Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

saba ganin sa kamar koda yaushe yana zaune yanzun idanun sa kan wata takadda yana kalla, a hankali ta fara takawa zuwa inda yake zaunen idanun ta a kansa "Ayrah..er carafke fa muma yau zamu yi" wata k'awar ta da itama ba zata wuce sa'ar ta ba ta fad'a da maganar ta me cike da tsamin baki, bata ma jita ba dan gaba d'aya hankalin ta yayi kansa, har zuwa sanda wata a cikin k'awayen nata ta dafa ta tana fad'in "A'ah ki taho enter zamu yi" ta fad'a tana dariya, hannu Ayrah ta saka ta zame hannun k'awar ta ta dake kan kafad'ar ta sannan tace "Ke ni ba zanyi ba.." daga haka tayi gaba, su kuma yaran duk basu bi ta kanta ba suka cigaba da wasan su, seda ta isa inda yake d'in sannan ta tsaya tana cigaba da kallan sa da kuma kayan dake jikin sa, a k'alla zeyi shekaru 12 ne, fari ne sosae kyakykyawa ajin farko, me manyan idanu da dogon hanci, ga wata bak'ar suma dake kwance akansa sedae daga gani kasan bata samun yadda take so dan haka ta d'an cukurkud'e kad'an, kayan jikin sa ma haka kana ganin su kasan sunji jiki amma da alama shi duk wad'annan basu dame shi ba dan kuwa har lokacin idanun sa na kan takaddar hannun sa ne "Kae!!" Ayrah ta fad'a tana kallan sa, da sauri ya d'aga manyan idanun sa ya sauke su akan Ayrahn, bece komae ba seya maeda kansa kan takaddar sa "Kae!!" ta sake fad'a a karo na, d'an lumshe idanun sa yayi sannan ya ninke takaddar a hannun sa ya mik'e, yana k'ok'arin barin wajen Ayrah tace "Kawo na koya maka.." seya d'an dakata kad'an kafin ya juyo yana kallan ta, hannu ta mik'a ta kar6i takaddar hannun sa tana kallan abinda ke ciki, ta karanta da karatun data iya sannan ta kalle shi yadda shima ita d'in yake kalla, seta saka dariya kawae hadda toshe baki kamar wata babba, dama fuskar tasa babu annuri yanzu kuma da yaga tana masa dariya seya sake tsuke ta ya sanya hannu ya kar6i takaddar hannun ta ya juya da nufin barin wajen, hannun ta ta saka ta rik'o nasa hannun, manyan idanun ta sun cika da k'walla tace "Yi hak'uri, gani nayi kae babba ne fa.." ta fad'a abinda take ganin shine ya dace ta fad'a "Allah kuwa idan kana so zan fad'awa Yah Sadeeq ya dinga kowa maka karatu.." seya juyo gaba d'ayan sa yana kallan ta lokaci d'aya murmushi na su6ucewa akan fuskar sa yace "Da gaske?" karo na farko kenan da yayi magana, seta jinjina kae kawae tana d'an murmushi... Ku sani wannan book d'in ina yin sa ne based on experience, zan iya cewa wani abun ma true ne wlh nake had'a muku dashi duk dan labarin ya k'ara armashi kuma ku fahimci sak'on da nake son isarwa, Allah yasa mu dace.. *ZARAH BINT YUSUF (Mhiz Innocent)*✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page_003 ___"Ke Ayrah!!" Yah Sadeeq ya fad'a yana k'arasowa wajen, dukkan su suka d'aga kae suka kalli inda yake, bata motsa daga inda take ba sedae ta cigaba da kallan sa har ya k'araso wajen, ya kalli inda yaron nan ke tsaye na tsawon sakanni sannan ya maeda kan Ayrah, kama hannun ta yayi ba tare da yace komae ba suka bar wajen, yayin da shi kuma ya bisu da ido har suka bar wajen, seda suka isa bakin ajin su sannan ya tsaya ya kalle ta fuskar sa a had'e yace "Meya kae ki can?" rau rau tayi da idanun ta, tana ta6e d'an k'aramin bakin ta kamar zata yi kuka "Ba nace miki ba'a wasa da maza ba?" jinjina kae kawae tayi, yace "Bari na sake ganin ki da wani!" ya fad'a yana sake had'e rae dan ta fahimci da gasken yake "Ya hak'uri Yah Sadeeq.." ta fad'a tana share k'wallar idanun ta, seya d'an yi murmushi kana yace "Yawwah..toh maza ki koma aji.." daga haka ta shige class d'in su shima ya tafi nasu ajin. .. Washe gari ma haka ta sake ganin yaron nan yana lek'e ta window, koda aka fita break seta ajjiye basket d'in ta a cikin ajin sannan ta fita zuwa inda ta ganshi a bayan ajin nasu yau sa6anin da da yake zama a gaban ajin nasu, yana zaune yau ma kamar jiyan yana karanta wata takadda dake hannun sa, seta k'arasa ta zauna tace "Wae kae ba'a saka a makaranta ba?" tayi maganar cike da sakarci, da sauri ya juyo yana kallan ta dan besan da zuwan ta wajen ba maganar ta kawae yaji, ganin ta ya sanya shi sakin ajiyar zuciya sannan ya jinjina kae "Kawo na koya maka toh" ta fad'a tana kallan sa, seya lumshe manyan idanun sa sannan ya mik'a mata takaddar hannun nasa, ta kalla abinda ke cikin takaddar, abinda aka koya musu yau ne seta dinga fad'a masa yadda ta fahimci aekin, shi kuma yana biye mata yana jin abinda take koya masan, kasancewar k'wak'walwar tasu ba d'aya bace kuma karatun su Ayrahn na yara ne yasa cikin k'ank'anin lokaci tana masa yake ganewa, tunda ta fara bece komae ba yayi shiru yana saurarar ta yana kallan ta yadda take maganar duk da ba wani iya magana tayi ba amma yana ganewa, wani abun ne dae sedae idan ta fad'a ya gyara da kanshi, idan ya fahimci bata san yadda zata fad'a ya gane ba, tana ji an kad'a k'ararrawa alamar an koma break seta yarda takaddar hannun ta ta mik'e tana waro idanun ta "Na tafi.." ta fad'a tana shirin wucewa yace "Nagode..ya sunan ki?" seta juyo ta zuba masa manyan idanun ta sannan tace bayan tayi murmushi "Ayrah.." ta fad'a tana juyawa, kamar wadda ta tuno wani abun seta juyo da sauri tace "Kae fa?" murmushi ne ya su6uce a kyakykyawar fuskar sa sannan yace "Suraj..." "Suraj!!" ta maemaeta sunan a la66an ta sannan ta wuce ba tare da ta sake cewa komae ba ta koma ajin su. ... Abba na sauke su a inda ya saba sauke su se suka tafi gida, kamar kullum da sallama suka shiga gidan nasu, Umma na zaune kan dadduma da alama sallah ta idar, tayi musu sannu da zuwa tana rik'e Ayrah data rungume ta "Tashi ki kae basket d'in kitchen.." Umma ta fad'a tana kallan Ayrah "Umma akwae abinci a ciki fa" da mamaki Umma ta kalle ta kana tace "Baki cinye ba?" girgiza kae Ayrah tayi tace "A'ah banci ba fa" mik'ewa Umma tayi rik'e da Ayrahn a hannun ta tace bayan ta zauna "Baki da lafiya ne ko a k'oshe kike?" "Ehh" Ayrahn ta fad'a tana cire hannun ta daga cikin na Umma ta wuce d'aki, Umma ta bita da kallo tana girgiza kae sannan ta dawo dashi ga Sadeeq dake tsaye tace "Meya hana ta cin abincin?" girgiza kae Yah Sadeeq yayi sannan yace "Wallahi Umma bansani ba, kuma amma banga alamar rashin lafiya a tattare da ita ba ballantana ace koh?" "Ehh hakane, may be ko yau a k'oshe take, ko kuma kana so ka koya mata halin ka" Umma ta fad'a tana kallan sa, murmushi Sadeeq yayi yana

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70