Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

yadda yake d'auke da towel ne ya sanya ni ganin yadda k'ak'k'arfan jikin sa yake, dogo ne me k'ak'k'arfan jiki, fari ne sosae wanda hakan ya sanya bak'ar sumar dake kan k'irjin sa ta bayyana kan ta sosae kan farar fatar sa wadda ke kwance luff luff kamar wadda ake kwantar da ita da Comb, yana da dogon hanci me tsayi, fuskar sa d'auke da bak'in sajen daya zagaye bakin sa, ringing d'in da yaji wayar sa nayi ne ya sanya shi sakin wani k'ayataccen murmushi ya ajje comb d'in kan stool d'in sannan ya mik'e ya k'arasa inda wayar ke ajje ya d'auka kana ya zauna ya jinjina da pillown dake kan tank'amemen gadon sa kana ya kara wayar a kunne bayan ya d'aga, da kukan ta ya fara cin karo cikin wayar, seya mik'e zaune yana bud'e manyan idanun sa yace "Subhanallahi..Ayrah meya saki kuka?" ya fad'a cikin kulawa, cigaba da kukan tayi kamar ranta ze fita, daga inda yake zaune kuwa yana jin kamar ana watsa masa dalma ne, mik'ewa tsaye yayi ya murza goshin sa da d'ayan hannun sa yana lumshe idanun sa har lokacin bata bar kukan ba, ya kuma yin k'asa da muryar sa yace "Ya isa haka don Allah, ya isa haka, pls kiyi shiru ki fad'a min why are u crying.." ya sake fad'a cikin rarrashi "Raj.." ta fad'a cikin kukan, ya lumshe idanu yana jin muryar ta ta har cikin gangar jikin sa "Na'am.. Ayrah, pls menene Uhmm?" daga inda take zaune ta d'an lumshe idanu tana sassauta kukan ta koma sheshshek'a se can ta fara magana tana yi tana d'an aje ajiyar zuciya "Abba ne.." "Me Abban yayi?" ya fad'a yana jin yadda ya k'agu yaji abinda ya sanya ta kuka haka "Abba yace bazan aure ka ba.. Raj meka yiwa Abba?" cikin rashin fahimta ya sake bud'e manyan idanun sa kana yace "Ni kuma?" kamar tana gaban sa ta jinjina kae, kafin yace komae kuma ta sake cewa "Na yarda da kae Raj, kawae ka fad'awa Abbun ku yazo wajen Abba, ina tunanin be gane Raj d'in da nake nufi ba.." neman waje yayi ya zauna kafin yace "Ohk..In Sha Allah, yanzu dae ki dena kukan kinji? In Sha Allah ni naki ne kema kuma tawa ce kinji?" jinjina kae tayi ba tare da tace komae ba, se kuma can tace "Ehh.." "Oh yah Smile.." ya fad'a daga inda yake yana d'an murmushi, goge fuskar ta tayi sannan ta d'an yi murmushin me d'an sauti wanda tasan hakan ze faran ta masa "Awwnnn That's my girl..yanzu dae ki aje waya kiyi bacci zan je na samu Abbu da wannan maganar.. I luv u.." ya k'arasa fad'a idanun sa a lumshe, itama nata idanun ta lumshe kamin tace "Tohm.." Tashi yayi ya k'arasa shiryawa cikin wata bluen shadda dan babu k'arya yayi missing manyan kaya, ba tare da ya d'ora hula akan sumar kansa ba ya d'auki wayar sa har lokacin be dena mamakin dalilin da yasa Abban nata yace haka ba. Kae tsaye parlourn k'asa ya sauko cikin nutsuwar data zame masa jiki, dae_dae lokacin da wata farar mata wadda ak'alla zatayi shekaru 45 zuwa 50, kyakykyawa ce kamar yadda d'an nata yake, tana sanye cikin wata atamfa me kyau d'inkin riga da skirt, jera warmers d'in data fito dasu daga kitchen akan dinning take, ta kalle shi da murmushi kan fuskar ta sannan tace "Ka k'araso ka fara cin abinci koh?, semu zauna mu samu muyi hira.." d'an murmushi ya saki kad'an kamin ya shafa sumar kansa yace "Tohm Ummee.. Amma inaso ne muyi wata magana me muhimmaci.." ya fad'a yana d'an lumshe manyan idanun sa kad'an, dae_dae lokacin Ummee ta gama jera kayan data fito dasu seta k'araso inda yake tsaye tace tana murmushi "Shikenan Raj, ni dama daga yadda na ganka nasan akwae magana a bakin ka" shima murmushin ya maeda mata sannan dukkan su suka wuce zuwa cikin k'aton parlourn daya k'awatu da had'ad'd'un kujeru, suna zama Alhaji Kabeer ya shigo cikin d'akin da sallama sanye cikin manyan kaya da babbar riga, dukan su suka amsa masa ya k'araso yana kallan su su duka kuma a lokaci guda yana amsa sannu da zuwan da suke masa, akan kujera ya zauna, yayin da Raj ya sauko daga kan kujerar yana shirin zama a k'asa Alhaji Kabeer yace "A'ah kayi komawar ka ka zauna, yau ae hira zamuyi.." murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa seya koma ya zauna yana kallan Alhaji Kabeer yace "Barka da dawowa Abbu.." "Barka kadae Raj" "Ko dae a kawo maka abincin nan ne?" Ummee ta fad'a tana kallan Abbun, girgiza kae yayi kafin yace "A'ah fara kawo min dae juice na sha.." mik'ewa Ummee tayi ta wuce inda ze sadata da dinning area, yayin da Abbu ya dawo da duban sa kan Raj yace "Ya hanyar dae? Kuma ya karatun?" "Alhamdulillah Abbu..ina tafe da wani albishir fa.." ya fad'a da murmushi kan fuskar sa, dae_dae lokacin da Ummee ta k'araso hannun ta d'auke da juice d'in ta ajjiye sannan ta fara k'ok'arin zubawa a cikin tambulan "Toh ko zamu bari mu fara cin abinci?" Abbu ya fad'a yana kar6ar juice d'in da Ummee ta mik'a masa kana ta nemi waje ta zauna, hannun sa ya kae kan sumar kansa ya d'an shafa sannan yace "A'ah Abbu.. Na k'agu na sanar daku ne.." Ummee ta kalli Abbu tana murmushi tace "Ae kawae ka k'yale shi ya fad'a dan tun d'azu ya kasa komae har abincin ma shima beci ba.." "Ohk ina jin ka.." Abbu ya fad'a yana kae juice d'in bakin sa "Abbu na samu matar aure.." dukkan su suka kalle shi cike da mamaki da kuma farin ciki duka a lokaci guda, mutumin da suka san kwata kwata baya kula wasu mata amma yau shine ke fad'in ya samu matar aure? Toh ta yaya? "Wacece wannan Raj?" Ummee tayi k'arfin halin fad'in haka, wani k'ayataccen murmushi ne ya su6uce masa sannan yace bayan ya lumshe idanun sa ya bud'e "Ayrah.." "Wacece Ayrah?" Ummee ta fad'a tana kafe shi da idanun ta "Ayrah dae wadda kika sani Ummee, kada kice min har kin manta ta, Ayrah dae tawa wadda kika sani.." k'warewar da Abba yayi ne ya sanya su duka suka kalle shi, babu k'ak'k'autawa ya shiga yin tari sosae, da sauri Raj ya mik'e ya isa fridge ya d'akko ruwa ya kawowa Abbun, da k'yar ya iya kar6a yasha ruwan, ya shiga sauke ajiyar zuciya kamar wanda yayi gudu "Sannu Abbu..sannu.." shine abinda Ummee keta maemaetawa amma Abbun bebi ta kanta ba ya kalli Raj yace "Ya..akayi ka had'u da ita?" yayi maganar a rarrabe yana kallan Raj, sosae Raj ke binsa da kallo yana so ya gano abinda ya sanya shi lokaci d'aya ya zama wani iri "Abbu.." "Ya akayi ka had'u da ita? Ko dama kuna tare tsawon lokacin nan?" Abbu ya katse masa maganar da yayi niyyar yi, girgiza kae Raj yayi har lokacin idanun sa nakan Abbu "Tun wuri ka rabu da ita Raj, ka rabu da ita dan auren ku baze ta6a yiwuwa ba, tun wuri ma ka cire ta a ranka zefi maka.." Abbu ya fad'a yana mik'ewa yayi hanyar d'akin sa, da kallo

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70