Skip to content

Chapter 59

Chapter 59

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

tsoro kada ace zumuncin su ya rabu saboda auren nan, dan a yadda yake ji har abada baze iya zama da wata a matsayin matar sa ba in dae ba Ayrah ba, toh ina ze kae ta? "Yaya na!" ta katse masa tunani da fad'in hakan "Wannan ne dama dalilin kiran?" ba tare data kawo komae ba tace tana murmushi "Ehh shine kawae.." "Ohk" ya fad'a yana katse wayar sannan ya jefar da ita gefe "Hello" ta furta bayan jin kamar kiran ya katse, seta sauke wayar daga kunnen ta tana kalla cike da takaecin katse wayar ba tare da sun k'are maganar ba, seta cigaba da kallan wayar kamar me nazari ko kuma me kallan wani abun a cikin wayar "Ke lafiya?" Mummy ta fad'a tana kallan ta "Mummy, Yah Suraj ne mana, Mummy har yanzun fa baya d'aga waya na ya yake so zuciya ta tayi?" ta k'are maganar kamar zata fasa ihu, tsaki Mummy taja sannan tace "Dallah rabu da shi, kwana nawa ya rage ya shigo hannun ki? Ke dae kawae ki maeda hankalin ki wajen gyaran jikin nan, dukkan magungunan nan ki tabbatar kina shan su kamar yadda suke a tsare, baki ga har kin fara chanjawa ba kina ta cika tako ina? ina me tabbatar miki a hannun ki zaki kama shi, dan kuwa da kan shi ze dinga bibiyar ki ba dae ke ki bi shi ba.." _*Ina fatan yanzu kun fahimci abinda nake k'ok'arin nuna muku, kowanne abu idan kaga writer tayi akwae dalilin yin sa, akwae dalilin rubuta shi, babu yadda za'ayi kayi abu babu dalili, nayi hakan ne dan janyo hankalin wasu iyayen masu saurin yankewa 'ya'yan su hukunci ba tare da sun yi dogon bincike b duk kuwa sa irin yaddar da kayi musu, su kan su ae gashi nan yanzu sun yi nadamar hakan da suka yi, dama kuma shi novel ya gaji haka, na san dukan ku baku yi tsammanin Umma ko Abba wani a cikin su ze d'auka Ayrahn da kan ta guduwa tayi ba, dukan ku nasan kun ta'allaqa ne akan zasu zata sace ta akayi, wannan dalilin ne yasa na juya muku kwanya, babu yadda za'ayi abinda readers ke tunani kae kuma kayi shi a wani lokacin, dan kuwa littafin ze zama lami ne, ze zamana kowa da kowa yasan abinda ze faru a gaba kenan, wannan ba shine kyakykyawan novel ba wanda tun farkon fara karantawa kasan abinda ze faru a gaba. Ina fatan za'a dena tambaya ta dalilin da yasa nayi hakan.*_ Kuyi manage da wannan pls.. https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 037 ___"Allah ko Mummy na?" Muneerah ta fad'a tana murmushi cike da jin dad'in zancen Mummy, murmushin itama Mummy ta maeda mata dashi kana tace "Kada ki saka kokwanto a ran ki, kamar yadda na fad'a haka ne ze kasance" farr tayi da idanun ta dake d'auke da lashes na kanti, wanda da tasan yanda ya sake shigar da k'ananun idanun ta da bata saka ba, amma ita gani take haka zalika ji take baya ita, mik'ewa tayi tana kallan Mummy tace "Yunwa nake ji Mummy kin gama abinci ne?" yamutsa fuska Mummy tayi sannan tace "Se dae idan yunwar kike ji ki dafa ko indomie ce ki ci" bata sake cewa komae ba se hanyar kitchen data wuce kawae. ... Sanye yake cikin k'ananan kaya, fuskar sa ta sake yin wani shahararren kyau kamar wanda ake k'arawa kyau, haka zalika kwantacciyar sumar kan sa ta sake yin bak'i da sake kwanciya, jikin sa babu abinda ke tashi se k'amshin sassanyan turaren sa me dad'in shak'a, a nutse yake takawa zuwa part d'in Abbu cike da fata a cikin ran sa, cikin sa'a kuwa k'ofar parlourn nasa a kulle take, lumshe idanun sa yayi sannan ya bud'e ya d'an kalli gefe da gefe sannan ya sanya spare key d'in daya d'auko daga d'akin Ummee ya bud'e k'ofar, a hankali ya tura kan sa cikin d'akin, kamar wanda ya fara ganin d'akin yau haka ya soma wuwwulga idanun sa ko ina na cikin d'akin, cikin sauri ya shige bedroom d'in Abbun sannan babu 6ata lokaci ya soma bincika inda yasan Abbun na ajiye abubuwa masu amfani a cikin wajen, ya kae wajen minti 30 yana binciken be samu abinda yake nema ba, har cikin ran sa ya d'an ji sanyi kad'an akan zargin daya soma yiwa Abbun nasa, se kuma ya dakata abu na k'arshe dabe duba ba shine saman wardrobe, cikin sauri yanzun ma ya soma bincikawa har zuwa sanda ya d'akko wata leda, be bud'e ba seda ya sakko da ita k'asa, cikin k'ank'anin lokaci ya shiga fito da abinda ke cikin ta, bayan ledar akwae wata ledar a ciki sannan wata jaka, seya tsaya ya bud'e madaedaeciyar jakar dae_dae lokacin da wani envelope ya bayyana, haka nan kawae yaji jikin sa yayi wani mugun sanyi duk da har zuwa lokacin be san menene a ciki ba, a nutse ya shiga zaro takaddun dake ciki, be tsaya ba seda ya fiddo su duka kana ya saka hannu ya d'ago su cikin hannun sa ya shiga karantawa, a hankali yake karantawa kamar me tsoron karantawa ko kuma me koyon karatu, abinda dae yake guda d'in shine ya faru, wato sunan Abban su Ayrah daya fito 6alo_6alo a jikin takaddar, runtse idanun sa yayi na tsawon minti 1 yana jin 6acin rae, zafi gami da wani irin takaeci mara misaltuwa, meyasa Abbun sa yayi haka? Meyasa Abbun sa ya zamo cikin mutanen da za'a kiran su da butulu? "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" shine abinda ya shiga maemaetawa a cikin bakin sa har lokacin kuma bugun da zuciyar sa ke yi be saitu ba, ya kae wajen minti 2 a hakan sannan ya mik'e dan tuna a inda yake, beyi k'asa a gwuiwa ba wajen d'aukar ledar ya maeda ta saman wardrobe sannan ya d'auki envelope d'in ya fito dashi, karo suka kusa yi da Ummee dake shirin shigowa cikin d'akin, da mamaki take kallan sa "A'ah Raj! dama kana nan? Abbun naku ya dawo ne?" seda ya d'aga idanun sa da suka yi d'an ja saboda 6acin rae sannan yace "A'ah.." ya fad'a yana shirin wucewa "Kae lafiyar ka kuwa a kwana biyun nan?" baya a mood d'in yin magana sosae, musamman kuma a yadda yake jin 6acin rae na taso masa haka nan ya sanya shi saurin girgiza kae sannan yace "Lafiya ta k'alau.." daga nan yayi gaba yana cigaba da kare envelope d'in hannun sa "A'ah wannan envelope d'in fa?" seya dakata da sauri kamar baze juyo ba se kuma ya d'an lumshe idanun sa sannan yace har lokacin be juya ba "Takaddu ne akan asibiti, nazo d'auka ne saboda naga baya nan" jinjina kae Ummee tayi ba tare data kawo komae a ran ta ba kawae ta k'arasa cikin bedroom d'in yayin da shi kuma ya cigaba da tafiya, yana shirin fita daga d'akin Abbu ya shigo cikin d'akin sanye cikin farar dakakkiyar shadda, kallan sa yayi da mamaki yace "A'ah Raj!.." "Wajen Ummee nazo, tana bedroom.." shine abinda ya furta kawae ba tare daya kalli Abbun ba kuma be jira cewar sa ba ya fice daga d'akin, da kallo kawae Abbu yabi shi dashi

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70