Skip to content

Chapter 31

Chapter 31

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

har ta tsinke be d'aga ba, ta sake kira nan ma dae be d'aga ba, a ranta kawae ta bada cewar may be ko bacci yake shiyasa be d'aga ba, duk da dae ta saba kiran sa a irin wannan lokacin kuma ya d'aga amma jiki da jini, k'ilan yau yayi wani aekin ne me wuya yasa yayi bacci da wuri, haka ta koma ta shiga lalubo number Abba.. se wata zuciyar ta zuga ta akan labarin baze musu armashi ta waya ba, kawae seta ajiye wayar tana murmushi a ranta tana sak'a gwara ta bari idan ta koma gida gata gasu Abban ta fad'a musu wannan babban albishir na cewar taga Raj, tasan suma za suyi farin ciki matuk'a k'ilan ma su fita farin cikin ko dan sanin da tayi iyayen nata na son farin cikin ta fiye da nasu.... Mhiz Innocent......✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 021_022 ___Bata dad'e da kwanciyar ba taji wani bacci na sakad'ar ta, se dae har lokacin bata hak'ura ba ta sake juyawa ta kalli inda Bahijja ke zaune tun d'azun, ga mamakin ta a wannan karon ma seta sake ganin ta zaunen dae tana danna waya, bata san sanda wani tsaki ya su6uce mata ba, se kawae ta hak'ura ta lumshe idanun ta amma mamaki ya cika zuciyar ta na Bahijjan, babu 6ata lokaci kuwa wani daddad'an barci me cike mafarkan Rk ya kwashe ta, ba ita ta farka ba se asuba. Yau ma kamar kullum da wuri suka gama shiryawa kasancewar ranar Monday ce, Monday d'in data kasance daga ita seta exam d'in da zasu fara, haka kawae taji tana jin haushin Bahijja amma kuma data tuna za tayi tozali ne da Rk se wani murmushi ya su6uce mata, a wannan karon Jidda ce kawae ta lura da murmushin wanda tun jiya ta lura da sauyawar Ayrahn, ta kasa hak'uri seda ta kalle ta tace "Ayrah wae meya faru naga daga jiya zuwa yau yanayin ki ya chanja?" d'an kallan ta tayi sanda take saka wani littafi cikin jaka sannan ta d'an ta6e baki kamar wadda ta gaji kana tace "Ni fa ba komae nace" "Haka kike ta fad'a tun jiya, Allah yasa haka ne" Jidda ta fad'a tana cigaba da nazarin ta, ba tace komae ba se d'an tura bakin ta da tayi tana k'arasa shirya kayan jakar ta, a ran ta se k'una k'uni take akan takura mata da suka yi tun jiyan. .. Tunda suka zauna jin su kawae take suna hira amma bama ta jin abinda suke cewa ballantana ta fahimta, gaba d'aya hankalin ta ya karkata ne ga son ganin ya shigo cikin ajin, ba'a k'ara minti 1 ba kuwa se gashi ya shigo cikin ajin dae_dae lokacin da ilahirin ajin ya d'auki shiru, lumshe idanun ta tayi tana shak'ar k'amshin sassanyan turaren sa me dad'in gaske sannan ta bud'e tana maeda duban ta kan fuskar sa da taga ta k'ara kyau fiye da jiya, se kawae ta shagala da kallan sa, yau d'in duka ya juye mata ya sake komawa Doctor Rk d'in sa babu fara'a yana yin komae ne cikin tsare gida, yau karon farko taji yanayin da yake d'in ya burge ta, ta san da yana sakin fuska kuma matan da za suce suna son sa se sun fi na yanzu yawa, tana jin sa ya fara magana cikin nutsuwa k'warewa da kuma takatsantsan amma sam bata fahimtar abinda yake fad'a d'in, kawae dae ta san magana yake amma ita bin sa kawae take da kallo kamar wata doluwa tana jin kamar ta had'iye shi amma duk bata san dalili ba, wayar ta dake rik'e a hannun ta ce tayi vibrate daga hannun ta, ta d'an dakata tana jin kamar ta share wayar se kuma tayi k'asa da kan ta ta duba wayar, d'an k'aramin sak'o ya bayyana akan wayar, seta shiga da sauri ta shiga karantawa ganin daga number da yake "Kallan fa?" shine abinda ke rubuce cikin message d'in daga number Rk, a'ah mamaki ne ya kamata har bata san sanda ta d'aga kae ta kalle shi ba, gashi dae anan lecturing d'in sa yake hankali kwance, toh kenan yaushe ya turo mata da message d'in? Toh yaushe ma ya gan ta tana kallan nasa, dan dae tunda ta zauna ba taga idanun sa akan kowa ba ballantana tace ya gan ta, a hankali ta sake maemaeta message d'in, se ta kae hannun ta ta rufe fuskar ta tana murmushi tuna duk kallan data masa ashe yana ganin ta? Lallae shi d'in na musamman ne "Ke meye haka wae?" Bahijja da tun d'azu take lura da duk wani motsin Ayrahn ta fad'a k'asa k'asa, da sauri Ayrah ta kalle ta ba tare da tace komae ba ta d'auke kae "Anya kuwa wannan yarinyar?" Bahijja ta fad'a a k'asan ran ta cike da mamaki, ita dae Ayrah bata sake bi ta kanta ba ta koma maeda hankali kan karatun da yake koya musu, amma duk iya k'ok'arin ta na ganin ta fahimta d'in ta kaasa, se kace wadda aka sanyawa hannu, a haka dae har ya gama lectures d'in baza tace ga abinda ta d'auka ba. ... Sanda suka koma Hostel bata lura da message d'in sa ba har seda ta zauna sannan taga message d'in nasa, da sauri ta shiga message d'in tana jin zuciyar ta na wani d'an bugawa a hankali kamar me jin tsoro "Nan gaba da face mask zan dinga shiga class, idan ba haka ba wataran za'a neme ni a rasa kin cinyewa su Abbu ni" komawa tayi ta kwanta kan gadon ta tana sakin wata dariya gami da rufe fuskar ta, ashe dae duk yana sane da ita duk kallan da take bin sa da shi yana gani, ita kan ta ta rasa gane abinda ya shiga kan ta ta kasa d'auke idanun ta daga kan sa, tana ji kuma kamar idan ta dena kallan sa zata bud'e ido taga baya nan, mik'ewa tayi ta fita daga cikin d'akin dan lokacin duk su Jidda suna ciki, suka bita da kallo kowacce da abinda take sak'awa a ran ta, amma abinda yafi damun kowaccen su shine chanjawar ta ta cikin lokaci k'ank'ani. .. Gyara zaman sa yayi kan kujerar da yake zaune kana a hankali ya furta "Kin wuni lafiya?" seta lumshe idanun ta sannan tace "Ehh.." murmushi yayi bayan ya d'an yi jimm kad'an yace "Ina fatan bakya fita daga cikin makarantar nan?" seta d'an bud'e manyan idanun ta kamar tana gaban sa, sosae yadda ta bud'e idanun yayi mata kyau, sannan ta rufe bakin ta tace a hankali "Ta66, ae na yiwa Yah Sadeeq alk'awarin bazan ta6a fita ba" ta fad'a a sakarce, yayi murmushi yana sake gyara zama muryar ta na masa wani irin dad'i yace "Dats my Ayrah" itama murmushin tayi sannan ta dakata sanda yake furta "Next week exam Uhmm?" kamar tana gaban sa ta jinjina kae kawae, shi kuma kamar yaga abinda tayi d'in yace "Idan anyi hutu In Sha Allah zan zo, may be ma har da su Abbu" yayi maganar a nutse, hakan ba k'aramin dad'i ya mata ba tana murmushi tace "Buhh baka bani labarin ba" ta fad'a tana tura

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70