Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

Raj, fitar yayi ya kalli Raj da Ayrah ke kalla tana fad'in "Ka taho mu tafi" ya kalle ta yayi murmurshi sannan ya maeda duban sa kan Yah Sadeeq daya fito daga motar "Ka shiga Abban na ciki" "Tohm" ya amsa da hakan yana k'arasawa ya shiga gaban dake a bud'e ya zauna "Barka da wannan lokaci" ya fad'a kansa a k'asa, cigaba da kallan kyakykyawan yaron Abba yayi wanda yake sa'an d'an sa Sadeeq, tun kafin ya kaega cewa yaron komae yaji wata nutsuwa tattare dashi amma duk seya watsar yace "Barka dae..yaya sunan ka?" Abba ya fad'a yana gyara zaman sa a inda yake zaune, har lokacin be d'ago ba ya furta "Suraj.." "Kaee Raj dae.." Ayrah dake baya ta fad'a tana waro idanun ta, dukkan su murmurshi suka yi kafin Abba ya sake cewa "Mahaefin ka fa?" "Kabeeru" jinjina kae Abba yayi sannan yace "Baka zuwa makaranta ne?" se a lokacin ya d'ago kae ya kalli Abban sannan ya maeda kan nasa k'asa yace "Ehh" d'an shiru Abba yayi yana tunanin tambayar da zata fito daga bakin sa haka dae ya cije yace "Suraj meyasa baka zuwa makaranta?" "Abba Raj ne fa" Ayrah ta sake fad'a, girgiza kae Abba yayi da d'an murmurshi akan fuskar sa kafin yace "Toh shikenan Raj" Yah Sadeeq dake gefen ta shima murmurshin yayi yana girgiza kae "Abbu bashi da kud'in saka ni.." "Shikenan kawae, idan nace zan saka ka zaka ji dad'i?" da sauri ya d'ago kae ya sake kallan Abban, ya lumshe idanun sa yana jin dad'i har besan sanda ya jinjina kae ba murmurshi na wanzuwa a kyakykyawar fuskar sa ba, Abba ma yayi murmurshi yace "Ka fad'a wa Abban naka idan yana da lokaci ya same ni a gida akwae maganar da zamu yi.." amsawa yayi da "Toh angode, Allah ya saka da alkhaeri" "Ameen" Abba ya fad'a yana sake yabawa da hankalin yaron, be bar cikin motar ba seda Abban ya bashi number sa yace ya kaewa Abban nasa ya kira shi.. (_A gurguje zanyi wajen nan pls, saboda idan nace zan ja nan d'in da nisa gaskiya zamu dad'e ne bamu matsa gaba ba, so shys nayi deciding kawae nayi briefing wajen amma yadda zaku fahimta_) ... Sanda Raj ya jewa da Iyayen sa maganar Abban sosae suka yi mamaki, dan da farko ma daya fad'awa Ummeen sa cewar mutumin yace ze sanya shi a makaranta bata yarda ba k'aryatawa tayi kuma ta rufe shi da fad'a dan lokacin ma tun safe babu abinda suka ci kuma har zuwa lokacin Abbun nasa be dawo ba, dama shine me fafutuka ya fita yayi er buga buga ya samo musu abinda zasu ci amma takamaemae bashi da tsayayyiyar sana'a, shiyasa idan ya fita ma ya samo wani abun gaba d'aya suna amfani dashi ne wajen samun abinda zasu ci "Toh hayaniyar me nake ji kuma da rana tsakar nan" maganar da taji daga tsakar gidan ne ya sanya ta dakatawa daga fad'an da take wa Raj, Malam Kabeeru ya k'araso hannun sa d'auke da wata leda, seta k'arasa ta kar6a tana fad'in "Sannu da zuwa Abbu" "Yawwah sannun ka dae" ya fad'a yana kallan Raj dake fad'in "Abbu sannu da zuwa" amsa sannu da zuwan yayi kafin yaja kujera er tsuguno ya zauna a tsakar gidan yana sauke numfashi "Meya faru ne kike ta fad'a tun daga soro nake jiyo muryar ki?" "Gashi nan yaron nan yazo min da wani zance wae wani mutumi yace ze sanya shi makaranta wae kuma ya bashi number sa ka ganta ma yace wae kaema kaje yana neman ka" ta fad'a tana mik'a masa wata takadda dake d'auke da number Abban, kallan su su duka Abbu yayi cikin mamaki, se kuma ya tsaeda idanun sa akan Raj yace "A'ina ya san ka?" d'an shiru kad'an yayi sannan yace bayan ya d'auke kae "A makarantar da nake zuwa" jinjina kae Abbu yayi yana mamakin yadda d'an nasa kullum burin sa shine yayi karatu amma shi kam ya rasa yadda zeyi ya cika masa wannan burin nasa, shi kansa sa yana sa kud'i zeyi k'ok'ari wajen cikawa d'an nasa buri ne ta hanyar kae shi wata k'asar ma ba Nigeria ba yayi karatu "Kuma ka tabbatar da gaske kake?" Abbu yayi k'arfin halin fad'in hakan duk da shi shaida ne akan d'an nasa duk da k'arancin shekaru irin nasa amma da wuya yayi k'arya a cikin lamarin sa "Ehh Abba Allah kuwa da gaske nake" "Ikon Allah" Abbu ya fad'a yana jinjina kae, Ummee tace "Toh zaka je d'in?" kallan ta Abbu yayi kana yace "Me ze hana, kika sani ko alkhaeri ke kiran mu?" "Toh Allah yasa, bari na tashi na d'ora mana shinkafar can mu samu mu ci" Ummee ta fad'a tana mik'ewa. Washe gari da wuri Abbu ya shirya tare shi da Raj, ya kira Abba da er k'aramar wayar sa yayi masa kwatancen gidan nasa sannan suka tafi gidan, daga gidan nasu akwae d'an nisa sosae dan haka suka d'an rage tafiyar a k'asa kafin suka tari adaedaeta ta k'arasa dasu da ragowar chanjin daya ragewa Abbu, a k'ofar gidan suka tsaya Abbu yayi wa Abba flashing a wayar sa saboda kud'in wayar sa daya k'are, ganin kiran nasa ya sanya Abba kawae ya fito dan ya fahimci yazo ne, suka gaesa cikin mutuntawa sannan kowannen su ya gabatar da kansa ga d'an uwan sa, tun a lokacin Abba yaji Abbun ya kwanta masa dan kana ganin sa kaga mutumin kirki gashi ko had'a idanu da Abban ya kasa yi, magana ta k'arshe data wakana a tsakanin su shine Abba yace bayan yaji yadda rayuwar su ke kasancewa, se yayi buga buga yake samu suci abinci, wani lokacin idan be samu komae ba haka zasu wuni da yunwa, shi gashi ba karatu yayi ba dududu iya secondary school ya tsaya, sana'a kuma ta k'i shi, shiyasa ma har lokaci be saka Raj a makaranta ba, saboda komae suka samu cikin su ne, kuma gashi Raj d'in ya tashi da k'aunar makaranta a ransa shi kuma be san yadda zeyi ya saka shi ba, dan idan yace ze saka shin zasu matuk'ar takura ne "Allah sarki, kar ka damu In Sha Allah kamar an saka Suraj a makaranta ne an gama, maganar sana'a kuma dama inaso na bud'e wani shago ne a cikin satin nan, toh idan zaka iya seka dinga zuwa muna zama tare ina sallamar ka" daga inda Abbu ke zaune kan wata kujera ya zamo kamar ze tsugunna yace muryar sa na rawa "Nagode sosae Alhaji, Allah ya saka da alkhaeri, ya biya buk'ata, yasa ka gama da duniya lafiya, nagode nagode sosae Alhaji" "Ya isa haka, babu komae Allah ya taemake mu.." Abba ya fad'a yana rik'o Abban, seya mik'e ya koma ya zauna dae_dae lokacin da Abba ke fad'in "In Sha Allah zuwa gobe se kazo mu fara shirye shirye.." "Toh Alhaji babu damuwa" ya fad'a yana cigaba da kwararowa Abban addu'a cikin matuk'ar farin ciki da jin dad'i. Sanda ya koma gida ya fad'awa matar sa zancen tayi matuk'ar farin ciki, haka suka had'u suka dinga yiwa Abba addu'o'i kala kala. Shima Abban daya jewa Umma da maganar taji dad'i sosae ta kuma yi addu'ar

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70