Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

da "Kana ganin idan naje wajen mahaefin ta a yanzu banyi gaggawa ba?" girgiza kae Muttala ya shiga yi ya d'an yi murmushi kana yace "A'ah ranka ya dad'e ka bari tukunna, kada su fahimci dalilin hidimar ka tun yanzu, zefi kyau mubi komae daki_daki.." "Gaskiya a haka ma nayi k'ok'ari wallahi, bari dae zan bar ta ta gabatar da first semester kawae zuwa lokacin zan je wajen baban nata" ya fad'a yana girgiza kae shima "Toh hakan ma babu laefi" Inji Muttala.. .... Tana sanye cikin doguwar rigar atamfa da hijab kasancewar sa favourite nata, sosae kyakykyawar fuskar ta tayi fayau kamar mara lafiya, fararen manyan idanun ta sunyi ja, hannun ta cikin na Umma tana kallan ta da idanun nata da suka sake yin rau rau, Umma tayi murmushi dan tana so ne ta kwantar mata da hankali tace "Ya isa haka shalele, kada ki 6ata fuskar nan taki yanzun nan mana Uhmm?" Umma ta fad'a tana sanya hannu ta d'auke k'wallar dake zuba akan kuncin ta "Umma ta zanyi kewar ki" ta fad'a tana kwantawa a jikin Umman, hannu Umma ta saka ta rik'o ta bayan tayi murmushi tace "Banda abin ki Ayrah ae ba dad'ewa zaki dinga yi ba, ko kin manta zaki dinga dawo mana hutu?" seta jinjina kae kawae "Toh idan kin gama kukan seki taho mu tafi" Yah Sadeeq daya shigo ya fad'a, seta d'aga kae tana kallan sa gami da murgud'a mitsitsin bakin ta "Iyeee.. Lallae ne yarinyar nan" Yah Sadeeq ya fad'a yana rik'e ha6a. Har k'ofar gida Umma ta rako su inda motar da zata kaesu Zarian take, seda taga tashin motar tasu sannan ta koma cikin gidan tana matse k'walla, dan kuwa tun tasowar Ayrahn baza tace ga ranar da suka ta6a rabuwa ba, dan tun tana yarinyar ta mayyar Umman ce, ko yadda da mutane ba wani sosae take ba ballantana ace taje ta kwana. ... "Ki maeda hankali kiyi karatu, sati d'ayan nan da aka wuce ki ki samu wata ta koya miki, banda yin k'awar da zaki zauna kina fad'a mata cikin ki duk da dae nasan halin ki amma dae gwara na tisa miki" Yah Sadeeq ya fad'a sanda suke tsaye a wani ke6antaccen waje, seta jinjina kae kawae dan bata tunanin zata iya magana, idan kuwa tace zatayi maganar toh tabbas kuka zata saka, Abba daya fahimci haka se yayi murmushi dan shi kansa har ya fara kewar Autar tasa, ya matsa kusa da ita yace "Ayi karatu sosae koh?" nan ma dae seta jinjina kan tana kae hannun ta idanun ta ta goge hawayen daya sauko akan fuskar ta, hannu Yah Sadeeq ya sanya cikin aljihun sa ya zaro wata k'aramar waya yace yana kallan k'anwar tasa "Yau dae ga alk'awarin mu.." seta kalli hannun nasa sannan ta kalle shi, bata san sanda murmushi ya su6uce a kyakykyawar fuskar ta ba, ta saka hannu ta kar6a cike da farin ciki kana ta d'an jujjuya ta sannan tace lokacin da wasu kyawawan hawaye suka samu damar zubowa akan kuncin ta "Amma nagode sosae Yah Sadeeq, Allah ya k'ara arzik'i" "Ameen" dukan su suka amsa da hakan cikin jin dad'in yadda ta d'an saki jiki.. seda suka d'an dad'e suna sallamar zuwa lokacin ta saki jiki suna ta d'an hira, se kuma daga baya tayi kukan ta ta godewa Allah, sannan su Abban suka tafi bayan sun kwantar mata da hankali... ... A hankali ta tura k'ofar d'akin hannun ta jaye da er trolley d'in ta da aka kar6o mata a wajen k'anwar Umma da itama zama ya dawo dasu cikin kano, dukkan su suka d'aga kae suka kalle ta sanda tayi sallama da kyakykyawar siririyar muryar ta data sake sirancewa saboda kukan da tayi, su 3 ne zaune a cikin d'akin, d'aya na daga gefe tana danna waya yayin da biyun ke zaune kusa da juna suna hira "Wa'alaeki Assalam" suka amsa dukan su suna bin bak'uwar fuskar da suka gani da kallo "Wow, tubarkallah Masha Allah" d'aya daga cikin su ta fad'a a ranta lokaci d'aya kuma tana mik'ewa tsaye ta k'arasa inda Ayrah take tace tana d'an yin murmushi "Anan d'akin kike?" tayi maganar tana kallan idanun ta da suka yi ja alamar kuka tayi, seta k'ak'alo murmushi ta wanzar akan fuskar ta wanda kana gani kasan beje ko'ina ba tana jinjina kae "U're highly welcome.." ta fad'a tana d'aukar bagcon data gani a gefen Ayrah tayi gaba, babu musu Ayrahn tabi bayan ta a hankali "Ruks ki tashi me waje tazo fa" wadda ta kar6i jakar Ayrahn ta fad'a tana kallan wadda ke zaune kan gado tana danna waya, wadda aka kira da Ruks d'in ce ta mik'e tana kallan Ayrah itama tayi murmushi tace "Barka da zuwa bak'uwa" "Umhum" Ayrah ta fad'a kawae tana jefa mata kalar murmurshin data yiwa Jidda, seta k'arasa ta zauna akan gadon tana jin ta gaba d'aya a wani irin takure, musamman yadda taga su duk lokaci d'aya suna neman sakin jiki da ita, seda Jidda ta ajje mata kayan ta gefe guda sannan ta dawo ta zauna kusa dasu Ruks ta zauna, Bahijja da tun d'azun ba tace komae ba se kallan Ayrah da take tace "Bak'uwa ya sunan ki?" a hankali ta bud'e bakin ta daya mata nauyi tace "Ayrah.." "Awwwn, sunan en gayu, suna me dad'i.." kusan a tare suka fad'i hakan, har seda hakan ya sanya ta tayi murmushi "Toh barkan ki da zuwa" Bahijja ta fad'a... Suna nan zaune d'akin har bayan isha'i suna hirar su, hirar da kusan duk akan abu d'aya suke yin ta, ita dae tana zaune a gefe guda se dae ta bisu da ido kawae, so take ta ke6e ita kad'ae tayi kukan ta ko zata ji sauk'in kewar gida data fara damun ta tun yanzun. "Ruks ki tashi ki d'ora mana ko Indomie ce pls, kinga bak'uwa ma ba taci komae ba" Jidda ta fad'a, Ruks ta kalli Ayrah tace "Ayrah kina jin yunwa ne?" seta girgiza kae kawae tana yabawa da kulawar mutanen da bata ta6a ganin su ba se yau "A'ah a k'oshe nake" ta fad'a tana kallan Ruks d'in "Toh dae kin ji, mu duk bama jin yunwa muma, a bar shi kawae pls" "Shikenan ae" Jidda ta fad'a "Kuuu, kun san k'arfe nawa kuwa?" Bahijja ta fad'a tana d'an waro eyes d'in ta "Wani abun ya faru?" Ruks da Jidda suka tambaya lokaci d'aya "Ni kam seda safen ku wallahi, kwanciya zanyi ko dan na tashi da wuri, gobe fa Doctor RK ne a farko, ko kun manta abinda yayi last Monday?" ta k'arasa maganar tana hayewa kan gadon ta "Nima kam seda safen ku" Ruks ta fad'a tana mik'ewa, harara Jidda ta jefa mata sannan tace "Toh ni me zan zauna jira hajiya? Ayrah seda safe" tayi maganar itama tana hayewa gadon ta.. Bin su tayi da kallo su duka lokacin da d'akin yayi shiru, se taji tsoro ya fara shigar ta, dan haka taja jikin ta ta maeda shi kan gadon ta kwanta, ta lullu6e kafatanin jikin ta da hijab d'in ta wani sanyi na ratsa ta, a hankali ta lumshe idanun ta wasu hawaye masu d'umi na sakkowa akan fuskar ta, wayar data tuna da ita ta

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70