Skip to content

Chapter 48

Chapter 48

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

uwa uba kuma ga yadda take ji a yanzun koda wane lokaci zata iya zubewa idan bata nemi wajen zama ba, dan haka babu musu ta shige cikin motar ta kwantar da kan ta tana sakin wata ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma kan ta na sake juya mata ta fara ganin ko ina na juya mata, sam be lura da yanayin da take ciki ba ya koma mazaunin driver yana sauke ajiyar zuciya, seda ya kalli inda take zaune sannan ya sake lumshe idanun sa kana ya d'auke kae yana jan motar ya fara tafiya.. .... A d'aya 6angaren kuwa a ranar da Ayrahn ta bar gidan gaba d'aya cikin su babu wanda ya rintsa, Yah Sadeeq zuciyar sa sosae take masa zafi idan ya tuna halin kafiya irin na k'anwar tasa data kasa barin d'a namiji duk da yadda Abba yace ba zata aure shi ba, ta 6angaren Umma kuwa kwana tayi tana kuka a ranar, ta kasa sakewa, koda tayi k'ok'arin tunanin ba hakan ne dalilin rashin ganin d'iyar ta ta ba se kuma ta kasa samun hujjar da zata rik'a akan hakan, koda tayi tunanin d'iyar ta ta bata da bud'ewar ido ko wayon da zata bi saurayi ta gudu se kuma ta tsaya ta tuna tasirin soyayya, musamman yadda Ayrahn ke k'aunar Raj d'in, da yadda taga rikicewar ta a jiya da Abba ke fad'a mata ba zata aure shi ba seta sake jin jikin ta yayi wani mugun sanyi, dan haka tayi kukan ta ta godewa Allah sannan tayi shiru, 6angaren Abba kuwa ranar da bugun zuciya ya kwana, wanda hakan ke alamta masa tashin ciwon sa, haka dae ya dinga daurewa baya so 6acin rae ya sanya yayi wa d'iyar tasa fata mara kyau. ... Washe_gari da safe Umma ta fito ta shiga kitchen dan ta samu ta sarrafa musu wani abun da zasu ci a matsayin abun karin, ta dad'e a kitchen d'in tana nazari se kuma ta fito kae tsaye ta wuce d'akin Abba, tana shirin shiga Abban ya fito seta dakata lokacin da shima ya dakata yana kallan yadda idanun ta suka yi ja da alama jiya kwana tayi tana kuka "Har yanzu kukan kike yi?" Abba ya tambaya yana cigaba da kallan ta, hannu Umma ta kae fuskar ta ta d'auke hawayen daya zuba, tun jiya take k'ok'arin cire damuwar daga cikin ran ta amma ta kasa, ta kasa mantawa, ko dae_dae da minti d'aya zuciyar ta ta kasa sukuni da wannan al'amari "Aou cigaba kuma zaki yi?" seta girgiza kae sannan tace bayan ta runtse idanun ta ta bud'e "Abban su bansan ina yin kukan ba, ko da nayi k'ok'arin mantawa hakan yana gagara ne a cikin zuciya ta, Abban su har yanzu na kasa amincewa ba mafarki nake yi ba" jinjina kae Abba ya shiga yi cike da gamsuwa da maganar Umman, shi kan sa jiya be rintsa ba ya zauna ne kawae se sak'e sak'e yake yi "Kiyi hak'uri ki dena kukan haka nan kin ji?" ya fad'a yana kallan ta "In Sha Allah, zan yi k'ok'ari naga hakan ta kasance.." Umma ta fad'a tana sake goge idanun ta. ... Driving yake a nutse kamar koda yaushe, jefi jefi yana juyawa yana duban inda take a takure cikin hijab ko k'wak'wk'waran motsi ba tayi, bece mata komae ba dan baya so ya tado da rigima tun yanzun dan haka ya mata shiru a ran sa yana tunanin mafita. Tafiya me tsayi suka yi kafin suka fara shiga garin Kano, zuwa lokacin kam mamaki take bashi ganin har lokacin bata motsa ba, a hankali ya fesar da iska daga bakin sa sannan yaja motar ya gangara gefen titi ya kashe ta ya d'an jinginar da kan sa akan steering na tsawon sakanni kana ya d'ago kan nasa ya dubi inda take, seda ya lumshe idanun sa kafin a hankali yace "Ayrah!!" beji ta amsa masa ba ko kuma ta d'ago har bayan wajen minti 1 sannan a hankali ya kae hannun sa kan hijab d'in nata ya d'an yi tapping nata, nan ma dae ba tayi motsi ba, seya ware manyan idanun sa akan ta sannan ya kae hannun sa a nutse gaba d'aya ya rik'o ta, se kuwa tayo baya zuwa jikin sa, k'irjin sa ya wani irin buga lokaci guda yana mamakin yadda yaji jikin ta yayi wani irin zafi daya wuce na k'a'ida, idanun sa akan kyakykyawar fuskar ta da tayi fayau kamar wadda tayi wata da watanni tana rashin lafiya, idanun ta a rufe suke, dogayen zara zaran eye lashes d'in ta sun kwanta sunyi luff akan idanun ta, a hankali ya sake bud'e bakin sa se dae yanzu a cunkushe ya furta "Ayrah!!" nan ma dae ba tace komae ba, runtse idanun sa yayi yana jin wani abu me kama da tsoro na shigar sa "Meya same ta?" ya tambayi kan sa, seya kae kunnen sa saetin dogon hancin ta da yayi ja kamar me mura, cikin lokaci k'ank'ani hucin numfashin da take fitarwa me zafi da kuma hucin zafin dake jikin ta ya sauka akan fuskar sa, seya sake lumshe idanun sa yana d'an tsayar da numfashin sa har lokacin cike da tsoro, cikin ikon Allah yaji numfashi kad'an na fita, be san sanda ya saki wata ajiyar zuciya ba sannan ya maeda ta kan kujerar ya kwantar kana ya tashi motar da gudun gaske ya wuce asibiti, sam gaba d'aya ma ya manta, haka zalika beyi tunanin komae ba ya wuce asibitin sa. Parking d'in motar sa yayi har lokacin bugun zuciyar sa be koma dae_dae ba, ya fito daga cikin motar cike da sassarfa wanda komae abin ka baka isa ka gane a yanayin da yake ciki ba, dan kuwa fuskar nan haka take babu yabo babu fallasa amma cikin zuciyar sa shi kad'ae yasan abinda yake ji, bud'e inda take kwance yayi beyi wata wata ba ya d'auke ta gaba d'ayan ta a hannun sa, sam be lura da kallan da en cikin asibitin ke bin sa dashi ba, yama manta abinda ya aekata haka ya wuce da ita cikin Office d'in sa, duk wad'anda ke kallan sa mamaki ne ya kamasu yadda suka ga Doctor Rk d'in da kan sa ya d'akko wata mace a hannun sa, nan take aka fara gulmammaki cikin asibitin, seda ya tsaya ya kar6i spare key d'in Office d'in sa dake ajje sannan ya wuce ya bud'e ya shiga har lokacin tana rik'e a hannun sa ya kwantar da ita kan gado. .. Hannun ta har rawa yake yi ta d'auki wayar ta ta nemo number Abbu ta kira, babu jimawa Abbu ya amsa wayar "Yalla6ae Doctor Rk ya shigo yanzun nan" daga inda Abbu yake ya saki ajiyar zuciya yana jin dad'i har cikin ran sa dan kuwa tun d'azun yake kiran layin Rk d'in amma se ace masa a kashe yake "Ohk ina nan zuwa nan da 10 minutes" shine kawae abinda Abbu ya fad'a yana katse wayar sannan ya chanja akalar tafiyar tasa zuwa asibitin. .. Kamar wanda aka jefo haka Abbu ya fad'o cikin asibitin, dae_dae lokacin da Rk ya fito daga cikin Office d'in sa, Abbu ya sake sauke ajiyar zuciya ganin d'an nasa, seya k'arasa kafin yace

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70