Skip to content

Chapter 43

Chapter 43

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

d'in. A inda Me gari ya saba zama suka isa sannan dukkan su suka tsaya, Mubarak ya kalle su yace "Ku zauna dukan ku" Ayrah ta d'aga kae a hankali ta kalli Muttala seya jinjina mata kae irin kamar nufin sa babu wanda ya gan shi, bata iya zama ba seda taga shi kan sa Muttalan ya zauna sannan ta raku6e waje d'aya kamar munafuka tana matse k'walla, zubewa Mubarak yayi a wajen sannan yace kan sa a k'asa "Yalla6ae gasu nan" kallan su Me gari yayi su duka, ita kuwa Ayrah gaba d'aya jikin ta rawa kawae yake yi har yanzu ta kasa gane mak'asudin zuwan ta wajen, dan kuwa sam ta kasa tuna yadda akayi tazo nan wajen, gyaran murya Me gari yayi sannan ya fara magana a nutse "Meya kawo ku gidan nan? Ina Alhaji Mato?" dae_dae lokacin wayar Muttala ta fara ringing, seya fiddo ta daga cikin aljihun sa, ganin me kiran ya sanya shi d'aga kae a hankali ya saci kallan Me gari sannan ya maeda kan sa kan wayar kawae ya d'aga, ban ji me akace daga can 6angaren ba na dae ji Muttalan yace "Muna wajen Me gari dukan mu" se kuma yayi shiru can kuma yace "Toh seka k'araso" Muttala ya fad'a yana katse wayar sannan ya kalli Me gari yace "Yalla6ae yanzu ma Alhaji Maton ze zo da kan sa" "Ahh toh Masha Allah" Me gari ya fad'a yana gyara zaman sa. Shiru ne ya wanzu a wajen na tsawon mintuna har zuwa lokacin da Alhaji Mato ya k'araso wajen da sallama cikin shadda kamar ko da yaushe me babbar riga, tumbin nan nasa kullum kamar k'ara ha6aka yake yi ya samu waje ya zauna abin sa, haka jajayen idanun sa ma sun k'ara wani ja kamar me ciwon ido, ya zube gaban Me gari da fara'a akan fuskar sa "Barka da wannan lokaci Ranka ya dad'e yalla6ae" ya fad'a yana d'aga hannun sa alamar girmamawa "Barka dae Alaji Mato, ashe ma kana kan hanya, kasan mutane ba abin yadda bane shiyasa na saka amin bincike, amma tunda ga ka kazo seka d'auki bak'in ka ku koma" gyara zama Alhaji Mato yayi yana satar kallan sahibar tasa da yaga ta k'ara masa kyau yace "Wato yalla6ae dama wajen ka nazo gaskiya" "Toh Ikon Allah, Allah yasa dae lafiya" Me gari ya fad'a shima yana gyara zaman sa, seda Alhaji Mato yaja numfashi sannan ya sake gyara zaman sa yana tunanin ta inda ze fara "Yalla6ae wannan da kake gani mata ta ce, tsautsayi yasa na sake ta kuma ban maeda ta ba har ta gama idda, shine nake so a maeda mana auren mu yalla6ae dan nasan aekin ka ne wannan d'in" d'aga kae Me gari yayi ya kalli Ayrah dake zaune tana jin maganar da Alhaji Mato yake yi ba dan tana fahimtar sa ba, ko kuma ta fahimci akan ta ake magana ba "Ikon Allah" shine abinda Me gari ya fad'a kawae sannan ya sake yin gyaran murya yace "yanzu a take kake nufi?" da sauri Alhaji Mato ya sake yin wani murmushin kafin yace "Ehh Ranka ya dad'e yalla6ae" "Allah ya gafarta malam ni ne nake neman auren ta yanzu, kuma muna son junan mu" dukkan su suka d'aga kae suna kallan me maganar cike da mamaki, da wani irin sauri ta d'aga kae ta kalli me maganar dan ta tabbatar wa da kan ta abinda take tunani, ita gaba d'aya kan ta ya kulle, har tana so ta dena gane komae, magana ake tayi gashi dae a gaban ta amma bata ganewa, bata fahimta, bata fuskan ta, ji take kamar dukan su wani yare suke yi, shin akan wa suke magana? Akan wata mace suke magana? Cigaba tayi da kallan sa sanda yake neman waje ya zauna yana lumshe idanun sa saboda gudun da bugun zuciyar sa keyi wanda ya wuce misali, ba k'in biyan kud'in shekara ba baya tunanin ko da abinda yafi hakane ya shiga tsakanin Abbu da Abba ze iya bari Ayrah ta auri wanin sa, wanin ma a gaban sa, Abba yace baze auri er sa ba se gashi wani ya d'auko ta wata uwa duniya dan a d'aura musu aure, toh meyasa baze yiwa kan sa wannan fad'an har yayi winning ba? Ko me zeyi se yayi yadda yayi aka d'aura musu aure a garin nan ba da wannan k'aton mutumin ba dashi za'a d'aura, tun da yasan ko d'aukar ta yayi ya maeda ta gidan su daga nashi iyayen har nasa ba amincewa zasu yi da auren junan su ba, dan haka ze zage damtse yasan yadda zasu yi suyi auren sirri in dae hakan ce mafita, ya ceci zuciyar sa sannan ya ceci Ayrah daga hannun wannan mugun mutumin "Malam daga ina kae kuma?" Me gari ta fad'a yana kallan Rk, ajiye numfashi Rk yayi sannan yace har lokacin be kalli kowa ba "Soyayya muke yi da ita, kuma bazan iya bar wa wani ita ba" yayi maganar a nutse kae ba zaka ta6a cewa tsara zancen yayi ba, bin sa da kallo Alhaji Mato yake yi dae_dae lokacin da Rk ya d'aga kan sa ya watsa masa wani banzan kallo me nuni da abubuwa da dama, da sauri Alhaji Mato ya d'auke kan sa yana jin tabbas idan yace wani abun asirin sa ka iya tonuwa mutuncin sa ya zube a banza, dole yayi tunanin mafita, d'aga kae Me gari yayi ya kalli Ayrah dake zaune kamar wadda aka kafe ta yace "Toh ke kin ji? Shin kina da ta cewa?" se a lokacin Ayrah ta d'aga kae ta kalli Me gari tana jin zuciyar ta kamar zata tarwatse, kwata kwata ta kasa bud'e bakin ta ballantana tace wani abu, toh ta bud'e d'in ma tace mene? Gaba d'aya ta kasa fahimtar wannan wasan kwaekwayon da suke gabatarwa a gaban ta, a hankali ta shiga tuna maganar Muttala se kawae ta shiga girgiza kae kamar wata kad'angaruwa, sauke numfashi Me gari yayi sannan ya kalli Alhaji Mato da kuma Rk yace "Ina ganin dukan ku ku tashi ku tafi, zan rik'e ta a hannu na zuwa gobe kafin a kira magabatan ta, gobe bayan an sakko daga masallaci ni da kae na zan d'aura mata aure da wanda ta za6a a matsayin wanda take so!" dukan su kallan Me garin suke yi, Alhaji Mato yana ji kamar ya tashi ya rufe Rk da duka, idanun nan nasa suka k'ara yin jawur, ta 6angaren Rk kuwa gaba d'aya tunanin sa ya tafi yadda zeyi ya shawo kan Ayrahn ta amince da auren sa cikin garin nan. Kamar wata kurma doluwa kuma bebiya haka take bin wadda akace ta mata jagora zuwa cikin gidan Me garin, har lokacin ta kasa amincewa ba wasan kwaekwayo akeyi ba, a haka har suka k'arasa cikin wani madaedaecin d'aki seda ta zauna sannan wadda ta kawo tan ta fice daga d'akin. ... A zaune take kamar wata munafuka cure waje d'aya, kuka kawae take yi cikin rashin sanin abin yi, wannan mutumin kawae take jira yazo ya mayar da ita gida amma har yanzun shiru, ta rasa gane dalilin ta na zuwa k'auyen nan, abinda ya sake jefa ta cikin wani mad'aukakin mamaki shine ganin

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70