Skip to content

Chapter 51

Chapter 51

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

ta da juyawa tana k'arewa titin kallo, in dae har ba tayi mistake ba nan titin Kano ne, bata san sanda ta saki wani murmushi me sauti ba tana ji kamar ta tashi ta taka rawa, duk da yadda yaji tayi murmushin hakan be sanya shi kallan ta ba sema sake tsuke face da yayi, haka ya cigaba da tafiya tana cigaba da bin titin da kallo, ita dae ba taga yayi hanyar unguwar su ba, tun tana k'ok'arin yin shiru taga iya gudun ruwan sa har taji zuciyar ta na son karaya ta kalle shi yadda yake driving a nutse sannan ta d'auke kae tana 6ata fuska itama "Bafa nan ne unguwar mu ba mu" tayi maganar murya a cunkushe, yadda tayi maganar ne ya sanya shi yin murmushin dabe shirya ba, gudun kada ta gan shi ya sanya shi saurin sake had'e fuska, kamar ba zece komae ba se kuma can bayan ya gama jan ajin sa yace "A haka zaki koma musu gidan kamar korarriya? So kike hankalin su ya sake tashi fiye da da? Zamu je kiyi wanka ne ki chanja kaya sannan na maeda ki gidan" yayi maganar cikin tsare gida shima tasa muryar a cunkushe "Toh ina ruwan ka?" ta fad'a bayan ta jefa masa harara, daga inda take tana ji kamar ta tashi ta rufe shi da duka, yace taemakon ta zeyi, ya taemake tan to kuma ina ruwan sa da yadda zata koma gida? Meye nasa a ciki? D'aga kafad'a yayi yana ta6e baki sannan yace "Babu ruwa na, amma ni dae bazan kae ki gida a haka ba" kallan jikin ta ta shiga yi, dan ita dae bata ga abinda tayi ba da yake nema ya fad'a mata magana ba dan haka ta sake kufula tace "Toh ka ajje ni in tafi da kae na mana, bana buk'atar taemakon ka a karo na biyu" ta fad'a tana jin yanda zuciyar ta ke mata zafi, be kula ta ba haka kuma be kalle ta ba hakan ya sake fusata ta, se kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya tana runtse idanu, yasan yanzu zata soma kukan nan nata da bata gajiya dashi dan haka yana karya kwanar wani layi yace a nutse "Shikenan muje na rubuta takaddar ki tafi" jin abinda ya fad'a d'in ne ya sanya ta kalli inda suka shigo sannan taja doguwar ajiyar zuciya tana hana kukan daya taho mata fitowa, a k'ofar wani gida ya tsaya da motar tasa sannan ya dakata ya d'auki wayar sa ya danno number Yaseer ya kira, bata dad'e tana ringing ba Yaseer ya d'aga "Kana gida ne?" Rk ya fad'a "Ehh.. Na dawo" Yaseer ya fad'a daga inda yake zaune kusa da matar sa Hameeda "Toh gani k'ofar gidan ka" dariya Yaseer yayi gami da fad'in "Haba mana Mr man, ae ba seka zolaye ni ba, nasan ba ta6a zuwa zaka yi ba" d'an murmushi kad'an Rk yayi sannan yace "Toh ka fito ka tabbatar mana, hope dae Madam na nan?" da mamaki Yaseer ya kalli Hameeda sannan yace "Yeah, amma dae fari dae bari na fito dan tabbatarwa" ya fad'a yana mik'ewa sannan ya kalli Hameeda yace "Yanzu Rk ze shigo, yace min yana waje" "Ikon Allah! Amma kuma babu sanarwa irin wannan babban bak'o haka?" "Ke dae bari naje na fara tabbatar da zuwan nasa" Yaseer ya fad'a yana ficewa daga d'akin. Kallan sa ta cigaba dayi da manyan idanun ta da suka yi rau rau sanda yake wayar, har zuwa sanda taga yana shirin ajje wayar, yana sane da kallan da take masa dan haka ya sake rik'e wayar sannan yace "Ka taho min da takadda da biro" se a lokacin ta d'auke kan ta daga kallan sa tana sauke ajiyar zuciya, "gaba d'aya yau lokaci baya sauri" ta ayyana a ran ta. Suna nan zaune babu wanda ke cewa da d'an uwan sa uffan, se ga Yaseer ya bud'e gate d'in gidan ya fito, da murmushi ya k'araso bakin motar Rk d'in yana fad'in "Ohh Rk ashe da gaske kake? Ban ta6a tunani ba wallahi" ya fad'a dae_dae sanda idanun sa suka sauka akan Ayrah dake zaune tana jira a mik'o mata takaddar ta ta wuce gidan su (lol), murmushi Rk yayi kana ya bud'e murfin motar ya fita ya kama hannun Yaseer suka gaesa "Wacece wannan?" Yaseer ya fad'a yana kallan cikin motar sannan ya dawo da duban sa kan Rk, iska Rk ya fesar daga bakin sa sannan yace "Muje ciki zan maka bayani" sosae kan Yaseer ya kulle, shi dae yasan Rk d'in bashi da wata budurwa balle yace budurwar sa ce, kae abinda ma ya sani a yadda yasan Rk d'in baze ta6a d'aukar budurwar sa yaje da ita wani gidan ba, amma jin abinda ya fad'a ya sanya shi fad'in "Ohk, let's get in" Yaseer ya fad'a yana yin gaba, komawa Rk yayi ya lek'a ta window d'in side d'in sa sannan yace yana kallan ta yadda idanun ta suka sake cika taff da hawaye, baya so yayi wani abun da zesa ta sake yin kukan dan haka ya karyar da murya yace a tsanake "Kiyi hak'uri Madam, ya manta be fito da takaddar ba, kizo muje ciki in rubuta acan" "Ka aeko a kawo min" ta fad'a tana d'auke kae "Shikenan tunda baki shirya kar6a ba" ya fad'a yana mik'ewa ya fara takawa, babu shiri ta bud'e murfin motar ta fito tana sauke numfashi a jere a jere, murmushi ya saki lokaci d'aya yana kae hannun sa kan kwantacciyar sumar kan sa ya shafa, tana ganin ya shige cikin gidan itama ta saka k'afar ta "Barka dae Madam" Yaseer ya fad'a yana kallan ta, kamar baza tace komae ba se kuma ta d'an saci kallan sa tace ciki ciki "Ina wuni?" shi bema ji ta ba dan haka ya sake jerawa da Rk suka cigaba da tafiya se dae babu wanda ke cewa komae, ita kuma tana bayan su tana bin Rk d'in cike da sassarfa, a haka har suka k'arasa cikin parlourn "Bismilllah The great Rk" Yaseer ya fad'a yana murmushi dan sosae yaji dad'in ganin Rk d'in, shima murmushin ya maeda masa sannan ya k'arasa cikin parlourn ya zauna kan had'ad'd'iyar kujerar dake cikin parlourn, tsayawa tayi kawae tana cigaba da kallan sa, so take kawae taga ya d'auki takadda amma bata gani ba dan haka ta cigaba da tsayuwar ta "Madam ki shigo mana!" Yaseer ya fad'a yana kallan Ayrah "Rabu da ita, bata buk'atar komawa gida ne" Rk ya fad'a yana d'an kallan ta ta gefen ido, a hankali ta cigaba ta takowa zuwa cikin d'akin har lokacin idanun ta na cike da k'wallar nan, seta nemi gefen wata kujera ta zauna tana cigaba da k'ik'k'ifta idanu, murmushi Yaseer yayi dan ya fahimci kuka take 6oyewa, toh wacece ita? Ya k'agu yaji menene had'in ta da Rk d'in, dae_dae lokacin Hameeda ta fito daga d'aki sanye cikin doguwar rigar atamfa da mayafi madaedaeci, ta k'araso cikin d'akin fuskar ta d'auke da murmushi tace "Barkan ku da zuwa" ta fad'a tana neman kusa da Ayrah da bata ma kalle ta ba ta zauna "Yawwah barka dae Madam, mun same ku lafiya?" Rk ya fad'a shima da d'an murmushin dake k'ara

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70