Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

wucewa d'aki.. ... Suna zaune a parlourn suna cin abinci, ita a d'an k'aramin plate d'in data saba cin abinci a ciki wanda indae ba'a ciki aka zuba mata ba bata ta6a cin abincin, yayin da Yah Sadeeq ke zaune kan kujera shi kuma yana rubutu a littafi, ita kuma Umma tana zaune kusa da Ayrahn itama tana cin nata abincin a plate, kallo suke a er madaedaeciyar Tvn su, tashar MBC bollywood suke kalla inda suke nuna film d'in Mujhse Dosti Karoge, sosae Ayrah ke kallan duk da ba wani fahimta take ba, daga film d'in hausan har na Indian kawae tana zama ne idanun ta duka akan Tvn amma in za'a tsare ta a tambaye ta ba ganewa take ba "Raj.." taji an fad'a a cikin film d'in, seta sake kallan cikin Tvn sosae, shiru tayi tana tuna sunan wannan d'in nan daya fad'a mata "Suraj.. Raj.." ta fad'a a fili tana saka hannun ta a kumatun ta kamar me tunani "Ayrah.." Umma ta fad'a tana kallan ta, seta kalli Umman kafin Umman ta sake cewa komae tace "Umma irin sunan wani d'an ajin mu.." "Wanne?" Umma ta fad'a tana kallan ta "Raj.." "Anya kuwa?" Umma ta fad'a tana kallan ta, jinjina kae tayi kana tace "Allah kuwa Umma, shima sunan sa Raj" "Toh yayi, k'arasa cin abincin ki" babu musu ta cigaba da cin abincin ta tana yi tana kallan Tvn. ... "Monitor jeka taho min da yaron can.." Uncle Abdoul ya fad'a yana kallan Monitorn ajin su Ayrah, tashi yayi ya fita daga ajin, ya zagaya inda Uncle d'in yake nuna masa, yana zaune gaba d'aya ya gama muzanta haka kuma ya tsorata, yana ganin shikenan daga yau korar sa za'ayi a hana shi shigowa makarantar gaba d'aya, be ta6a tunanin za'a iya ganin sa ba dan yadda yake takatsantsan akan kar wanda ya ganshi, se gashi yau malami da kansa ya ganshi, ya d'an runtse idanu kad'an yana jin kwata kwata babu dad'i "Wae kazo inji Uncle" maganar data sanya shi saurin bud'e idanun sa kenan yana kallan yaron da yazo kiran sa, k'irjin sa na bugawa haka ya mik'e yana jin kamar ya gudu amma beyi hakan ba yabi bayan sa har zuwa cikin ajin, a k'ofar ajin ya tsaya ya kasa yin gaba ko baya har zuwa sanda monitorn ya wuce wajen zaman sa ya zauna "K'araso ciki" Uncle d'in ya fad'a yana kallan Suraj, ya kasa d'aga ido gaba d'aya ya kalli cikin ajin dan yasan idanun kowa na kansa ne "Me yake kawo ka nan?" Uncle Abdoul ya tambaya, kasa cewa komae yayi dan baya jin ze iya fad'in wani abun "Wani abun kake siyarwa?" k'arya bata daga cikin halayen sa amma yau yana ganin gwara yayi tan, dan haka kawae ya jinjina kae "Toh kada ka sake zuwa nan wajen siyar da abu saboda kana d'aukewa wasu hankali, ka tafi can harabar makaranta ka dinga siyarwa.. Ina kayan siyarwar taka?" "Toh.. Suna waje.." ya fad'a a hankali "Tashi kaje toh.." Uncle ya fad'a, da sauri ya mik'e cike da sassarfa ya fice daga ajin, binsa tayi da kallo dan tunda ya shigo take kallan sa har zuwa sanda ya fita d'in.. Ana fita break kuwa ta zagaya inda ya saba zama, yana zaune se dae sa6anin yadda take ganin sa da takadda a hannun sa yanzu ya d'ora kansa akan cinyar sa ne, ta k'arasa ta zauna sannan tace a hankali "Raj.." maganar da yaji ya sanya shi d'aga idanun sa ya kalle ta, seya maeda kansa kawae yayi shiru "Toh na dena kula ka" ta fad'a tana tura d'an k'aramin bakin ta gaba kuma tana shirin mik'ewa, da sauri ya juyo yana kallan ta se tace "Toh me aka maka?" ta fad'a har ranta tana jin ba dad'i na yanayin data ganshi, seya sake d'agowa ya kalli idanun ta da suka yi rau rau kamar za tayi kuka, da sauri ya girgiza kae kafin yace a nutse "Ance kar na sake lek'awa cikin ajin.." "Ya hak'uri" ta fad'a kamar me shirin yin kuka, bece komae ba illah kallan ta kawae da yake yi, ta rufe idanun ta sannan ta bud'e tace "Kawae ka dena lek'awa zan dinga koya maka komae kaga ni babba ce" ta fad'a tana murmushi, shima murmushin yayi sannan yace "Tohm nagode.." "Ae ni babba ce koh?" ta fad'a tana kallan sa, ya sake yin murmushi sannan yace "Ehh sosae ma" "Yeah" ta fad'a tana dariya har da rufe fuskar ta. Tun daga ranar ya kasance kullum taje makaranta idan aka fita break bata cin komae sedae ta tafi wajen Raj ta zauna ta koya masa duk abinda aka koya musu, kuma In Sha Allah kullum ta koma gida se tayi wa Umma zancen Raj, babu ranar banza da za'a tashi a kwanta Umma ba taji maganar Raj a bakin Ayrah ba. Yau ma kamar kullum yana zaune yana jiran ta dan yanzu yama dena lek'e ya hak'ura gaba d'aya, yafi ganewa idan tazo d'in kawae ta koya masa "Raj.." yaji ta fad'a daga inda yake zaune, se yayi murmushi ya juya yana kallan ta dan ba tun yau ba yake fad'a mata sunan sa Suraj ba Raj ba amma ita ta kasa chanjawa kullum da Raj take kiran sa, dan haka yanzun har ya hak'ura ya dena tuna mata idan ta kira shi da Raj d'in kawae amsawa yake yi, tazo ta zauna da littafin ta a hannu, d'ayan hannun nata d'auke da mangoro guda d'aya irin babban nan, ta shiga koya masa abinda aka koya musun, tana yi tana shan mangoron ta cikin nishad'i, yana lura da yadda take sha wani lokacin har da lumshe ido amma yarinta besa ko bismilllah tayi masa ba "Kina san mangoro ne?" yayi maganar yana kallan ta, da sauri ta d'aga kae ta kalle shi sannan ta jinjina kae tana murmushi, shima murmushin yayi sannan yace "Zan dinga tsinko miki a wata bishiya" "Don Allah?" ta fad'a tana kallan sa "Ehh" yace, sannan suka cigaba da karatun su.. ... "Wae Ayrah me yake damun ki ne? Kullum kika fita da abinci sedae ki dawo dashi babu abinda aka ta6a a cikin sa?" Umma ta fad'a tana tsare Ayrah da idanun ta, ba tace komae ba se tura bakin ta da tayi hawaye na taruwa a manyan k'wayar idanun ta "Umma shi fa baya zuwa makaranta, shine nake koya masa" tayi maganar tana kallan Umma "Waye?" Umma ta fad'a da mamaki "Raj!" Ayrah ta fad'a kae tsaye "Oh god" Umma tace tana dafe goshin ta, wae wanene Raj d'in nan ne? Kullum garin Allah se Ayrahn tayi zancen sa "Kikace d'an ajin ku ne kuma?" girgiza kae Ayrah tayi sannan tace "Allah kuwa Umma da gaske nake" murmushi Umma tayi kad'an sannan tace "Toh me yake kawo shi makarantar?" Shiru tayi da alama bata fahimci tambayar Umman ba, sema cewa da tayi "Umma shi nake koyawa karatu fa in an fita break" da mamaki Umma ke kallan Ayrahn, tace har lokacin tana kallan ta "Yaro ne?" girgiza kae tayi tana ta6e baki kana tace "A'ah babba ne." ta fad'a tana kae hannun ta sama kamar me auna tsayin wani "Babba kamar wa?" Umma ta fad'a "Kamar Yah Sadeeq" d'an

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70