Chapter 40
Chapter 40
sauke wayar daga kunnen sa yana sake k'arewa wayar kallo, anya kuwa ita d'in ce? Anya kuwa Ayrahn sa ce? Menene haka ya faru wanda ya chanja mata ra'ayi haka daga daren jiya zuwa yau d'in? Me akace mata yayi da zata jefe shi da wad'annan kalmomin? Tabbas da tasan yadda kalmomin nata suka jefa shi cikin wani irin yanayi da bata fad'a masa ba, meya same ta haka? Shin ba shine ya kamata ya fad'i hakan ba tunda iyayen tane suka yiwa nasa iyayen laefi ba? Amma beyi hakan ba se ita? Kodae dama bata son sa ne tuntuni? Ko kuwa dae akwae wani 6oyayyen al'amari wanda dukan su basu sani ba? Lallae ya zama dole yasan gaskiyar al'amarin nan, yasan dalilin Ayrahn na jifan sa da wad'annan muggan kalaman, zuciyar sa dake masa wani irin zafi tana kuma harbawa da k'arfi ya danne da hannayen sa yana runtse idanun sa, ya kae wajen minti d'aya a hakan sannan ya bud'e idanun sa yana fesar da iska me zafi daga cikin bakin sa sannan kae tsaye ya fice daga d'akin bayan ya d'auki mukullin motar sa. Da sassarfa ya k'arasa inda motar tasa take ya shiga ya tashe ta da sauri duk da shi d'in ba ma'abocin gudu bane, Abbu da fitowar sa kenan daga parlourn sa yaga tashin motar Rk d'in, mamaki ne ya kama shi sosae dan shi kam yayi tunanin tun yau Rk d'in ze koma asibiti bakin aeki, dan shi indae ta 6angaren sa ne babu lokacin 6atawa, kowanne lokaci baya barin sa ya tafi a banza seya nemo abinda zeyi a cikin lokacin wanda ze saka ya samu kud'i, shiyasa ko lokacin da Rk d'in yaje Zaria yaga baze iya barin sa haka nan babu wani abun daze samu kud'i ba, dan haka shi in dae ta shine tunda jiya ya dawo toh yau ma ya d'ora kan aekin babu wani 6ata lokaci "Toh ina ze je haka?" Abbu ya tambayi kan sa, ganin dae babu wanda ze amsa masa tambayar ne ya sanya shi cigaba da tafiya a ran sa yana cigaba da tunanin inda Rk d'in zeje. ... Driving yake yi amma har lokacin tunani yak'i barin ruhi da k'wak'walwar sa, shi likita ne yasan illar da tunani kan iya haefarwa dan ya kan sha bawa mutane shawara akan hakan, amma a wannan karon shi kan sa ya kasa hana kan sa, se yanzu ya fahimci ashe idan k'wak'walwa na son yin tunani ba mutum ke tsarawa kan sa yin tunanin ba ita da kan ta take yin tunanin kuma babu yadda ka isa kayi da ita. A haka dae har ya k'arasa unguwar ta su yana tuna kwatancen data masa, a d'an nesa kad'an ya tsaya da gidan yana kallan cikin layin da babu kowa kasancewar safiya ce dan kuwa har lokacin ko 8 ba tayi ba, seya d'aga lumsassun idanun sa dake d'auke da bacci ya dubi gidan a ran sa yana sak'a tabbas nan d'in ne in dae yabi kwatancen data masa dae_dae, wayar sa ya janyo da take ajje kan kujerar kusa dashi ya danno number ta cike da fatan ta d'aga wayar, se dae addu'ar sa bata kar6u ba dan kuwa har ta gama ringing d'in bata d'auka ba tana kuma jin wayar na ringing ta san me kiran shiyasa tak'i kula wayar, wani kiran ne ya sake shigowa seta mik'e daga kwanciyar da take tana ganin blocking d'in da tayi niyyar yi tun d'azun shine kawae mafitar da tasan idan tayi ze dena kiran ta, kafin takae ga aekata abinda tayi niyya Umma ta d'aga labulen d'akin ta lek'o "Ayrah ki fito ki samu wani abun ki ci" se ta d'aga kae da sauri sannan ta furta "Toh.." kawae, itama Umman bata takura ba dan tana so ne ta bari ta gama kukan ta sannan ta rarrashe ta, idan ba haka ba tasan yanzu tunzura ta kawae zata yi, Umman na fita Ayrah ta maeda kallan ta kan wayar dae_dae lokacin da wani sak'o ya shigo cikin wayar, seta dakata ta shiga cikin sak'on, gajeren sak'o ne daga number Rk a hankali ta shiga karantawa "Don Allah ki fito ina k'ofar gidan ku, inaso naji tabbacin maganar dake fitowa daga cikin bakin ki, ina so na tabbatar da abinda kunnuwa na suke ji" fuskar ta a matuk'ar tamke haka zalika ran ta ya sake 6aci, tana ga lokaci yayi da zata kira shi da sunan dake ta yawo a cikin k'wak'walwar ta koda hakan zesa ya fahimci ta gane wanene shi da mahaefin sa, ko kuwa ya d'auka saboda son da take masa zata iya fatali da umarnin iyayen ta? Ko kuwa me yake nufi da ita? "Butulu" shine sunan dake ta yawo a k'wak'walwar ta, wayar ta ta ta d'auka ta danna number sa a blocking sannan ta jefar da ita gefe ta mik'e tana sanye cikin doguwar rigar atamfa ta zari hijab ta saka sannan ta lek'o tsakar gidan tana hange, babu kowa a tsakar gidan taji dad'in hakan dan bata so ta sake 6atawa Abba ko Umma rae daga dawowar ta jiya bayan 6acin ran data saka musu a jiyan, a hankali ta shiga takawa cikin tsakar gidan har zuwa sanda ta fice daga cikin gidan... ... Wanda ke driving d'in ya kalli Muttala yace "Nifa na gaji wallahi, tun jiya muke a wajen nan amma har yanzu banga alamar zata fito ba" tsaki Muttala yaja kana yace "Gaggawar ta menene? Wallahi idan ta nine bank'i mu sake kwana cikin motar nan ba tunda dae babu wanda ya ganmu har yanzun" Muttala ya fad'a har lokacin idanun sa na kan k'ofar gidan su Ayrah.. A dae_dae lokacin ne Ayrah ta fito daga cikin gidan, a hankali ta shiga bud'e manyan idanun ta dan hango inda motar sa take. A lokacin ne shi kuma kiran Abbu ya shigo wayar sa, seya d'auki wayar yana karawa a kunnen sa idanun sa a lumshe dan yanzu kuma be san da wanne Abbun yazo ba gashi kuma rok'on da yayi wa Ayrah baya tunanin taji ta kar6a zata fito, se abin ya sake masa yawa, daga can 6angaren Abbu yace "Ka shiga asibitin ne?" shiru yayi na d'an wani lokaci kafin a hankali ya bud'e bakin sa bayan ya kae hannu ya shafa kwantaccen sajen dake kwance luff luff akan fuskar sa "Abbu ban shiga ba tukunna" shiru Abbu yayi yana sake karanto yanayin Rk d'in daga cikin muryar sa, yace a hankali "Ko dae akan maganar dana maka jiya ce?" shiru yayi dan ko ya bud'e bakin sama be san abinda zece ba, Abbu yace "Toh ka bud'e kunnen ka da kyau kaji, in dae akan maganar nan ce ka kwantar da hankalin ka kamar an riga an d'aura muku aure ne da Muneerah, dan haka ina ganin ka ajje komae a gefe ka koma bakin aekin ka" kafin yace komae Abbun ya katse wayar, seya jefar da wayar yana sake jin yadda yanayin nasa yake sake ta'azzara, abubuwa na neman yiwa zuciya da k'wak'walwar sa yawa. A hankali ta cigaba da takawa har lokacin fuskar ta babu walwala manyan fararen idanun nan nata sun yi zuru zuru kamar mara lafiya, da sauri wanda ke driving
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70