Chapter 28
Chapter 28
motar sa yayi gaba ita kuma ta rufa masa baya zuwa wajen, ya shiga motar sa yayin da ita kuma ta shiga ta ta kowanne ya tada tasa. A hankali take takawa fuskar nan ta ta kamar wadda aka yiwa duka, se cika take tana batsewa, wayar ta ce tayi k'ara ta zaro ta daga cikin hijab d'in jikin ta sannan ta d'aga tana karawa a kunnen ta, daga can 6angaren Yah Sadeeq yace "Ayrah.." "Na'am Yah Sadeeq" ta fad'a tana d'an tura bakin ta gaba kad'an, daga can 6angaren yayi murmushi kana yace "Yau kuma waya ta6a min k'anwa ta? Ko dae wannan likitan ne?" daga inda take ta d'an yi murmushi jin yadda Yah Sadeeq d'in ya gano hakan da wuri, ko da yake hakan ba abin mamaki bane dan kusan koda yaushe k'orafin ta baya wuce akan Rk "Shi ne" ta fad'a tana sake kwa6e fuska kamar tana gaban sa "Wae ni kam meyasa doctorn nan ya takurawa k'anwa ta ne?" "Oho masa" kafin Yah Sadeeq d'in yace komae ta sake fad'in "Yah Sadeeq ina Umma?" "Umma na gida, idan na koma zan kira ki In Allah ya yadda se ku gaesa" bata san sanda wani murmushi ya su6uce mata ba, haka suka cigaba da hira da yayan nata cike da k'aunar juna. ... Ita da Jidda ne cikin Cafe d'in, mutumin ya kalle su sanda Ayrah ke fad'in "Pls kayi mana kaaji" seya jinjina kae sannan yace "Ohk, amma zan je na samo mae idan zaku jira ni" "Babu matsala.." Ayrah ta fad'a tana neman waje ta zauna, dae_dae lokacin da mutumin ke shirin fita daga wajen yayi dae_dae da lokacin daya shigo cikin madaedaecin Cafe d'in, yana sanye cikin wata kyakykyawar riga da bluen jeans wad'anda suka matuk'ar yi masa kyau, kamar koda yaushe yanzu ma kan sa babu komae se kwantacciyar sumar kan sa da koda yaushe kamar ana k'ara mata shek'i ne da kyau, dakatawa mutumin yayi da murmushi kan fuskar sa yana fad'in "Doctor.. doctor barka da zuwa" yayi maganar yana mik'a masa hannu, Rk ya mik'a masa hannu suka gaesa shima da wani tsadadden murmushi akan fuskar sa, Jidda data ga shigowar sa sanda ta mik'e tace "Barka da wannan lokaci Sir" "Barka" yayi maganar har lokacin hannun su na cikin na juna shi da mutumin "Bari naje pls Ayrah, me zan siyo miki?" murmushi tayi kana tace "Mango" dariya Jidda tayi k'asa k'asa sannan tace "Nima bansan meyasa na tambaya ba bayan na san ina tare da mayyar mangoro Ayrah!!" ba saurarar su yake ba kuma be damu da kallan wadda ta gaeshe shi ba amma tabbas wannan maganar ta sauka cikin kunnen sa har be san sanda yayi sauri ya d'aga kae ya kalli Jiddan ba, ita kuwa sosae hakan ya mata dad'i har da chanja tafiya ko da ta janyo hankalin sa, se dae abinda bata sani ba sam bema kalli fuskar ta ba balle akae ga kallan tafiyar ta, bega wadda take bayan ta ba saboda ita Jidda ta taso zata fita ne, kafin kuma ya maeda duban sa wajen seya jiyo mutumin nan na fad'in "Raj pls bari na d'an je na samo mae zan yi wani aeki ne, idan babu damuwa a jira ni pls" yayi maganar yana murmushi, se kawae ya d'aga masa kae yana lumshe manyan idanun sa, shi kuma yace "Toh nagode" yayi maganar yana bin bayan Jidda data fita, tunda taji sunan da mutumin nan ya ambata ta d'aga dara daran idanun ta ta kalli wanda aka kira da Raj d'in, bata san sanda ta mik'e ba har handout d'in dake kan cinyar ta ta zame, shima ita yake kalla yana so ya bar k'wak'walwar sa tayi aekin daya dace, cikin en sakannin da basu wuce 2 ba idanun su suka sark'e cikin na juna, a lokaci guda zuciyoyin su suka buga wanda har seda Rk ya d'an lumshe manyan kyawawan idanun sa, yanayi ne da be ta6a jin sa akan kowacce d'iya mace ba, wani sabon al'amari ne daya dad'e yana bashi mamaki, dukkan su se suka kaasa d'auke idanun su daga cikin na juna duk da yadda hakan ke azalzalar zuciyoyin kowannen su, sun kae tsawon minti 1 a haka kafin Ayrah tayi watsi da duk wani tsoro, wasu wasi tare da taraddadi ta watsa su gefe sannan ta tattaro jarumta kana ta d'aga yatsan ta dake rawa kamar me, ta nuna shi sannan ta bud'e bakin ta daya mata wani irin nauyi bayan ta lumshe idanun ta sanda wasu kyawawan hawaye suka zuba akan fuskar ta ta furta.... Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 019_020 "Raj!?" ta k'arashe maganar da sigar tambaya, lumshe nasa idanun yayi daga cikin nata yana jin yadda zuciyar sa ke azalzalar sa na k'ara k'aemi, cigaba tayi da kallan sa har lokacin bugun zuciyar ta be koma dae_dae ba jira take kawae ta tabbatar, taji daga bakin sa cewar da gaske shine Raj, a hankali ya jinjina kan sa sannan da muryar sa wadda ta d'an shak'e shima saboda tsananin mamaki yace k'asa k'asa, wanda idan ba dan babu hayaniya a wajen ba da ko ita da take a cikin wajen ba zata ji ba "Ayrah!!?" seta shiga jinjina kae da sauri wasu hawaye na cigaba da ambaliya akan kuncin ta sannan lokaci guda kuma ta saki wani murmushi duk da har lokacin bata dena kukan ba, ta kaasa daurewa, ta kaasa cijewa, har izuwa lokacin wani irin azalzala zuciyar ta ke yi tana wani irin zillo dan haka cikin k'ank'anin lokaci da kuma sauri ta k'arasa ta rungume shi lokaci guda tana runtse idanun ta ko zata ji sauk'i daga abinda take ji a cikin zuciyar ta, k'irjin ta ya cigaba da bugawa da sauri da sauri kamar wadda tayi gudu, kamar wani soko ya tsaya kawae bayan sauke wata doguwar ajiyar zuciya, yana jin yadda ta rik'e shi sosae da alama tsananin farin ciki ne ya sanya ta hakan, wani sassanyan murmurshi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa sannan akan la66an sa ya furta "Har yanzu dae bata chanja ba" hannun sa ya saka ya zame ta daga jikin sa sanda take kuka me d'an sauti, a hankali ya k'arasa ya zaunar da ita kan kujerar wajen sannan ya saki hannun ta a ransa yana furta "Astagfirullah" a kunnen ta abinda ya fad'a d'in ya sauka duk kuma se taji wata matsananciyar kunya ta kama ta, ta kaasa controlling kan ta a lokacin, ta rasa abinda za tayi taji sauk'i, farin ciki da kuma mamaki gami da son tabbatar da abinda ta gani ne ya sanya ta rungume shi ba tare da wani tunani ba, yana tsugunne akan k'afafun sa daga k'asan inda take yana cigaba da kallan kyakykyawar fuskar ta, shi kan sa har ya zuwa lokacin ya kasa dena mamakin shin da gaske Ayrah ce? wannan d'in Ayrahn sa ce? Dae_dae lokacin ta d'ago jajayen idanun ta ta sauke su a kan sa farar fuskar nan tayi jawur haka zalika a d'an shagwa6e ta kalle shi, be san sanda wani murmushi ya su6uce masa ba, babu shakka ita d'in ce, kuma har yanzu halayen ta na nan "Da gaske
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70