Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

sauke ajiyar zuciya Umma tayi dae_dae lokacin da Abba yayi sallama cikin d'akin, da gudu Ayrah ta tafi ta rungume Abban tana fad'in "Abba sannu da zuwa" hannu ya saka ya d'aga ta sama sannan yace "Yawwah an baby" ya fad'a yana sauke ta sannan yaja hannun ta zuwa cikin d'akin suka zauna "Sannu da zuwa Abban su" Umma ta fad'a tana kallan Abba, kallan ta Abba yayi yana karantar yanayin ta cikin kulawa yace "Wani abu ya faru ne?" girgiza kae tayi sannan tace "A'ah kawae dae Ayrah ce.." "Me Ayrahn tayi?" Abba ya fad'a yana gyara zaman sa, ajiyar zuciya Umma ta sauke tana bin Ayrah da kallo wadda tayi cikin d'aki da gudu "Kamar kasan sunan Raj a bakin Ayrah koh?" d'an shiru Abba yayi sannan yace "Ehh k'warae, kamar d'an ajin su koh?" girgiza kae Umma tayi sannan tace "Bana tunanin d'an ajin su ne, a yadda take bani labari kuma na fahimta, kamar ba'a makarantar yake ba, ina nufin baya zuwa makaranta, kuma yana son karatu shiyasa yake zuwa yana lek'e a ajin su.." "Lek'e kuma?" "Wallahi kuwa Abban su, nima abin ya bani mamaki" "Ikon Allah.." Abba ya fad'a yana jinjina kae "Shikenan In Sha Allah zan binciki al'amarin, idan da akwae halin taemakawa sena taemaka masa" murmushi Umma tayi kana tace "Allah ya saka da alkhaeri Abban su, ya k'ara bud'i.." ire iren halayen Abban dake sake birgeta kenan, duk da shima ba wani k'arfin hali yake dashi ba amma yana iya k'ok'arin sa wajen ganin ya taemakawa wanda ke k'asan sa kuma mabuk'aci, shima murmushin Abba yayi sannan yace "Albishirin ki.." "Goro.." Umma ta fad'a tana gyara zama "Alhaji mato ya yadda ze bani hayar shagon nan, idan yaso a hankali sena dinga biyan sa.." "Kae Masha Allah, Alhamdulillah Allah mun gode maka" Umma ta fad'a fuskar ta d'auke da mad'aukakin murmushi "Toh amma ina tunanin Sadeeq yayi k'ank'anta da wanda ze dinga taemaka min, koma ba haka ba inaso dukkan su su samu karatu me zurfi.." Abba ya fad'a yana zurfafa tunani cikin k'wak'walwar sa, murmushi Umma tayi sannan tace "Ae Abban su wannan me sauk'i ne In Allah ya yadda, tunda aka samu wannan" "Hakane kuma.." Abba ya fad'a yana kallan Yah Sadeeq daya fito daga cikin d'aki sanye cikin Uniform d'in Islamiyya, ya k'araso ya zauna yana kallan Abban yace "Abba sannu da zuwa" "Yawwah Sadeeq..za'a tafi makarantar ne?" "Ehh Abba" "Toh Allah ya kiyaye" Abba ya fad'a, Sadeeq ya amsa da "Ameen, Umma na tafi.." ya kae k'arshen maganar yana kallan Umma, itama addu'ar ta masa sannan ya fara k'ok'arin fita, yana dab da fita d'in Abba yace "Afff, Sadeeq..!" juyowa yayi yana amsa kiran Abban sannan ya dawo, Abba yace "Gobe idan kaje makaranta akwae wani yaro... Kikace sunan sa?" ya k'arasa maganar yana kallan Umma "Raj.. Haka dae tace min sunan sa" "Ikon Allah.." Abba ya fad'a yana maeda duban sa kan Yah Sadeeq yace "Kaji sunan sa Raj, anan makarantar ku yake, ita Ayrah ta sanshi, seta nuna maka shi kazo min dashi idan an tashi" "Toh Abba.." Yah Sadeeq ya fad'a yana ficewa daga d'akin, a ransa yana tuna sunan, kusan kullum se Ayrah tayi maganar me sunan amma be ta6a bawa zancen muhimmaci ba se kuma gashi Abba da kansa yace a kira masa shi... *Zarah Bint Yusuf (Mhiz Innocent)*✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* Page_004_005 ____Tun kafin ta k'arasa ta hango shi zaune yana kallan inda ta saba 6illowa ta wajen sassanyan murmurshi kwance akan fuskar sa, itama murmurshin ta maeda masa sannan ta k'araso ta zauna, ya sake yin wani murmurshin sannan yace yana mik'a mata wata leda "Gashi.." d'an bud'e manyan idanun ta tayi kamar wata babba sannan ta kar6a, tun kafin ta bud'e tasan menene dan haka ta rik'o hannun sa ta rungume tana jin dad'i tace "Wae siyowa kayi?" girgiza kae kawae yayi yana ta6e baki, bata kuma bi takan zancen ba suka cigaba da abinda ya kawo su wajen, suna yi tana shan mangoron ta, shi kuma yana kallan ta hakan na masa dad'i ko ba komae shima yau yayi mata wani abun da taji dad'i.. Seda aka tashi daga school d'in sannan Yah Sadeeq ya kama hannun Ayrah dake jiran sa a k'ofar ajin su "Muje ki kae ni wajen Raj" ya fad'a har lokacin suna tafiya, babu musu ta gyad'a kae tana cigaba da wasan ta hannun ta cikin nasa a haka har suka k'arasa inda tasan zasu same shi, cikin sa'a kuwa se suka tadda shi a tsaye da alama shima ya gama abinda zeyi zeyi gaba ne, juyawar da zeyi se suka had'a ido da Yah Sadeeq, sosae k'irjin sa ya buga sanda yagan su suna cigaba da tahowa inda yake, kawae se ya tsaya ya kasa gaba ya kasa baya, sam idanun sa be sauka akan Ayrah da keta yi masa murmurshi ba, a hankali ya lumshe manyan idanun sa dae_dae lokacin da suka ida isowa dab dashi, Yah Sadeeq yace yana kallan sa "Sannu.." d'aga ido yayi ya kalle shi se dae ya gaza cewa komae dan be san da wanne shi kuma yazo ba, se dae ga mamakin sa se yaji yace "Abban mu na son ganin ka idan babu damuwa" idan babu damuwar daya ambata shi ya sanya ya d'an ji sanyi dan da farko har ya fara tunanin ko za'a raba shi ne da Ayrah, amma abinda be gane ba shine meye had'in sa da Abban nasu? Ko dae abinda zuciyar tasa ke harsashe ne kawae dae yayi amfani da kalmomi biyun nan dan kada ya saka masa shakku akan maganar? "Zamu iya tafiya?" ya tsinto maganar Yah Sadeeq d'in "Toh" ya furta cikin rashin sanin mafita "Yau a gidan mu zaka kwana Raj?" Ayrah ta fad'a tana cigaba da tsalle tsallen ta, suna gaba yayin da Raj ke bayan su har suka k'arasa bakin Gate d'in ya cigaba da binsu zuwa wani waje ke6antacce kuma rufaffe wanda anan ne suka saba zama su jira Abban, Yah Sadeeq ya nemi waje ya zauna yayin da shi kuma ya tsaya a gefe tunani fall cikin ransa, Yah Sadeeq na zama Ayrah ta zame hannun ta zuwa wajen Raj ta fara masa surutu yayin da yau gaba d'aya yake jin sa a takure musamman da yake kusa da wata bak'uwar fuska, dan haka amsar sa ta zama bata wuce murmurshi da gyad'a kae, shi kam Yah Sadeeq bin su kawae yake da kallo yana mamakin yadda Ayrahn ta saba da shi cikin k'ank'anin lokaci, basu dad'e da zama ba Abba ya iso, ita ta fara yin gaba da gudu sanda ta hango Abban, Yah Sadeeq yabi bayan ta, seda ya kusa isa inda motar Abban take sannan ya tuna da Raj, ya juyo ya kalle shi yace "Ka taho ga Abban namu nan yazo" binsa yayi a baya suka k'arasa har inda Abban yake, Yah Sadeeq ya bud'e front seat ya shiga yayin da Ayrah ta shiga baya, Abba yabi Raj da kallo dake tsaye a waje kafin ya maeda duban sa ga Yah Sadeeq yace "Shine wannan?" jinjina kae yayi kafin yace "Ehh Abba" "Koma baya shi kuma ya shigo nan" Abba ya fad'a yana sake Kallan

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70