Chapter 29
Chapter 29
Raj d'ina ne kae?" ta sake tambaya dan har lokacin tana tantama ne, musamman yadda tasan Raj d'in ta basu da hali, amma wannan tana ganin sa ne mutum me kud'i, a yadda ma taji ana kiran sa kamar likita ne in dae ba tayi mistake ba, idanun sa ya kashe mata wanda hakan ya sanya ta saurin kauda nata idon tana jin wani irin bak'on al'amari da tunda take bata ta6a jin sa akan kowanne d'a namiji ba, yanayin da take ji a yanzun wanda ke tafiya da dukkan wani bugun numfashin ta "Raj Kabeer" yayi maganar yana mik'ewa ya zauna gefen ta dan ya sake tabbatar mata da shi d'in ne ba wani ba, a hankali ta sake lumshe idanun ta tana jin wani irin dad'i na cigaba da ratsa ta, ita kam yau wace irin rana ce me muhimmaci a wajen ta? Wace irin ranar farin ciki ce a gare ta wadda a cikin ta taga Raj, yau gata ga Raj d'in ta bayan tsawon wasu shekaru? "Meyasa baku sake zuwa gidan mu ba?" tayi maganar tana langa6ar da kae gami da kallan sa, se dae a wannan karon bata kalli k'wayar idanun sa ba, kafin ya kae ga cewa komae me Cafe d'in yayi sallama ya shigo wajen, da mamaki ya kalli Rk dake zaune kujera d'aya da wata 'ya mace, abin ya matuk'ar bashi mamaki har hakan seda ya bayyana akan fuskar sa amma ya maaze yace "Doctor!!" dukan su suka kalle shi dan sam basu san da shigowar sa ba saboda yadda suka shagala da son jin abubuwa da dama daga kowannen su "Pls jira ni a waje!!" Rk ya fad'a bayan ya d'an kalli Mutumin, cike da mamakin dae ya furta "Ohk.." sannan yayi waje ya nemi waje ya zauna har lokacin yana cigaba da mamakin Rk d'in, kamar bashi ba.. "Bansani ba, nima bansan dalili ba" yayi maganar a ransa yana zurfafa tunani ko ze gano dalilin da yasa basu je gidan su Ayrahn ba amma ya kaasa, ita tunda ta gano shine Raj duk wannan tsoron nasa da take ji se taji kamar ya tafi, gaba d'aya ma ta manta shi a matsayin Rk kawae tana masa kallan Raj ne "Kullum ina tunanin ka, amma baka ta6a zuwa waje na ba" tayi maganar kamar zata saka kuka, d'an shiru yayi yana cigaba da kallan ta sannan yace bayan ya lumshe idanun sa "Ban san a ina zan same ki ba Ayrah, ki min uzuri pls.." yana gama maganar aka shiga kiran sallah a masallaci, dan haka dukan su suka yi shiru har zuwa sanda aka idar da kiran Sallahr sannan suka mik'e kusan a tare, Rk ya kalle ta sannan ya mik'a mata wayar sa daya fito da ita daga cikin aljihu yace "Samun contact naki" babu musu ta kar6i tsaleliyar tsadaddiyar wayar tasa ta sanya number ta a ciki sannan ta mik'a masa a ranta tana jin farin ciki mara misaltuwa, daga yanayin yadda ta fahimta abubuwa da dama sun chanjawa Raj d'in nata, kamar bashi ne Raj d'in da ba, kamar an chanja shi ne da wani sabo, ko da yake ba abin mamaki bane komae ikon Allah ne, da farko sune a sama yanzu kuma Raj d'in se dae ma shi ya taemaki wasu ba dae a taemaka masa ba, babu abinda Allah baya iya yi, yadda tayi shiru kamar me tunani ya bashi damar cigaba da k'arewa kyakykyawar fuskar ta kallo yana cigaba da karanto abubuwa da dama "Muje koh?" yayi maganar a hankali kamar me rad'a, seta d'aga kae ta kalle shi kana ta lumshe idanun ta a lokaci guda tana bud'e su, itace ta fara yin gaba sannan yabi bayan ta har suka fito, me Cafe d'in nan ya mik'e yana kallan sa yace "Doctor zaka wuce ne?" "Yeah" ya fad'a a gajarce "Tohm shikenan, Allah ya tsare" ya fad'a yana d'an satar kallan Ayrah yana so yaga wace me sa'ar ce wannan da Doctor d'in da kan sa yake kula ta "Ameen" ya fad'a yana wucewa zuwa wajen motar sa Ayrah na binsa har zuwa sanda ya bud'e murfin gaba sannan ya juyo ya kalle ta, se yaga a yanzu da suka fito haske sosae ma kamar tafi kyau, d'an guntun murmushi ya wanzu a gefen bakin sa sannan yace "I will call u Uhmm?" ya k'arashe maganar yana rufe idanun sa kad'an sannan ya bud'e, jinjina kae tayi ba tare da tace komae ba, haka kawae take jin babu dad'i har cikin ran ta, ji take ina ma su kasance a haka har abada, gefe guda kuma tana ganin kamar idan ya tafi d'in za'a sake maemaeta wancan karon, wato baze sake dawowa ba se bayan wasu shekaru, ko kuma yana matsawa daga wajen zata farka ne daga bacci taga duk abinda ya faru d'in mafarki ne ba gaske ba, haka dae ta kawar da duk wad'annan kawae ta jinjina masa kae sanda yake shigewa cikin motar, ta cigaba da tsayuwa har zuwa sanda yaja motar ya bar wajen yana cigaba da kallan ta, itama shi d'in take kalla. A hankali ta sauke wata ajiyar zuciya sanda ya 6acewa ganin ta, seta shiga jan k'afar ta data mata wani nauyi ta shiga takawa tana cigaba da tunanin Raj d'in, tana tuna Raj d'in da daga farko take masa kallan mutum mara kirki, mugu kuma mara tausayi, mutumin da mazan ajin su kaff ba taga wanda baya tsoron sa ba ballantana kuma akae ga mata, matan dake rububin sa kamar me, se gashi a rana d'aya a kuma lokaci d'aya hakan ya juye zuwa wani sabon al'amari, daga yadda zuciyar ta ke cigaba da harbawa tana tunanin Rk d'in ta fahimci akwae wani gagarumin abu, se dae ta gaza gane menene shi?. Cikin farin cikin daya gaza 6oyuwa akan fuskar ta ta shiga d'akin nasu, dukkan su suka bita da kallo, sabon abu ne da ba kasafae suka saba ganin sa akan fuskar ta ba, abu ne ma da zasu iya cewa in dae ba da Yah Sadeeq, Umman ta ko Abban ta take waya ba basa ganin irin wannan annurin akan fuskar ta, se dae na yau ma ya shallake wad'ancan d'in, dan kuwa tana shigowa ta jefar da Handout d'in hannun ta sannan ta kwanta akan gado tana sakin wani k'awataccen murmushi gami da lumshe idanu, da mamaki Jidda da Ruks suka kalli junan su, se kuma cikin k'arfin hali Ruks ta furta "Ayrah lafiya kuwa?" da sauri ta bud'e idanun ta dan gaba d'aya ma ta manta ba ita kad'ae ce cikin d'akin ba "Eh. Ehh" ta fad'a tana mik'ewa zuwa toilet, suka sake bin ta da kallo sanda ta shige toilet d'in "Ikon Allah" suka had'a baki wajen fad'ar hakan, babu dad'ewa ta fito, Jidda ta dube ta tace "Ga mangoron ki nan cikin leda" "Bash shi kawae, zuwa da safe zan sha" tayi maganar tana janyo hijab dan gabatar da Sallah "Toh lallae akwae damuwa" Jidda ta fad'a tana bin ta da kallo sanda take k'ok'arin tada Sallahr.. Wajen k'arfe 9pm ne na daren ranar tana kwance kan gadon ta, tun d'azu take expecting kiran sa amma kuma tana fatan kafin ya kira ace su Jidda sunyi bacci, se
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70