Chapter 55
Chapter 55
k'irjin ta ya soma bugawa idan ta tuna abinda ze fito daga bakin na ta, ba tare da tunanin komae ba ba kuma tare da tsayawa dogon nazari ba ta furta "Abba ban san daga inda zan fara ba Umma wani cukurkudad'd'en al'amari ne Umma" ta k'arasa maganar tana kallan Umma, dukkan su zuba mata ido suka yi suna kallan ta musamman Yah Sadeeq dake karanto zallar gaskiya a tattare da k'anwar ta sa amma duk da haka bece komae ba, ganin da tayi duk suna kallan ta ya sanya ta cigaba da fad'in "Umma yanzu haka an d'aura mana aure da Raj fa!" ta k'arasa fad'a tana jin wani zafi da ciwo a cikin zuciyar ta musamman yanzu data tuna a gaban Abba ne kuma laefin da aka yiwa Abba ne ya sanya yace ba zata aure shi ba, da wani irin sauri Umma ta saki Ayrah dake jikin ta sannan ta soma matsawa gefe har lokacin idanun ta akan Ayrahn k'irjin ta kuma still yana bugawa da k'arfin daya wuce na d'azu, Abba da Yah Sadeeq suma duka kallan ta suke yi kafin Abba ya girgiza kae yana d'auke kae wani murmushin takaeci me ciwo na su6uce masa, shi kan sa ji yake daze iya kuka da yayi koda abinda yake ji cikin zuciyar sa ze ragu, ya d'auki sakanni masu yawa a hakan sannan ya juyo yana cigaba da kallan Ayrahn dake share hawayen fuskar ta "Ashe zargin da muke gaskiya ne Ayrah? Bama iya za6ar namiji ki kayi akan mu ba? Kin je kin auri abinda zuciyar ki ke so acan wani wajen? Bama iya guduwa kika yi ba Ayrah? Hadda aure ku kayi? Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" Abba ya fad'a yana sauke numfashi saboda yadda k'irjin sa ya masa wani irin nauyi sannan a hankali ya zame a wajen ya kwanta ko zeji sauk'in abinda yake ji, se a lokacin hawayen da suka taru a cikin idanun Umma suka zubo cike da takaeci ta furta "Ayrah kin cuce mu kin cuci kan ki, kin wulak'anta mu kin wulak'anta kan ki, kin tozarta mu kin tozarta kan ki tunda har kika iya d'aukar jiki kika bi saurayi kuka tafi wani wajen aka d'aura muku aure saboda iyayen ki sun ce basa son shi, meyasa kika yi haka Ayrah?" Umma ta k'arasa fad'a wasu zafafan hawaye suna zuba akan fuskar ta, Yah Sadeeq dake gefe kawae kallan su yake yi su duka musamman Ayrah da yaga ta rikice daga kallan daya mata tun farkon lokacin da Abba ya fara magana, a hankali ta shiga girgiza kae k'irjin ta na wani irin bugawa idanun ta da suka cika taff da hawaye har wani dishi_dishi suke gani, cikin kuka ta kalli Umma tana girgiza kae tace "Umma ku yafe min don Allah, Umma nayi nadamar zuwa na duniya, ni banza ce kuma shashasha Umma, Umma ku tsaya inyi muku bayanin abinda ya faru don Allah.. wallahi.." d'aga mata hannu Abba yayi daga inda yake kwance dafe da saetin zuciyar sa yace "Ki tashi ki fita a gidan nan, bana son na sake ganin ki cikin gidan nan, kin za6i d'a namiji akan mu saboda haka kije duniya ce ae.." sake fashewa da kuka tayi a cikin ranta tana maemaeta kalmar "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" shin me yake shirin faruwa ne? A cikin su babu wanda ze tsaya ya saurare ta tayi musu cikakken bayani "Umma bani da laefi" ta fad'a cikin kuka, ba tare da Umma ta kalle ta ba tana jin wani iri cikin ranta, tana jin danasanin haehuwar 'ya irin ta, data san idan tazo duniya zata bijirewa umarnin su ta aekata wannan mummunan abun da har su mutu ba za'a bar yin gulmar su da hakan ba da tun farko tayi addu'ar Allah yasa cikin ya zube "Ki tashi ki fita a gidan nan bana son sake ganin ki, idan kuma na sake ganin k'afar ki cikin gidan nan sena tsine miki.." Umman ta k'arasa fad'a tana gyarawa Abba kwanciya lokaci guda kuma tana goge hawayen da suka k'i tsayawa da zuba akan fuskar ta, runtse idanun ta tayi hawaye sunk'i dena zuba daga idanun ta "Allah ka d'au raena na huta da wannan bala'in.." ta fad'a tana jin yadda ilahirin jikin ta ke rawa kamar mazari, kallan ta Umma ta sake yi tana shirin cewa wani abun seta mik'e da sauri, bata so Umman ta sake furta wata kalma mara dad'i a kan ta dan haka ta mik'e duk da yanda take jin jiri na d'ibar ta amma haka ta tashi bata ko ganin gaban ta ta fito daga cikin gidan..Tafiya kawae take yi ba tare da tana sanin inda take jefa k'afafun ta ba, hawaye ne ke ta sintiri akan kuncin ta, Raj ya cuce ta, ya cuci rayuwar ta, ya yaudare ta da kalaman bakin sa daga k'arshe ya raba ta da iyayen ta, ya sanya bata da wani 'yanci ta koma k'ark'ashin sa akan wani son zuciya nasa, meyasa dangin su duka suka kasance masu son zuciya? Meyasa Raj zeyi mata haka? tunda take bata ta6a tunanin soyayya na komawa k'iyayya ba, sedae yau gata dumu dumu cikin matsananciyar k'iyayyar Raj wadda bata san adadin ta ba, wadda ke ruruwa yanzun a cikin zuciyar ta saboda abinda ya aekata mata, bata jin a yanzu a fad'in duniyar nan akwae wanda ta tsana kamar shi, dan kuwa duk mutumin daze raba ta da iyayen ta mak'iyin ta ne, kamar daga sama ta jiyo muryar sa daga gefen ta "Muje ki huta da kae na zan zo na musu bayani" ya fad'a a nutse, wani banzan kallo ta d'aga fusatattun idanun ta ta watsa masa tana jin yadda zuciyar ta ke cigaba da mata zafi, bata jin a yanzu zata iya masa magana, ko da kuma ta bud'e baki da niyyar yin magana to tasan kalaman da zasu fita daga bakin ta masu zafi ne zuwa ga wanda za'a fad'awa, dan haka ta cigaba da tafiya ba tare data d'auki wani mataki akan hawayen dake ta zuba daga idanun ta ba, ya san yanzu ran ta a 6ace yake kuma ko ze mutu baza ta kula shi ba ballantana ta shiga motar sa, dan haka ya kalli gefe da gefe sannan ya k'arasa a nutse zuwa inda take babu 6ata lokaci ya sanya hannun sa ya d'auke ta dukan ta, duka k'arfin ta ta saka tana k'ok'arin k'wace jikin ta dan ta sauka daga jikin sa amma ina yak'i bata damar hakan, sema k'arasawa da yayi ya bud'e front seat ya jefa ta ya kulle sannan ya koma mazaunin driver ya shiga shima ya kulle side d'in sa, hannun ta ta saka dan bud'e murfin k'ofar amma ta ji shi a rufe dan haka ta sanya hannun ta ta fara turawa nan ma ta kasa, kawae seta koma jikin kujerar tana fashewa da wani marayan kuka, daga inda yake ya d'an runtse idanun sa kukan nata na ratsa shi, amma a yadda yaga k'wayar idanun ta cike suke da fusatattun abubuwa ya sanya shi yi mata shiru ta cigaba da rera kukan ta kamar ran ta ze fita. ... Wajen minti 1 bayan ta fita babu wanda ya sake cewa komae, Yah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70