i tsayawa da zuba a fuskar ta tace cikin raunanniyar murya "Idan da gaske taemako na zaka yi toh ka kira min Abba na, ko kuma ka maeda ni gidan mu saboda bana son ganin ka" tsayawa yayi ya cigaba da kallan ta yanda take maganar bilhak'k'i da gaskiyar ta, shi har yanzu idan tana wani abun mamaki take bashi, meyasa ta fishi d'aukar zafi haka? Meyasa duk da abinda Abban ta yayi wa Abbun sa besa ya guje ta ba se ita? Meyasa take abu kamar da mak'iyin ta take tare? Meyasa ta chanja lokaci d'aya? Lumshe idanun sa yayi yana hana yanda ran sa ke neman 6aci tasiri, sosae zuciyar sa ke masa zafi na maganganun ta amma ya daure ya sake runtse idanun sa na tsawon sakanni sannan ya bud'e su a kan ta sanda suka yi wani ja kamar wanda abu ya zubar wa cikin ido, seya maeda kallan sa kan ta sannan yace sanda bugun zuciyar sa ke cigaba da k'aruwa "Wannan shine abinda kike so na miki? Ki sani ba zaki ta6a barin garin nan babu aure akan ki ba, ko dae ki bari ki auri wancan mutumin ko kuma ki amince da aure na na Contract, The choice is yours.." yayi maganar yana lumshe idanun sa kafin ya d'ora da fad'in "Idan kuma kina tunanin abinda kike tunani shine mafita.. well.. se kije ki samu wad'anda suka sato ki dan a d'aura miki aure da d'aya daga cikin su kice su baki waya ki kira Abban ki..." ya k'are maganar da wani irin murmushin takaeci daya fice daga gefen bakin sa, daga haka ya juya yana shirin ficewa daga soron, bata san sanda ta mik'e da wani irin sauri ba se kawae tsintar hannun sa yayi cikin nata, ya dakata lokaci d'aya yana lumshe idanun sa lokaci d'aya kuma yana jin yanda jikin sa ya amsa, se kuma ta sake shi kafin kamar zata fashe da kuka ta furta "Na amince!!" ta fad'a dae_dae lokacin da wani kuka me sauti ya k'wace mata, seda ya sake runtse idanun sa kafin ya juyo inda take, ya sanya hannun sa cikin aljihu ya fiddo da wata takadda da biro sannan ya mik'a mata ba tare daya dubi kukan da take yi kamar ran ta ze fita ba "Ki saka hannu!" ya fad'a yana mik'a mata, kamar ba zata d'ago ba se kuma a hankali ta fara rage sautin kukan nata sannan ta sanya hannu ta kar6a, sosae bugun zuciyar ta ke k'aruwa ta kar6i takaddar daya mik'a mata, tsayawa tayi kawae tana kallan takaddar kamar me karatu ko me nazarin abinda ke cikin takaddar, hawayen da yak'i tsayawa a idanun ta se sauka yake akan takaddar, wajen minti 1 tayi a hakan da dae ta fahimci bata da wata mafita se kawae ta d'aga biron ta d'ora shi kan takaddar, duk da yadda hannun ta ke rawa hakan be sata dakatawa ba se da tayi signature sannan ta jefar da takaddar daga hannun ta tana runtse idanun ta, bata jira ta sake jin komae daga bakin sa ba ta mik'e ta fara takawa a hankali saboda jirin dake d'ibar ta, hakan ne ya sanya ta yin layi kamar wadda tayi maye, bin bayan ta yayi da kallo sanda ta 6acewa ganin sa daga inda yake yana jiyo sheshshek'ar kukan ta, ya kae minti d'aya a hakan kamar wanda aka sassak'a sannan ya lumshe idanun sa ya saka hannu ya d'auki takaddar kana ya fice daga soron. Kae tsaye cikin motar sa ya koma ya jinginar da kan sa akan kujerar daya kwantar da ita, idanun sa a lumshe zuciyar sa na harbawa da k'arfin gaske, hannun sa dake d'auke da takaddar ya rufe ta a cikin hannun nasa kamar wanda ze yaga takaddar, se kuma ya bud'e hannun yana sauke numfashi a hankali, wayar sa dake ajje kan kujera ce tayi ringing, se a lokacin ya bud'e lumsassun idanun sa ya d'ora akan wayar "Abbu" ya bayyana akan screen d'in, seya maeda idanun sa kawae ya rufe yana cigaba da sauke numfashi akae akae, be d'aga wayar ba har ta gaji dan kan ta ta dena ringing d'in sannan ya janyo ta ya kashe ta gaba d'aya, gaba d'aya zuciyar sa a dame take yanzu haka, ya rasa ma meya kamata yayi, baya tunanin koya d'aga wayar ma ze iya cewa wani abun, dan haka k'in d'agawar kawae shine mafita. ... B'angaren Ayrah kuwa a tsakar d'akin ta zube tana sakin wani gigitaccen kuka me tsuma zuciyar me sauraro, zuciyar ta gaba d'aya a cunkushe take, ta rasa abinda zatayi, ta rasa tunanin daya kamata tayi, abinda ta sani kawae shine yanda zuciyar ta ke bugawa kamar zata faso k'irjin ta ta fito, ta kae fiye da minti 30 tana kukan sannan ta fara sauke ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma tana neman kan wani d'an madaedaecin gado dake cikin d'akin ta d'ora kan ta akae cikin rashin sanin abinyi. ... "Yalla6ae kayi hak'uri ka zauna mu samo mafita" Muttala ya fad'a yana kallan Alhaji Mato daya kasa zama, idanun nan nasa sun sake ja kamar garwashi, haka zalika bak'ar fuskar sa ta sake had'ewa cikin rashin walwala "Waye shi? Wanene uban shi? Me yake tak'ama dashi? Ya akayi yasan da plan d'in mu? Ya akayi ya biyo mu cikin garin nan?" shine abinda Alhaji Maton ya fad'a a zafafe "Ka kwantar da hankalin ka Yalla6ae, zuwa gobe zan bincika maka waye shi" wani banzan kallo Alhaji Mato ya watsawa Muttala kafin yace "Muna da wannan lokacin? Tambayar ka nake muna dashi?" ya k'are maganar yana kallan sa, shiru Muttala yayi yana sake tunanin wata mafitar, hakan ya sake bawa Alhaji Mato damar yin shiru shima yana nazarin abinda ya kamata yayi kafin goben "Ya shiga gona ta, bazan k'yale shi ba wallahi, yana so yayi wasa dani, ba zeji da dad'i ba, Muttala asan yadda za'ayi a gama mun dashi kafin goben, shi kad'ae ne matsala ta a yanzun.." Alhaji Mato ya k'are maganar yana kallan Muttala "An gama ranka ya dad'e" .... Washe_gari da safe wajen k'arfe 8 tana zaune kan dadduma kamar maraeniyar data rasa uwa da uba, manyan idanun nan nata sun sake yin zuru zuru, ga yunwar da take ji amma saboda tashin hankalin da take ji ta kasa kae koda ruwa ne cikin bakin ta, haka nan kawae take zaune, ita ba Azumi ba ita ba cin abinci ba, idan ka gan ta seta baka tausayi musamman yadda har lokacin hawaye be bar zuba akan kuncin ta ba duk da yadda ta dena kukan amma hakan be hana hawayen zuba ba, ita kad'ae tasan yadda take ji a cikin zuciya, k'wak'walwa da gangar jikin ta, tana nan zaune gaba d'aya

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70