Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

ta babu d'an kwali se wata hula data saka ta zame ta har wajen rabin kan ta, wanda ya fito da kusan rabin kitson attach d'in dake kan ta, a hankali ta k'arasa ta ajje cooler data d'auko sannan ta koma ta kwaso ragowar kana ta dawo taja kujera ta zauna tana kallan sa cike da matsananciyar k'aunar sa tace "Sannu da zuwa Yaya na" se a lokacin ma shi yasan da wanzuwar ta a wajen, ya d'an d'aga kan sa ya kalle ta da kyawawan manyan idanun sa sannan ya d'auke, seta lumshe idanun ta tana jin idanun nasa kamar wani abu ne a cikin su wanda ya sanya bata iya jure kallan cikin k'wayar idanun sa, sosae taji dad'in yadda ya kalle tan, kafin ta dawo daga wannan kuma taji yace "Yawwah barka.." seta sake yin murmushi tana janyo plate ta fara serving nasa, Mummy da fitowar ta kenan daga d'aki ta kalli Muneerat dake zuba masa abinci cikin plate da gasken gaske, seta girgiza kae a ranta tana raya "Lallae soyayya me chanja mutum" dan kuwa tasan halin k'wuiwa irin na d'iyar ta ta, bata aekin komae cikin gida, koda abinci ne kuwa se dae a kawo mata idan an kawo kuma a zuba mata, ina ganin da da dama ma cewa zata yi a bata a baki. Plate d'in ta tura gaban sa sanda ta gama zuba komae a muhallin sa sannan ta koma kan kujerar tana fad'in "Bismilllah Yaya na" seya ajje wayar sa a gefen sa, sannan yaja plate d'in a hankali yace "Thank u" wani irin farr tayi da idanu tana jin dad'i mara misaltuwa, ko ba komae tasan tayi abin kirki tunda gashi wanda tayi dan shi d'in har godiya ya mata, zata so ace kuma wannan kwalliyar ma ya kalla yace tayi kyau da tafi kowa farin ciki, se dae tasan kafin ma ya kalle tan abu ne me wuya ballantana yace tayi kyau, wayar sa daya ajje tabi da kallo sanda ta kawo wani haske, tana jin kamar ta janyo wayar ta duba wani abu amma se dae ba zata iya ba musamman daya kasance idanun sa na wajen, se kawae ta cigaba da kallan had'ad'd'iyar wallpaper wayar tasa dake d'auke da tambarin "A" wanda ita har yanzu tayi tunanin ta fad'ad'a k'wak'walwar ta amma ta gaza gane abinda yake nufi da hakan "Uhmm Yaya na ya d'alibae?" tayi k'arfin halin fad'in hakan dan katse shirun daya wanzu a wajen na wasu mintuna dan tasan ko da zata shekara ba tace komae ba, shi shirun baze dame shi ba balle yace wani abun, d'an ta6e baki yayi gami da yamutsa fuska ta d'auka ma ba zece komae ba se kuma taji yace "Alhamdulillah, baza kiyi karatu bane?" yayi maganar sanda ya ajje spoon cikin plate d'in, bata bawa maganar daya fad'a muhimmaci ba seta kalli abincin daya keci da kallo sannan ta kalle shi sanda yake k'ok'arin mik'ewa tace "Wae har ka gama?" ta fad'a itama bayan ta mik'e tsaye cikin maraeraece fuska, sake yamutsa fuska yayi kana yace "Ehh, dama ba yunwa nake ji ba, kije kiyi karatun ki" ya fad'a yana d'aukar wayar sa, seta bishi da kallo sanda yake wucewa har ya fice daga d'akin, komawa tayi ta zauna tana jin yadda wasu k'walla suka tarar mata a ido, dae_dae lokacin Mummy ta k'araso taja kujera ta zauna tana kallan ta tace "Muneerah meya faru?" seta d'ago idanun ta ta kalli Mummyn sannan tace "Mummy kinga fa abinda yaci, kamar dan ina wajen ne fa yak'i ci da yawa fa" "Ke waye ya fad'a miki haka Muneerah?" Mummy ta fad'a tana kallan ta, seta sake maraeraece fuska sannan tace kamar zata sanya kuka "Toh Mummy se yaushe ne zamu saba, har yanzu kullum jiya i yau" ajiyar zuciya Mummy ta sauke sannan tace "Uhmm Muneerah gajen hak'uri ne dake, idan ma kun saba idan ma baku saba ba aure ne dae kin san za'a yi shi koh? Ko kuwa kin ta6a ganin Daddyn ki yayi magana 2? Sun riga sun gama magana saboda haka ki kwantar da hankalin ki, ko ba yanzu ba zaku saba nan gaba" hannu Muneerah ta saka ta sake share k'wallar idanun ta sannan tace "Da gaske Mummy?" ta fad'a kamar zata yi kuka, murmushi Mummy tayi tana jan Muneerah jikin ta tace "K'warae kuwa Munee.." se a lokacin Muneerahn tayi murmushi tana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa na mamaye ta, ji take kamar taje tace wa Daddyn nata idan za'a saka musu rana kada a saka da yawa, kae ita da zata iya ma da kanta za taje wajen Abban Rk d'in tayi masa maganar kar a saka ranar da yawa. ... Yana fitowa compound d'in gidan motar Daddy ta shigo gidan, seya k'arasa zuwa parking space d'in zuwa wajen motar, ya sanya hannu ya bud'e murfin motar inda Daddy ke zaune, Daddy ya fito yana murmushi yace "Ka dawo kenan Doctor?" murmushi Rk yayi kana yace "Ehh Daddy, barka da dawowa" "Yawwah" ya fad'a sanda yake mik'a masa brief case d'in hannun sa, hannu 2 Rk ya saka ya kar6a kana suka fara takawa zuwa d'akin Daddyn "Ya karatu ya kuma d'alibae?" Daddyn ya fad'a har lokacin suna tafiya "Alhamdulillah Daddy" Rk ya fad'a "Toh Allah ya taemaka" "Ameen" ya fad'a sannan suka cigaba da tafiya, seda suka shiga parlour sannan Rk ya ajje brief case d'in hannun sa kan kujera kana ya sake fad'in "Sannu da dawowa Daddy" "Yawwah.." Daddy ya fad'a yana sake jin k'aunar Rk d'in a ransa, d'aya daga cikin halayen daya sanya yake son aura masa Muneerah shine tarbiyyar sa, sosae hakan ke k'ara masa k'aemi wajen son cika wannan burin nasu shi da d'an uwan sa "Bari na wuce.." Rk ya fad'a "Tohm shikenan, idan da akwae wata matsalar seka sanar dani" Daddy ya fad'a yana bin Rk da kallo sanda yake ficewa daga cikin d'akin. .. Fitowar su kenan daga Capteria, su 3 ne a wannan karon, rana ta farko kenan data fara bin su Capteria saboda k'aryar su data musu yawa, ita kuwa ba er kowan kowa ba idan tace zata biye musu d'an kud'in da take dashi seta k'arar dashi a kwanaki k'alilan, dan haka take kama kan ta sosae, daga ita se Jidda se Ruks ne yanzun, tana sanye cikin abaya maroon colour da mayafin ta data yafa shi bayan ta saka wata kyakykyawar hula saboda kada sumar ta ta fito. Sun zo zasu gifta ta wajen wasu jerin reading chairs Jidda tace "Ko mu d'an zauna mu huta ne?" da sauri Ayrah ta girgiza kae sannan tace "A'ah ni kam na gaji" dan har ga Allah ta gaji so take ta zauna ta huta, idan da dama ma ta kwanta "Haka dae, Allah kuwa Ayrah kin fiya lalaci" Jidda ta fad'a tana kallan ta bayan ta jefa mata harara, murgud'a d'an k'aramin bakin ta tayi ba tare da tace komae ba, Ruks tace "Gaskiya dae kam, ya kamata mu huta" ganin su dae hutawar zasu yi ya sanya ta ta6e baki sannan tace "Ni dae na tafi.." ta fad'a tana yin gaba, suka bita da kallo sannan suka nemi waje suka zauna. A hankali take tafiya zuciyar ta

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70