Chapter 14
Chapter 14
Mato a wayar sa, ya kalli wayar na tsawon sakanni sannan ya d'aga ya kara ta a kunnen sa, daga can 6angaren Alhaji Mato yace "Haji Ibraheem na jika shiru kwana 2 yasa nace bari na ta6o ka" d'an numfashi kad'an Abba ya sauke sannan yace "Wallahi kuwa, nima ina ta k'ok'arin kiran ka se kuma na sha'afa, dama zuwa anjima nake so nazo wajen naka, ina so ka sake min kwantance" "Toh toh Madallah.." Alhaji Maton ya fad'a yana d'orawa da yiwa Abban kwatance, Umma ta kalle shi sanda ya gama wayar tace a nutse "Yanzu ya za'ayi da shi kenan?" seda Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Zan fad'a masa gaskiya ne, idan ya yadda da k'addara shikenan idan kuma be amince ba yace sena biya shi kud'in sa se nasan yadda za'ayi.." "Toh Allah Ubangiji yasa ma shima ya kar6i wannan k'addarar" "Ameen" Abba ya fad'a ba dan yana da tabbacin hakan ba, dan shi sheda ne akan son kud'i irin na Alhaji Maton. .. Shiru Alhaji Maton yayi har Abba ya gama masa bayanin abinda ya faru, se yayi murmushi yana girgiza kae kana ya d'aga kae ya kalli Abba yace "Haji Khaleel ni fa gani nake ko menene ya faru kae ka jawa kanka, ba sau d'aya ba ba sau biyu ba na fad'a maka na kuma baka shawara ka rabu da matar ka, farar k'afa gare ta, an kore ka daga banki, kazo ka fara teaching an dakatar da kae ka fara kasuwanci wani ya gudu da kud'in wannan kad'ae be ishe ka ka gane.." "Malam ya ishe ni haka!" Abba ya fad'a yana d'aga masa hannu idanun sa akan sa cike da zallahr 6acin rae "Aou aou toh hakane abin, wato har yanzu kae ka kasa gane Annabi ya faku koh?, toh cigaba da zama da ita, ina ga ba zaka fahimci abinda nake fad'a maka ba se ranar da kayan sakawa ma ya gagare ka sakawa.." Abba ya runtse idanun sa zafin zuciyar da yanzun ya zame masa jiki se k'aruwa yake yi, a nutse ya mik'e tsaye sannan cikin kaurin murya ya furta "Kana buk'atar kud'in ka ne ko kuwa?" "A'ah se kuma in k'i buk'ata, ina jiran kud'i na a cikin satin nan kawae" Alhaji Mato ya fad'a shima yana mik'ewa ya bar wajen, da kallo Abba ya bishi yana mamakin wannan banzan hali irin na Alhaji Maton, shikenan kuma a matsayin ka na bawa musulmi Allah baze jarabce ka ba? Da wannan tunanin ya koma gida yana sak'a da warwarar yadda ze biya Alhaji Maton kud'in sa. Sanda ya koma gidan bayan yaci abinci Umma ta tambaye shi yadda suka yi da Alhaji Maton, duk se yaji tausayin ta ya kama shi yadda wani ke ik'rarin duk dalilin tane abubuwa ke faruwa dashi, abinda shi kuma baze ta6a yadda ba kenan, dan kuwa shi musulmi ne daya yadda da k'addara me kyau da kuma mara kyau, gyara zama yayi yana kallan ta "Kada ki damu, zan san yadda zanyi in biya shi kud'in sa.." cike da mamaki Umma tace "Aou yace se an biya shi?" "K'warae kuwa" Abba ya fad'a "Ikon Allah.." Umma ta fad'a tana girgiza kae... Abba beyi k'asa a gwuiwa ba wajen d'akko motar sa ya siyar da ita ba, saboda matsalolin da take dasu yasa ba tayi wani daraja ba gata kuma dama ba babbar mota bace, seya d'auki kud'in Alhaji Mato ya bashi sannan ya rik'e ragowar a hannun sa dan amfanin yau da gobe, abinda ya tsaya masa a rae yanzun kawae shine yadda zeyi ya samu sana'a ko dan ya sanya 'ya'yan nasa a makaranta, abinda ya k'ara masa k'aemi ma akan saka su a makarantar shine.. Rannan suna zaune a cikin parlourn dukan su suna kallan Al jazeera inda Abba ke kallan labarae, Ayrah na zaune gefen Abban itama tana kallan T.Vn kamar me fuskantar abinda ake nunawa a ciki, daga k'arshe a cikin labaran aka nuno wasu d'alibae da Uniform d'in su, se kuwa tayi zumbur ta tashi zaune tana kallan Abba tace "Abba mun dena zuwa makaranta?" kallan ta Abba yayi cikin mamakin jin furucin ta, se yayi murmushi sannan yace yana shafa doguwar sumar kanta dake a bud'e "A'ah za'a sanya ku mana" "Abba yaushe?" ta sake tambayar sa, seya d'an yi shiru kana yace "Nan bada dad'ewa ba Uhmm?" "Hadda Raj koh?" ta fad'a tana murmurshi, zancen kenan dan kullum idan ba tayi maganar Raj ba toh ba Ayrahn bace "Ehh" Abba ya fad'a yana maeda duban sa kan T.V. .... Sosae Umma ta takurawa Abba akan zuwa asibiti saboda rashin baccin da yake samu, shima kansa rashin baccin na damun sa dan haka a wannan karon da tazo masa da k'orafi be musa mata ba ya shirya ya tafi asibitin, gwajin hawan jini aka fara masa, kuma tashin farko su kaga yanda jinin sa ya hau, sosae suka bashi shawarwari akan hakan da kuma magunguna, hakan ba k'aramin kuma tayar masa da hankali yayi ba, amma gudun kada hankalin Umma ya tashi yasa be sanar da ita ba, kawae yace mata an gwada shi amma basu fad'a masa aenahin abinda ke damun sa ba se result d'in ya fito, haka ta yadda da abinda ya fad'a mata d'in, yayin da shi kuma ya cigaba da shan magungunan sa ba tare daya bari Umman ta sani ba. A lokacin ne ya cigaba da fama da rashin bacci da kuma tunanin daya zame masa jiki, se kuma bugun zuciya da shima baya rabo dashi, haka wataran ze kwana a zaune, se dae da yake baya bari lokacin ya tafi masa a banza se hakan yake sakawa baya wani damuwa sosae, dan kuwa k'arin lokacin karatun Qur'an ya samu, idan dae ya fahimci bacci baze zo masa ba seya fito tsakar gidan nasu ya shimfid'a dadduma yayi ta karatu har zuwa asuba, ranar da kuma ya samu baccin se yayi baccin sosae, sau da dama Umma kan farka ta same shi yana karatu, dalilin kenan daya sanya bata damu da rashin baccin nasa ba, saboda ta riga data saba da ganin sa cikin dare yana tashi karatu, se dae tasan ya k'ara lokacin karatun, amma duk da haka bata kawo rashin samun bacci ne ya sanya shi k'ara lokacin karatun ba, tafi ta'allak'a hakan da yanayin rayuwa kawae.. Sanda Umman ta gano ciwon dake tattare da Abban ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, dan har kuka seda tayi, Abba ya fesar da iska daga bakin sa yana kallan ta yace "Kiyi hak'uri kiyi shiru, kada kisa nima nawa hankalin ya tashi mana" "Amma Abban su meyasa ka 6oye min?" "Toh yanzu ba gashi kin sani ba?" ya fad'a yana kallan ta, seta share hawayen fuskar ta sannan tace "Duk da kullum cikin yi maka addu'a nake, amma ko ba komae zan dage da maka addu'a akan ciwon koh?" "Toh shikenan nayi laefi amin afuwa" ya fad'a yana kallan ta da tattausan murmushi akan fuskar sa, itama murmurshin tayi duk da yadda can k'asan zuciyar ta ke cunkushe da tausayin Abban. .. Sosae Abba ya dage wajen neman sana'ar da zata rufa musu asiri, se dae har zuwa lokacin be samu ba, gaba d'aya yanzu burin sa be
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70