Chapter 39
Chapter 39
haka ya fice daga d'akin, bin sa da kallo dukan su suka yi har ya fice d'in sannan Ummee ta maeda duban ta kan Abbu tace "Kaga kuwa yanayin yaron nan?" ajiyar zuciya Abbu ya sauke sannan yace "Nagani mana, 6acin ran sa ko wani abun ba shi ne ze sa mu fasa abinda muka yi niyya ba, ina ganin gwara ma ya kwantar da hankalin sa ya kar6e ta hannu biyu a matsayin mata, dan kuwa babu abinda ze hana mu d'aura musu aure idan ranar da zamu tsayar tazo" jinjina kae Ummee ta shiga yi cike da na'am da zancen Abbun sannan tace "K'warae kuwa, kuma ina ganin wannan ce kad'ae hanyar da zamu bi dan ya manta da batun waccan yarinyar" "Ni abinda ke bani mamaki ashe har yanzu Abban Sadeeq na cikin Kano amma bamu ta6a had'uwa ba?" Abbu ya fad'a cike da mamaki, murmushi Ummee tayi kana tace "Allah yana son ka ae shiyasa hakan bata ta6a kasancewa ba" .. Kae tsaye d'akin sa ya koma har lokacin zuciyar sa na masa wani irin zafi, ya kwanta kan gadon sa ringingine yana sauke wani zazzafan numfashi daga bakin sa, hannun sa ya d'ora a kan sa tunani barkatae sunk'i barin k'wak'walwar sa, abubuwa na neman cakud'e masa, ya Abbu yake so yayi da rayuwar sa? Tun farkon rayuwar sa be san wani abu wae shi bijirewa umarnin iyaye ba, se dae gashi yau sun zo masa da wani abu da yake ganin ze iya bijire musu a kan sa, Muneerahn da idanun ta ke a bud'e, wayayyiya wadda wayewar ta tayi yawa, gefe guda kuma ga Ayrah, Ayrahn da yake mutuwar so, son da be san iya adadin sa ba, se dae ga wata k'addara na neman giftawa cikin alak'ar su, meyasa Abban ta zece baze aure ta bayan shine yayiwa mahaefin sa laefi? Meyasa ze yanke wannan d'anyen hukuncin? Duk inda d'iyar sa take yasan tana can zuciyar ta a cunkushe da hukuncin da mahaefin ta ya yankewa rayuwar su, seya mik'e zaune yana mantawa da rayuwar wata Muneerah dan kuwa yasan abu ne me matuk'ar wuya auren su ya yiwu dan baya tunanin ko da bashi da wadda yake so ze iya auran Muneerah duk da kasancewar ta er uwar sa ballantana kuma yana da ita. Wayar sa ya d'auka ya sake kiran number Ayrah se dae kamar d'azun yanzun ma abinda take fad'a masa shine wayar a kashe take, jefar da wayar yayi yana runtse idanun sa lokaci guda kuma yana sanya hannayen sa duka biyu ya cusa su cikin sumar kan sa, meya kamata ya aekata yanzun? Tabbas ba dan dare yayi sosae ba babu abinda ze hana shi tashi ya tafi gidan su Ayrahn dan yasan tabbas Abban ta ne ya k'wace mata wayar dan kada tayi magana dashi, gaba d'aya zuciyar sa ta kasa sukuni ta kasa hutawa ko dae_dae da second d'aya ne a cikin daren nan, bacci kuwa beyi ko da gangancin d'aukar sa ba balle kuma ya d'auke san. ... Tun d'azu yake sintiri cikin d'akin ya kasa zama, ran sa a matuk'ar 6ace yake so yake kawae ya tuna mafita akan wannan al'amari, be ta6a tunanin yarinyar nan da yake so er gidan Ibraheem bace, Muttala dake gefen sa shi kan sa ya kasa cewa komae, kawae yayi shiru ne yana kallan Alhaji Mato, ya kae wajen minti 5 a haka sannan ya d'aga kae yana kallan Muttala fuskar sa d'auke da wani shu'umin murmushi yace "Muttala!" "Na'am yalla6ae" Muttala ya fad'a yana d'aga kae ya kalle shi, Alhaji Mato ya nemi waje ya zauna kan kujera sannan ya fara magana "Ayi yadda za'ayi a d'akko min yarinyar nan daga daren yau zuwa safiyar gobe bana son 6ata lokaci.." kallan sa Muttala yayi sannan yace "Ranka ya dad'e satowa kuma?" shima kallan sa Alhaji Maton yayi kana yace "K'warae kuwa, zan tafi da ita wani k'auye dana ta6a zuwa aeki, acan zan samu wanda ze d'aura mana aure" jinjina kae Muttala yayi kana yace "An gama ranka ya dad'e, In Sha Allah zaka ji ni daga yau d'in zuwa gobe" jinjina kae Alhaji Mato yayi yana murmushi a ran sa yana ayyana yadda Ayrahn zata zama mallakin sa. ... Washe gari da safe wajen k'arfe 7 yana sanye cikin k'ananan kaya da suka matuk'ar amshe shi, se dae fuskar sa a cunkushe take kamar wanda akama mutuwa, haka zalika idan ka lura ma da kyau zaka ga har wani 6urmawa idanun sa suka yi, se dae da yake shi d'in na musamman ne hakan ma k'ara masa kyau yayi, wayar sa ya sake d'auka ya sake danna kiran ta a karo na barkatae, daga wannan kiran baya tunanin ze sake kira se dae kawae a tsince shi a k'ofar gidan nasu, cikin sa'a se yaji wayar na ringing, babu shiri ya mik'e tsaye zuciyar sa na cigaba da bugawa tare da sautin yadda ringing d'in ke fita. A 6angaren ta kuwa ita kan ta bata samu ta rintsa ba tun jiyan, data gama kukan ta kawae seta kwanta tayi shiru abin ta tana tunanin halin d'an adam, koda Asuba ma kafin kowa ya fito ita ta riga kowa fitowa tayi alwala tayi Sallah ta koma ta kwanta har lokacin idanun ta suna nan a yadda suke sun yi jawur haka zalika sun kumbura. Tana nan zaunen ta janyo wayar ta ta kunna ta sannan ta shiga contact a hankali ta lalubo number sa zuciyar ta na cigaba da harbawa da k'arfin gaske, tana so tayi fatali da duk wani abu daya ke so ya kawo mata cikas dan haka ta d'an runtse idanun ta sannan ta bud'e ta sake d'ora idanun ta kan jerarriyar special number sa, tana shirin yin blocking number tasa sega kiran sa ya shigo, seta tsaya tana sake k'arewa number kallo kamar me son karanto wani abun, tabbas ya kamata ta isar da abinda ke ran ta, ta fad'a masa babu ita babu shi koda hakan zesa ya rabu da ita kada ya sake gigin koda kiran ta ne, dab da zata tsinke ta d'aga wayar, daga 6angaren sa ya sauke wata 6oyayyiyar ajiyar zuciya sannan yace a hankali kuma a tausashe yana son kawar da duk wani 6acin ran dake d'awaeniya dashi "Ayrah!" da sauri ta runtse idanun ta tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa ta kae wajen second 30 a haka sannan ta bud'e, dan shi har ya fara tunanin ko Abban ne ya d'aga da kan sa seya ji ta tana fad'in "Kada ka sake kira na, ka manta ka ta6a sanin wata me suna na ko me kama ta ballantana ni, kayi k'ok'ari ka goge duk wani lokaci da muka ta6a kasancewa tare, ka manta da babin rayuwa ta, kada ka sake kira na a waya dan kuwa har abada bazan ta6a auran mutum irin ka ba" daga haka ta katse wayar bata jira yace komae ba ta jefar da wayar a gefen ta tana fashewa da kuka lokaci guda kuma tana tuna yadda ta kawowa Abba Rk a farko amma daga k'arshe su suka koma cikin arzik'in yayin da suka tura su su kuma suka koma cikin k'uncin rayuwa. Tsayawa yayi kamar wani sak'ago, ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70