Chapter 15
Chapter 15
wuce na yadda ze samu ya sanya Yah Sadeeq da Ayrah a makaranta ba dan haka idan ya tashi tun safe ya fita baya dawowa se dare amma har zuwa lokacin be samu ba. .. "Abba wae ana sallama da kae" Yah Sadeeq ya fad'a yana Kallan Abba dake zaune "Inji wa?" Abban ya fad'a yana kallan sa, girgiza kae Yah Sadeeq yayi sannan yace "Abba bansan shi ba.." "Toh Ikon Allah" Abba ya fad'a yana mik'ewa, ya kalli Umma da itama kallan sa take yace "Bari naje.." "A dawo lafiya" ta fad'a sanda yake barin tsakar gidan zuwa waje.. Murmushi yayi sanda yaga mak'ocin sane wanda suke yawan had'uwa a masallaci, seya mik'a masa hannu suka gaesa sannan mutumin yace "Wato dama magana ce akan wani aeki, yasa nace bari na maka magana idan zaka iya toh seka fara ko ranar litinin ne.." sosae annurin fuskar Abba ya k'aru yace "Ina jin ka wane irin aeki ne?" "Aekin Company ne haka amma ba wani aekin wahala bane sosae, idan ka amince zaka iya se muje ka gani" sosae Abba yaji dad'in wannan abu dan haka cikin farin ciki yace "Toh nagode nagode sosae, Allah ya saka da alkhaeri.." "Ameen Ameen" mutumin ya fad'a. Abba na komawa gida ya sanar da Umma abin alkhaerin daya same su, sosae Umman ma taji dad'i dan haka babu 6ata lokaci Abba ya gabatar da isthikara, kafin ya fara zuwa aekin kuwa sosae yaji ya kwanta masa, har ya k'agu ma ya fara aekin.. Ranar litinin kuwa Abba ya fara aekin, kuma a ranar aka fad'a masa albashin sa, duk da kud'in basu taka kara sun karya ba amma shi a wajen sa da iyalin sa sosae suka ji dad'i, suka kuma godewa Allah.. Babu 6ata lokaci k'arshen wata nayi Abba ya sanya su Ayrah a makarantar gwamnati d'an nesa da gidan su, yayi amfani da kud'in ya siya musu duk wasu kaya na buk'ata da yasan zasu buk'ace su, farin ciki a wajen Ayrah kamar zata yi mene, dan sosae tayi missing School, yadda suka samu background me kyau ya sanya yanzun abin bezo musu da wahala ba, duk da yanayi na chanji da yake tsakanin government school da private school, dan haka suka cigaba da karatun su.. Kud'in Abban gaba d'aya yake k'arewa a wajen hidimar makaranta, kud'in mota da kuma kud'in cefane dan haka akwae wani mutum da yake siyar da kayan abinci a wajen sa yake kar6ar bashin abinci duk k'arshen wata, wani watan kuma seya bashi kud'in sa ya sake kar6ar wasu, haka rayuwar tasu ta cigaba da kasancewa. Tun daga wancan lokacin Abba be sake bi takan Alhaji Mato ba dan ya riga yasan babu abinda ze saka ya sake bashi wani abun ko kuma jari, dan haka kwata kwata ma bebi ta kansa ba, ya fita harkar sa kamar yadda shima ya fita tasa. A 6angaren Ayrah kuwa zuwa lokacin tun tana zancen Raj har ta gaji ta dena yi, dan tun iyayen na biye mata har suka zo suka dena kula ta idan tayi zancen nasa, basu san me zasu ce mata akan Raj d'in ba dan kuwa a lokacin shekarun ta sunyi kad'an ta fahimci irin abinda Abbun yayi wa Abba. .. Kwanaki nata tafiya, haka watanni ma suna ta shud'ewa suka had'u suka bada shekaru, izuwa lokacin sosae hidimomi suka taru suka k'ara yiwa Abba yawa, ga kuma kullum yadda tsadar abubuwa ke k'aruwa amma kuma albashin sa kamar na da ne, ba'a k'ara musu ba ballantana su samu sauk'in yadda abubuwa ke ta tashi, k'arshen wata ne a lokacin sanda aka musu albashi, dama kuma kafin zuwan albashin ya riga ya kashe su da bashi, kae tsaye seda ya fara zuwa kasuwa ya siyowa su Ayrah sabbin Uniform, a yadda yaso ma har da jaka da takalma ze siya musu saboda yadda nasun suka tsufa amma kuma yasan idan yayi hakan zasu takura ne matuk'a, dan haka kawae daga Uniform d'in ya baro kasuwar, daga nan ya wuce ya biya wad'anda ke binsa bashi wanda bashi da yawa, ya zama na saura kud'in daya san na cefane ne kawae dana kud'in motar su Ayrahn. Wajen da yaje na k'arshe shine wajen wanda yake kar6ar kayan abinci a wajen sa, ya k'arasa da sallama yana neman waje ya zauna, amsa masa sallamar mutumin yayi sannan Abba ya d'an yi shiru yana tunanin ta inda ze fara, seya sanya hannu cikin aljihu ya d'akko kud'in daya ware wanda ze bashi, ya mik'a masa yace "Gashi.." kar6a mutumin yayi yana karkad'e hannun sa da fulawa ta 6ata, ya k'irga sannan ya kalli Abba "Wani abun za'a baka da kud'in ne?" girgiza kae Abba yayi cikin sarewa da yadda yaga mutumin kamar wanda ze bashi kayan kyauta yace "A'ah kayi hak'uri don Allah, kasan lamarin ne se a hankali, ka rik'e wannan, a bani kayan kamar yadda aka saba bani idan yaso se a d'ora akan wad'ancan" tun kafin ya kae k'arshen maganar mutumin ya fara girgiza kae, yana gamawa yace "A'ah wallahi bazan iya ba, kae ma kayi hak'uri, duk lokacin daka gama biyan bashin se kazo mu san yadda za'ayi, shine kawae alfarmar da zan iya maka" Abba ya runtse idanun sa yana jin gaba d'aya jikin sa babu dad'i, dama daga yadda yaga yanayin mutumin yasan ba lallae ya yadda da abinda yazo masa dashi d'in ba, dan haka ya mik'e yace a hankali "Toh nagode, zan kawo maka cikon kud'in In Allah ya yadda.." Abba ya fad'a yana yin gaba, mutumin ya bishi da kallo yace bayan yaja tsaki "Ayi mutum kullum cikin neman alfarma yake, na tsani irin haka wallahi" ya fad'a yana d'aura wani mae a cikin leda.. ... Da sallama Abba ya shiga gidan, Ayrah ta k'arasa ta rungume Abban tana fad'in "Abba sannu da zuwa" "Yawwah sannu Auta" ya fad'a yana sakar mata ledar hannun sa daya shigo da ita, tana shirin juyawa yace "Ina d'an kwalin kuma?" "Abba tsifa Umma ke min, yanzun na cire shi" ta fad'a tana d'an murmushi gami da shafa kanta "Toh ayi maza a gama tsifar a rufe kan" Abba ya fad'a sanda yake kallan Umma dake masa sannu da zuwa, Ayrah ta k'araso ta ajje ledar hannun ta, sannan ta tafi da d'ayar kitchen dan ko Abban be fad'a ba tasan tsarabar tace, er madaedaeciyar roba ta d'akko ta zuba mangoron nata a ciki sannan taje ta wanke shi kana ta dawo cikin parlourn dae_dae lokacin da Abba ke fad'in "Lafiya kuwa Sadeeq ke bacci da yamman nan?" "Wallahi kuwa Abban su kamar zazza6i ne a jikin sa d'azun" "Toh Subhanallahi Allah ya sawwak'e... Ga rama can ki kwad'a mana ita muci yanzun, kafin dare kuma mu san yadda za'ayi.." babu musu Umma ta mik'e ta fita daga d'akin zuwa kitchen ta gyara ramar tass ta kwad'a ta sannan ta kawowa Abba tasa kana ta zubo musu ita da Ayrah har ma da Yah Sadeeq, kallan Ayrah dake ta shan mangoron ta hankali kwance tayi ta girgiza kae tana murmushi tace "Tashi Sadeeq ya tashi haka nan yaci abinci.." da "toh" ta amsa sannan ta mik'e ta fita bayan ta wanke hannun ta ta dawo cikin d'akin, hannun ta ta saka a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70