Chapter 24
Chapter 24
halin fad'in "Kee.. Akwae mummuna ne a cikin mu? Ko kuma dae ke kin sare, idan kin sare ne just tell us kinga yanzu yak'in ya rage tsakani na da Jidda" Bahijja ta ta6e baki kawae ba tare da tace komae ba, Jidda tace "Idan baki janye ba toh zamu ware rana ne muje duk cikin dabara mu isar da sirrin dake zuciyoyin mu" da sauri Bahijja ta kalle su, kallan nan irin na baku da hankali wanda bata san tayi musu shi d'in ba seda taga suna bin ta da kallan tuhuma sannan tayi k'ok'arin saeta kan ta..... Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 015_016 ___"Bahijja!" Ruks ta fad'a tana sake kallan ta sosae, seta gyara zaman ta sannan tace bayan ta saki wani murmurshin yak'e "Na'am, ehh haka ya kamata muyi kam.." daga haka basu sake cewa komae ba suka yi shiru se dae kowa da abinda yake sak'awa a cikin ransa. A hankali ta k'arasa bakin gadon ta chanja hijab d'in jikin ta da wani sannan ta kalle su su duka tace har lokacin fuskar ta ba yabo ba fallasa "Zan d'an je na dawo" ta fad'a tana shirin ficewa daga d'akin, mik'ewa Jidda tayi tace bayan ta d'auki mayafin ta "Muje na raka ki.." kamar tace ta barshi se kuma taga kamar hakan be dace ba dan haka seta dakata ta jira Jiddan har ta k'araso inda take suka fita tare. Ba laefi yanzu suna tafiyar suna d'an ta6a hira, hirar da se Jidda ta d'auko ta sannan Ayrah kan amsa mata har zuwa sanda Jiddan tace "Ina zamu je wae?" "Mango zan siyo.." harara Jidda ta jefa mata sannan tace "Amma shine baki fad'a min ba, toh ae mun wuce wajen masu siyarwar" "Aou mantawa nayi" ta fad'a tana dariya gami da sanya hannun ta akan bakin ta, daga haka suka juya Jidda ta kae su wajen da masu saeda fruits suke sosae, kae tsaye wajen me mango d'in suka je, Ayrah ta fad'a masa adadin data ke so, shi kuma ya fara zuba mata cikin leda. A hankali wata bak'ar had'ad'd'iyar mota ta gangara ta tsaya kusa da me siyar da mangon, su biyu ne cikin motar Rk zaune a wajen me zaman banza yana danna waya, yayin da Yaseer ke driving, kallan sa yayi sanda yaga yayi parking motar a wani waje daban, da mamaki yace "A'ah meye haka?" Yaseer yace "Fruit zan d'an siya, sun min kyau gaskiya.." "Oh god, ji wani kuma" Rk ya fad'a yana watsa masa harara, Yaseer yace "5 min pls.." ya fad'a sanda yake bud'e motar yana kuma d'aga hannun sa, Rk bece komae ba se d'aga kafad'a da yayi gami da ta6e baki lokaci d'aya yana maeda kansa kan wayar sa, wajen minti 2 da fitar Yaseer d'in, a hankali ya d'aga manyan idanun sa ya kalli wajen, acan ya hango shi tsaye wajen me siyar da mango yana ta zuba shi da me mangoron, seya samu kansa da jan tsaki gami da furta "Yaseer!!" ya fad'a yana shirin d'auke kansa idanun sa suka sauka akan fuskar ta sanda wani sassanya kuma kyakykyawan murmushi yake tashi akan fuskar ta wanda ya matuk'ar k'awata kuma ya sake fito da aenahin kyawun ta, cikin en sekonnin da basu wuce 2 ba yaji yanayin bugun zuciyar sa ya sauya wanda har be san sanda ya rintse idanun sa ba yana sanya hannun sa saetin zuciyar sa, seya maeda kansa jikin kujera yana sake lumshe idanun sa kafin a hankali ya fesar da wata iska daga bakin sa "What happen to me?" he asked him self still dae idanun sa suna a lumshe haka zalika hannun sa dafe da k'irjin sa, yafi minti 2 a haka kafin bugun numfashin sa ya fara komawa dae_dae, dae_dae lokacin kuma da Yaseer ya bud'e murfin motar ya shigo, da mamaki ya kalli Rk da har lokacin be bud'e idanun sa ba yace "Rk.. Lafiya?" se a lokacin ya shiga bud'e idanun sa dake d'auke da dogayen bak'in gashin idanu masu matuk'ar kyau sannan ya sauke su kan Yaseer yace muryar sa a d'an ciki "Babu komae.." "Sure?" seya jinjina masa kae kawae yana sake lumshe ido, shi kansa ba zece ga dalilin da yasa yaji bugun zuciyar sa ya chanja tafarar d'aya ba "Ohk.." Yaseer ya fad'a yana kunna motar ya fara driving, seda suka yi nisa da fara tafiyar sannan Yaseer ya kalli Rk kana ya maeda duban sa kan titi yace "Ina tunanin gobe zan koma Kano fa.." "Saboda?" Rk ya fad'a bayan ya d'an kalle shi "Madam ta matsa wallahi, ni kuma bansan 6acin ran ta, so dole na koma a goben gaskiya" murmushi Rk yayi wanda ya sake fito da aenahin kyansa kana yace bayan yaja k'aramin tsaki "Idan ba kayi haka ba ae bazan gane kae ne ba" "Me kuma nayi?" Yaseer ya fad'a yana dariya, shiru Rk ya masa dan yasan dama da biyu yayi maganar "Mutumi na kae ma ka daure kayi auren nan wallahi.." kafin ya kae ga k'arasawa Rk yace "Bismilllahi.., pls wae kae baka gajiya da zancen nan ne? Ka dae san bazan k'ara shekarun da nayi a baya ba tare da nayi aure ba koh?" "Yawwah mutumi na yanzu kace dae na fara shiri kenan?" Yaseer ya fad'a duk da yayi mamakin jin zancen Rk d'in "Kamar haka kake so na fad'a koh? Toh ae gashi nan na fad'a maka" Rk yayi maganar cikin basarwa, tsaki Yaseer ya ja yana fad'in k'asa_k'asa "Ae seka yi ta zama" duk da ya ji shi amma bece masa komae ba ya cigaba da danna wayar sa.. .... Da sallama ya shiga cikin parlourn, Mummy dake zaune kan kujera ta taso tana fad'in "Sannu da zuwa likita, ka dawo lafiya?" murmushi yayi kana yace "Lafiya k'alau Mummy, Daddy fa?" "Be shigo ba tukunnah" seya jinjina kae kawae, can ya jiyo Mummyn na fad'in "Ka dad'e da shigowa ne?" d'an ta6e baki yayi kana yace bayan ya girgiza kae "Nop, ban wuce 1 hour ba.." "Ohk bari Muneerat ta kawo maka abinci yanzun nan" seya d'an yi shiru kad'an, baya son Mummyn ta dinga had'a harkar sa da yarinyar ballantana har suyi tunanin wani abun, se dae 'ya 'ya ce, ko yaya ya nuna baya son hakan yasan ba zata ji dad'i ba, so ko dan kulawar Mummyn a gare shi ya sanya ya dinga d'auke kae akan wasu abubuwan, dan haka bece komae ba ya wuce dinning area, ya ja kujera ya zauna bayan ya ciro wayar sa daga cikin aljihu ya fara dannawa. Wajen mintuna 10 da zaman nasa, wata madaedaeciyar budurwa er kimanin shekaru 22 ta fito daga cikin kitchen sanye cikin riga da skirt na atamfa wanda suka yi cif cif a jikin ta, se dae kasancewar haka take a tsaye yasa kayan basu wani mata kyau ba sun dae yi mata cas cas kamar a jikin ta aka d'inka, daga fuska babu laefi tana da nata kyan dae_dae misali, bak'a ce se dae ba can ba, amma saboda man da take shafawa yasa fuskar ta ta ta fito tayi haske sosae kuma take wani irin shek'i, sannan kuma doguwa ce babu laefi, kan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70