Chapter 23
Chapter 23
da suka ida rikita ta, ta sake jin zuciyar ta ta buga da k'arfin da yafi na d'azu, a hankali ya janye nasa idanun fuskar sa ba yabo ba fallasa ya sake fad'in "Fita!" yanzun kam ta tabbatar da ita yake, dan haka jiki a matuk'ar sanyaye taja k'afafun ta ta fice daga cikin ajin, tana jin yadda idanun en ajin suka mata chaaa aka wanda har hakan ya jawo tafiyar ta ta sake chanjawa tana tafiya tana wani rangaji kamar er maye, tun kafin ta ida fitowa daga cikin ajin wani kuka ya k'wace mata, dan haka ita tama manta da wannan mutumin dake jiran ta kawae ta wuce Hostel, akan gadon ta ta zube tana fashewa da kuka, ta san mutumin be santa ba bata san shi ba ba dan haka ba se tace tsanar ta yayi shiyasa yake korar ta kullum, ban da haka meyasa wani ya shiga kafin ita be kore shi ba se ita, wayar ta data ajiye akan gadon dama bata tafi da ita class ba ce ta fara ringing seta janyo wayar ta d'aga tana k'ok'arin tsayar da kukan "Subhanallahi Auta meya faru? Har yanzu baki dena kukan ba?" Yah Sadeeq ya fad'a, seta sake hasaso fuskar Rk cikin idanun ta kana ta harari iska tana murgud'a baki sannan tace "Toh ba wani malami bane, Yah Sadeeq wallahi mugu ne kuma.." "Kae Subhanallahi, Ayrah bakya so karatun naki yayi albarka?" "Toh Yah Sadeeq sau biyu fa yana hana ni shiga aji wae na makara" murmushi Yah Sadeeq yayi daga inda yake kafin yace "Toh kiyi hak'uri, kuma kada na sake ji kince bashi da kirki, daga yanzu ki dinga shiryawa da wuri kina tafiya class kin ji?" seta d'aga kae kamar yana kallan ta sannan tace "Ehh" "Dats my sister.." ya fad'a yana murmushi, seda Yah Sadeeq ya ajje wayar sannan tace bayan ta sake tuna fuskar Rk "Mugu kawae.." K'arfe 3 suka fito daga lectures d'in, Jidda, Ruks Bahijja har ma da Ayrah suka fito daga class d'in dan komawa Hostel, suna cikin tafiya kafin su k'arasa Hostel d'in Bahijja ta kalle su tace "Ku wuce pls yanzu zanje na dawo" "Ina zaki je?" Ruks ta fad'a tana kallan ta, seta d'an yamutse fuska kafin tace "Yanzun zan dawo pls, akwae sak'on da zan kar6a wajen wata cousin sister d'i ta data fara zuwa school d'in nan" "Ohk" suka fad'a kusan a tare, suka cigaba da tafiya yayin da ita kuma Bahijja ta juya.. A hankali take takawa zuwa wajen, seta kalli gefe da gefe ganin babu idon wad'anda ke kanta yasa ta wuce wajen, seta dakata a bakin k'ofar office d'in nasa sannan ta kalli wani wanda ke tsaye a wajen tace "Pls Doctor na ciki?" "Yeah.." ya fad'a yana kallan ta "Pls taemaka kamin iso mana" ta fad'a tana maraeraece fuska, seya d'aga kafad'a yana wucewa ciki, wajen minti 2 se gashi ya fito yace "Ki shiga.." murmushi Bahijja tayi cikin jin dad'i kana tace "Nagode sosae.." ta fad'a tana zame takalmin k'afar ta ta shige cikin office d'in, dae_dae lokacin Rk yana tsaye gefen kujerar office d'in, da sallama ta shiga ba tare daya kalle ta ba yace "Come in" seta lumshe idanu tana jin yadda muryar tasa ke k'ara dad'i, ta k'arasa ta zube a k'asa tana fad'in "Sir barka da rana.." kamar be ji ba seda ya nemi waje ya zauna ya bud'e wani littafi sannan yace "Barka..how can i help u?" yayi maganar a had'e "Sir.. Pls zuwa nayi na rok'i alfarma" "Umhum.." yayi maganar har lokacin yana kallan littafin hannun sa, sosae taji dad'in yadda ya amsa matan, dan haka seta gyara zama tace "Sir dama Mama na ce tace a cikin malamae na samu wanda ze d'an dinga taemaka min da abinda bangane ba, shine.. Shine nace bari nazo na kar6i koda contact naka ne, idan ina da buk'atar taemako sena kira ka.." a hankali ya ajje littafin dake hannun sa ya d'aga kyawawan idanun sa ya zube su kan Bahijja, be san sanda ya basu fuska da har irin wannan raenin ze shiga tsakanin su ba, seya kwantar da kansa akan kujera hannayen sa duka biyun ya sark'e su cikin juna kana ya sanya su a ha6ar sa yana d'an juya kujerar daya ke kae, jin shiru ya sanya ta fad'in ba tare data d'ago ta kalle shi ba, dan tasan idan tace zata kalle shin wannan kwarjinin nasa da idanun nan nasa zasu sanya ta kasa fad'ar abinda tayi niyyar fad'a, koma gaba d'aya ta manta abinda zata fad'a d'in "Shine dama abinda ya.." "U shut up bloody fool.." ya fad'a cikin er d'aga murya yana sake watsa mata idanun sa, tuni ta rikice ta d'ago kamar zata yi kuka dan gaba d'aya ya gama rikita ta da wannan razananniyar muryar tasa, bata jira ya sake cewa komae ba ta mik'e jiki na rawa ta fice daga Office d'in, dogon tsaki yaja yana jin wani irin 6acin rae na taso masa, a hankali ya lumshe idanun sa yana sake kwantar da kansa kan kujerar.. Seda ta tsaya ta saeta kan ta sannan ta tura k'ofar d'akin nasu, dukan su suka kalle ta cikin mamakin ganin ta kamar a birkice kuma a firgice "Bahijja lafiya?" Ruks ta fad'a tana kallan ta, se tayi wani yak'e kafin ta nemi waje ta zauna tace "Lafiya mana me kika gani?" "A'ah babu komae" Ruks ta fad'a tana d'an ta6e baki "Dama ke muke jira muna tattaunawa ne akan yadda zamu tunkari Doctor Rk da k'udirin mu, idan yaso seya za6i d'aya duk wadda ya za6a kuma ragowar se suyi hak'uri.." a hankali ta zuro k'afafun ta daga kan gadon da take kae ta kalle su su duka sannan tace "Sam banga amfanin mutum mara kirki ba, wanda be san darajar d'an adam ba, ku kamar ma bakwa ganin abinda yake min" Ayrah ta fad'a dan yau sun gama kae ta bango, kullum cikin zancen sa suke amma sau 2 yana mata d'iban albarka basu ta6a nuna sun gani ba ko sun sani, dukkan su suka kalle ta yadda tayi maganar da alama abin na mata ciwo a rae, Jidda ta dafa cinyar Ayrah tace "K'awa ta mutumin nan fa in dae kabi k'a'idar sa toh zaka zauna lafiya, though dae he is not friendly but he is nice wallahi, baya son hayaniya kamar yadda bashi da hayaniya, daga zarar kin san halin sa fa shikenan babu wata matsala da zata sake faruwa tsakanin ku" ta6e baki Ayrah tayi dan ita dae ba taga inda za'a yabi mutumin ba, kuma ma meye had'in ta dashi da har zata tsaya sanin halin sa? Banda ma dae ita za tayi missing da wallahi ba zata sake zuwa ajin nasa ba in dae tasan shine ze d'auke su, kawae seta mik'e ta shige toilet, Jidda ta dawo da duban ta kan su Ruks tace "Yawwah ya kuke ganin za'ayi?" Bahijja ta ta6e baki "Nifa bana tunanin ze za6i wata a cikin mu wallahi, ina ganin kawae mu hak'ura mu bar abin a ran mu" tayi maganar tana fatan duk su hak'ura d'in su bar ta ita tayi yak'in ta ita kad'ae, shek'ek'e duka suka kalle ta kafin Ruks tayi k'arfin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70