Chapter 35
Chapter 35
Bahijja ta fad'a dan tana ganin kamar duk tafi su takaeci da abinda Ayrahn ta aekata musu, ta shammace su, tayi wasa da hankalin su, ta kuma nuna musu yawan shekaru ba shine wayo ba. .. Da sallama ya shiga d'akin yana sanye cikin wasu k'ananan kaya masu kyau da taushi, kan sa d'auke da facing cap data matuk'ar k'awata shigar sa ya fito yayi kyau abin sa, cikin sa'a seya samu Mummy har ma da Daddy a d'akin, ba k'aramin dad'in ganin hakan yayi ba, dan haka ya k'arasa ya zauna k'asan Carpet yace "Barkan ku da warhaka" "Barka kadae" suka had'a baki wajen fad'in hakan "Daddy dama inaso ne na shaeda maka yau zan koma Kano" "Kano kuma Likita? Wani abu ne ya faru?" seya girgiza kae kawae yana d'an lumshe idanun sa kad'an bece komae ba har zuwa sanda Mummy tace "Haba kae kuwa Raj, gaggawar ta me ce?" "A'ah Mummy.." shine abinda kawae ya fad'a, Daddy yace "Ko dae akwae abinda zaka yi ne acan d'in?" tambayar Daddyn ta matuk'ar yi masa dad'i dan haka da sauri ya furta "Ehh Daddy, akwae wani abu me muhimmanci da zan gabatar acan d'in.." "Toh shikenan babu damuwa, akwae maganar ma dama da zaku yi da Abbun naka.." be bawa zancen muhimmanci ba dan haka kawae abinda yace shine "Tohm" "Allah yayi maka albarka kaji Doctor, Allah kuma ya sanya albarka" shine abinda Mummy tace "Ameen" kawae yace duk da ita kan ta be gane akan maganar da take magana ba, ya dae fi tunanin itama taji labarin ajiye aekin da zeyi ne yasa take magana fatan alkhaeri, seya mik'e hannun sa d'aya cikin aljihun sa yace bayan yayi murmushi "Daddy bari naje na sake shiryawa" "Toh Raj, seka fito" daga haka ya fice daga d'akin. .. Ko jakar ta bata iya d'auka ba ta fad'a cikin gidan nasu da gudu tana kwad'a sallama da siririyar muryar ta, wani sanyi Umma taji ya ratsa ta jin muryar shalelen er tata, kafin ma ta kae ga k'arasowa Umman ta fito daga cikin d'akin ta, aekuwa tana shigowa ba tayi wata wata ba ta fad'a jikin Umman tana sakin dariya lokaci d'aya tana furta "Nayi kewar ki sosae Umma ta" murmushi Umma tayi ita kan ta tasan tayi kewar d'iyar ta ta sosae, dan haka itana ta rungume ta tana fad'in "Yanzu ae gani gaki koh?" seta jinjina kae har lokacin tana jikin Umma, sun kae wajen minti 1 a haka sannan Ayrah ta saki Umma tana fad'in "Umma ina Yah Sadeeq?" "Yana d'aki bacci yake" Umma ta fad'a tana kallan d'iyar ta ta "Umma wallahi yanzu Yah Sadeeq ya zama malalaci, kullum cikin bacci" ta fad'a lokacin data shiga d'akin nasa, seta hange shi kwance kan gadon idanun sa a rufe ya lullu6e rabin jikin sa da bargo, se tayi murmushi tana jin dad'in ganin sa sannan ta k'arasa ciki tana fad'in "Yah Sadeeq ka tashi, na dawo" kamar daga sama ya jiyo muryar lilin ta sa, dan haka a hankali ya bud'e idanun sa se kuwa ya sauke su a kan ta, murmushi suka sakarwa junan su sannan Yah Sadeeq yace "Yanzu kuka shigo?" "Ehh Yah Sadeeq nayi kewar ka wallahi" ta fad'a tana 6ata fuska, dariya yayi yana jin dad'in ganin k'anwar ta sa dan shi kan sa yayi kewar ta irin sosae d'in nan "Nayi kewar rigimar nan taki Auta" ya fad'a har lokacin yana murmushi "Kae Yah Sadeeq rigima kuma?" ta fad'a har lokacin dae tana 6ata fuska gami da tura baki "Toh shikenan dae ya hanya?" ya fad'a yana k'ok'arin tashi zaune, shi kan sa baya so ta gane karaya ce a k'afar sa dan ya riga yasan halin ta yanzun nan zata fishi shiga damuwa, se akayi sa'a ma tace "Yah Sadeeq kayi baccin toh, idan ka tashi se muyi hirar" ta fad'a tana kallan sa, seya koma ya kwanta ba dan yana tunanin ze iya baccin ba sannan yace "Toh shikenan Auta.." "Yawwah Yah Sadeeq" ta fad'a tana ficewa daga d'akin tana fad'in "Umma kin ga lalacin Yah Sadeeq d'in koh? Ya sake komawa baccin" ta fad'a tana k'arasawa tsakar gidan, dae_dae lokacin da Umma take fad'in "Za dae a tantance malalacin" turo d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace "Kae Umma" dariya Umma tayi tana fad'in "Toh shikenan, ina Abban?" "Aou" ta fad'a bayan ta kae hannun ta kan bakin ta sannan tace "Allah sarki Umma k'anwar Zaenab ce ta rasu shine ya tafi za'a kae ta" "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun, ashe ta rasu? Toh Allah ya ji k'an ta, ashe ba mazauniya bace" Umma ta fad'a tana tuna yarinyar data rasun wadda ba tafi wata 5 da haehuwa ba, k'arasowa Ayrah tayi ta zauna kan tabarmar da Umma ta shimfid'a, seda Umma ta zauna sannan ta d'ora kan ta akan cinyar Umman tace "Umma nazo muku da wani albishir, amma bazan fad'a ba se Abba ya dawo" "Wane albishir ne wannan?" "A'ah Umma se Abba da ya dawo" Ayrahn ta fad'a tana sake gyara kwanciyar ta kan cinyar Umma "Toh shikenan, ya exam ya karatun?" "Umma komae Alhamdulillah fa" ta fad'a tana murmushi, daga haka suka cigaba da hira, Umma nata jin labaran da Ayrahn ke ta bata, wani tayi dariya wani ta girgiza kae cike da ganin wautar Ayrahn, se dae lokaci lokaci ta kan yi shiru ta saki murmushi me k'ayatarwa idan ta tuna Rk, Umman na lura da ita amma har lokacin tak'i fad'awa Umma komae game da albishir d'in da tace zata yi musu, dan haka itama ta mata shiru kawae tana cigaba da saurarar hirar da take mata. ... A 6angaren Rk kuwa dab da maghrib ya isa gidan nasu cikin motar sa, k'atuwar harabar gida dake d'auke da manya manyan motoci a gefe guda, shuke shuke da sauran abubuwa na burgewa, kae tsaye parking lot d'in ya wuce da motar sa yayi parking nata dae_dae lokacin da wani ya k'araso da sauri yana fad'in "Barka da dawowa yalla6ae" ya fad'a yana duk'awa "Barka, a shigar min da kaya ciki" shine abinda Rk ya fad'a yana wucewa cikin tafiyar nan tasa ta nutsuwa hannun sa d'aya cikin aljihun sa, tafiya me tsayi ce yayi kafin ta sada shi da aenahin inda d'aku nan masu gidan yake, yayi murmushi sanda ya ganshi a k'ofar Parlourn Ummeen sa, babu 6ata lokaci ya sanya k'afar sa cikin k'aton hamshak'in Parlourn da sallama, Ummee na zaune kan kujera hannun ta d'auke da remote tana shirin chanja channel yayi sallama, seta ajje remote d'in akan kujera tana kallan sa sanda wani k'awataccen murmushi ya su6uce a fuskar ta tace tana k'arasawa inda yake "Oyoyo Oyoyo.." k'arasawa yayi inda take yayi hugging nata sannan ya zauna a k'asan kujerar yace cikin girmamawa "Ummee barka da wannan lokacin" "Barka dae ya hanya?" "Hanya Alhamdulillah" ya fad'a dae_dae sanda aka k'walla kiran Sallah a masallacin su dake jikin gidan nasu, se yayi saurin mik'ewa yana fad'in "Ummee bari naje" "Toh Raj seka dawo" ta fad'a tana bin sa da kallo har lokacin da murmushi kan fuskar ta. A harabar gidan suka yi kaci6us da Abbu dake sanye cikin wata dakakkiyar bluen shadda d'inkin babbar riga data matuk'ar yi masa kwarjini "Welcome my Son"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70