Chapter 27
Chapter 27
yayi yabi kowa ya kar6a paper sa, wasu duk suka baada yayin da wasu k'alilan basu bayar ba saboda basu gama ba, Monitorn bebi ta kansu ba ya had'a paper hannun sa yabi bayan Rk daya fice daga cikin ajin har zuwa motar sa, ya bud'e ya shige motar sannan Monitorn ya ajje masa papers d'in a front seat, dae_dae sanda yake tada motar su 3 suka fito, Ayrah se wata er ajin tasu Fateema, sannan wani su kad'ae ne basu bayar ba, Monitor ya kalle su sannan ya kalli Rk yace a hankali "Sir.. Pls wad'anda basu bayar ba!" da mamaki Rk ya kalle shi kamar ba zece komae ba se kuma yace "Saboda raeni?" da sauri ya girgiza kae lokaci d'aya yana furta "No sir, ina sauri ne ban kar6i ta sun ba saboda kada dukan mu mu rasa, Sorry sir" "Leave them, next tym zasu yi saurin baka.." yayi maganar sanda yake maeda kan sa kan driving d'in daze soma "Pls Sir, ayi musu hak'uri ba dan halin su ba" yayi d'an shiru sannan yace bayan ya fesar da iska daga bakin sa "Su wakilta mutum d'aya a kae min office" ya fad'a yana yin gaba "Thank u so much Sir" Monitorn ya fad'a yana mik'ewa tsaye zuwa bakin class d'in, daga inda take ta runtse idanun ta tana ganin kamar tun yanzu tayi failing course d'in tunda gashi ta rasa C.A, tana shirin komawa cikin ajin hannun ta akan fuskar ta tana ji kamar ta fashe da kuka ta jiyo muryar Monitorn nasu na fad'in "Ayrah.." seta dakata lokaci d'aya tana juyowa, ya kalli yanda fararen idanun ta suka sauya kala sannan yace bayan yayi murmurshi "Doctor yace a cikin wad'anda ba kuyi submitting Paper ku ba ku wakilta mutum d'aya ya kae masa" lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin dad'i na ratsa ta, seta kalli Fatima dake gefen ta itama rik'e da tata Paper a hannun ta tace tana kallan namijin da shima be bada ba, bata san sunan sa ba dan ita harkar matan ajin nasu ma bata kowa take shiga ba ballantana ta mazan ajin nasu "Gashi zaka kae masa?" ta k'are maganar tana kallan sa, Monitor ya kalle ta yace "kin san yadda za'ayi? Ki kar6i Paper su ki had'a ki kae masa" da mamaki ta kalle shi jin furucin sa kafin tace komae ya sake jinjina kae, da sauri ta girgiza kae sannan tace da sauri tun kafin ma ya sake cewa komae "A'ah ba zan iya ba.." tayi maganar da dukkan gaskiyar ta, dan a yadda take ji koda za'a ce sun rasa exam ne ba C.A ba ba zata iya zuwa wajen mutumin ba, cikin maraeraecewa Fateema tace "Don Allah Ayrah kije ki kae kin ji?" "Toh ke waya hana ki zuwa?" ta fad'i abinda take sak'awa cikin ran ta, kafin duk suce komae ta sake fad'in "Babu inda zan je ni" tayi maganar kamar zata saka kuka, hannu Monitor ya saka ya kar6i takaddun hannun su duka har ta Ayrah sannan yace "Zo muje mu kae masa" tunda taga ya kar6a se kawae ta bishi a baya kamar wata doluwa, a haka har suka k'arasa Office d'in Rk, seya kalle ta bayan sun dakata daga tafiyar yace "Kinga abinda yasa nace ki kae masa da kan ki, su Fateema sun fiya kaud'i, kuma kin san halin doctor.. kada suzo su janyo muku shiyasa nace ke kije, yanzu dae kije ki kae kada lokaci ya k'ure yace baze kar6a ba" hannu ta sanya ta kar6a fuskar ta a cunkushe, sannan ta runtse idanu tana karanto addu'ar da duk tazo bakin ta kana ta fara takawa zuwa bakin Office d'in, da sallama d'auke akan la66an ta ta shiga cikin Office d'in, ba tare data kalli kowa ba ta zube akan k'afafun ta, wani irin sassanyan k'amshi ke tashi cikin Office d'in, wanda ya had'e da k'amshin turaren sa da kuma shi kan sa na Office d'in ga kuma sanyin A.C hakan ba k'aramin k'arawa yanayin Office d'in dad'in shak'a yayi ba. Da mamaki Muneerah dake zaune kan kujera ta kalle ta, seta saka hannu ta zame k'aramin glass d'in dake fuskar ta ta cigaba da kallan ta "Malama menene zaki shigowa mutane waje without even taking excuse?" taji maganar daga gefen ta, idan kujerar da Muneerahn ke kae ta d'ago ta kalle ta toh Ayrah ma ta kalle ta, seta d'aga kae a hankali ta kalli inda yake zaune kan kujera yayi shiru hannayen sa rik'e da ha6ar sa kamar me tunani "Sir.." karo na farko kenan data ta6a yi masa magana, ita bata so ma hakan ta faru ba, so tayi har ta gama makarantar wata magana ba zata ta6a had'a ta da shi ba, idanun sa masu kaefi ya d'aga ya kalli Muneerah dake sake fad'in cikin kufula "Kamar dake nake koh?" lumshe idanun ta Ayrah tayi ba tare data juya ta kalli Muneerah ba tace "Sir test d'in mu na kawo.." tayi maganar tana mik'ewa daga zaunen da take ta ajje masa kan bench d'in dake gaban sa, jin bece komae bane ya sanya ta mik'ewa tana jin k'irjin ta na bugawa lokaci d'aya kuma tana fatan Allah yasa kada yace wani abun, ya kar6a kenan "Don't ever try dis mistake again.." ta jiyo daddad'ar muryar sa yana fad'in hakan kuma a hankali kamar wanda akawa dole, ba tare data kalle shi ba ballantana bugun zuciyar ta ya k'aru tace "In Sha Allah" tana shirin fita ta jiyo muryar Muneerah na fad'in "Kin ci sa'a yau an miki uzuri, saboda haka se ki kiyaye" ta fad'a ita a lallae dole se an gane wata ce ita a wajen Rk d'in, kallan ta kawae Ayrah tayi tana jin wani irin takaeci da haushi na musamman na zuwa suka tirnik'e ta, dan haka yanzu ma ba tace komae ba se sake d'auke kan ta da tayi, daga haka ta sanya k'afa ta fice daga Office d'in, galala Muneerah ta bita da kallo sanda ta gama ficewa daga Office d'in sannan ta dawo da duban ta kan Rk tace "Baby wannan d'alibar ka ce?" kallan Muneerah yayi kallo irin na cikin ido wanda ya sanya ta kauda kan ta gefe se dae har lokacin bata ji yace komae ba dan haka ta sake furta "Baka tunanin shirun da ka mata bayan abinda tamin kamar ze janyo min raeni ne" "Meye had'in ki da ita?" yayi maganar cikin basarwa, se tayi shiru kawae tana mamakin wannan mutumin, yaja Papers d'in data kawo ya had'a su da ragowar sannan ya mik'e yana zura wayar sa cikin aljihu yace "Zan fita" "Da wuri haka Baby? Ina zaka je?" yamutsa fuska yayi ba tare da ya bawa tambayar ta ta muhimmaci ba yace "Zaki tafi ne?" a shagwa6e ta furta "Haba haba kae kuwa Yaya na, ni fa hira nazo na taya ka" kansa ya d'an dafe dan shi yana jin kamar ciwon kae take k'ok'arin saka masa, a yayin da ita a 6angaren ta tana yin komae ne dan saboda ta burge shi, jin da tayi bece komae bane ya sanya ta fad'in "Ohk muje na raka ka" ta fad'a tana murmushi "No babu buk'ata" ya fad'a yana d'aukar key d'in
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70