Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

fall cike da tunanin Umman ta, sosae take jin kewar ta musamman a kwanakin nan duk da kullum se sunyi waya, amma ta k'agu ta gan ta "Raj!!" taji an ambata daga bayan ta, wanda kiran sunan ya gama fita ne da bugun zuciyar ta, take a lokaci guda taji bugun zuciyar ta ya sauya, suna ne da zata iya kiran sa da extra ordinary one, sannan kuma tun daga wancan lokacin bata sake jin me irin sunan ba ballantana tayi tsammanin ko suna ne yazo d'aya, "ko dae shine?" ta tambayi kan ta, wannan tambayar data yiwa kanta ya sanya har bata san lokacin data juya da wani irin sauri ba tana wuwwulga kyawawan idanun ta cikin harabar makarantar, dae_dae lokacin data hango wani ya k'arasa shigewa cikin wata hamshak'iyar mota, cikin sakannin da basu wuce 5 ba motar ta bar wajen, ji tayi kamar sun tafi da duk wani kuzari da numfashin ta, ta lumshe idanun ta tana jan numfashin ta a nutse ko zata samu ya dawo dae_dae "Raj!" yanda aka fad'i sunan ya sake dawo mata cikin kwanyar ta, seta sake bud'e idanun ta tana fatan ace taga Raj d'in ta a gaban ta, toh koma dae kunnen ta ne ke mata gizo?..... Mhiz Innocent....... ✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 017_018 ___A hankali ta sauke numfashi tana sake lumshe idanun ta, ganin da tayi ta tsaya ne akan hanya ya sanya ta jan k'afafun ta ta fara takawa zuwa Hostel, da k'yar ta iya k'arasawa cikin d'akin saboda yadda jikin ta yayi wani irin mugun sanyi haka zalika k'irjin ta ya mata wani irin nauyi. Ajiye littafin hannun ta tayi sannan ta haye kan gadon ta taja pillow ta kwanta tana lumshe idanun ta "Raj!" ta sake fad'a akan la66an ta, cikin lokaci k'ank'ani rayuwar su ta baya ta fara dawo mata cikin kwanya kamar wadda ake haskawa, wata irin kewa ta musamman ta shiga ratsa ta, tana jin ina ma ace ta gan shi, ina ma ta sake ganin shi a rayuwar ta ko da sau d'aya ne, ko ina ya shiga? Ina yake? Meyasa bata sakr ganin sa tun wancan lokacin ba? Se yanzu ta tsaya tayi wa kan ta wad'annan tambayoyin wanda ada k'uruciya bata bar ta tayi ba, tabbas Raj d'in wani mutum ne na musamman a rayuwar ta wanda bata tunanin har abada zata ta6a mantawa da shi, koda kuwa bata sake ganin sa ba a kafatanin rayuwar ta, ko idan ta gan shi zata gane shi? Tana zaune a haka kamar me shirya film duk wani abu daya faru a rayuwar su tana k'ok'arin tuna su, duk da wasu abubuwan da dama ta manta saboda yanayin shekarun ta a wancan lokacin har zuwa sanda Bahijja ta shigo cikin d'akin, ta kalle ta yadda take juyi daga wannan 6angaren gadon zuwa wani 6angaren "Lafiya kuwa Ayrah?" seta bud'e ido da sauri yadda ta tsorata dan sam bata san da shigowar Bahijjan ba kawae maganar ta taji, ganin ta ya sanya ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Ehh.. Yanzu kika shigo?" "Ehh yanzun nan" Bahijja ta fad'a tana zame mayafin jikin ta, Ayrah ta koma ta kwanta dan sosae take jin dad'in tunanin da take yi. *** *** *** .. Littafin ta ta d'auka ta sake karantawa sannan ta rufe, Ruks dake kusa da ita tace "Wae Ayrah gaba d'aya littafin kike k'ok'arin karancewa ne? Test ce fa ba exam ba" ta fad'a dan tun jiya data farka cikin dare taga Ayrahn na ta karatu, shiru Ayrahn ta mata har seda ta gama zuba littafan ta cikin jaka sannan tace kamar bata son yin maganar "Ae dae na gama" jinjina kae Ruks tayi sannan tace "Gaskiyane, sannu da k'ok'ari, ni kam dae ina kusa da ke" "Toh" Ayrah ta furta dan ita sam bata da k'yashi a rayuwar ta, bata k'i duk abinda ta karanta kema ta baki ki rubuta ba, se dae abin nata har da rashin wayo da ga6un ta, dan kuwa zata iya bud'e miki paper ta kiyi copying ba abinda ya dame ta, Bahijja dake saka takalmi tace "Wallahi dama ni topic d'in daya gama mana last week kawae na karanta, couz ina da tabbacin a cikin sa zeyi tambaya" dariya Jidda tayi sanda take k'ok'arin ficewa daga d'akin tace "Ashe duk gwara ni ma, cha66.." tayi maganar tana ficewa daga d'akin, suma duk se suka rankaya suka fice daga cikin d'akin zuwa class. Sanda suka je 8 ba tayi ba dan haka sun riga shi zuwa, seda suka je da wajen mintuna 5 sannan yazo, tunda suka shiga ajin ta d'auko littafin ta ta cigaba da dubawa, Ruks da Bahijja sune a gefe da gefen ta yayin da Jidda ke kusa da Ruks, tun ranar data fahimci su zaman baya kamar a jikin su yake seta k'yale su kawae ita take zaman ta a gaba, se dae wani lokacin ne se suma su zauna a gaban, musamman kuma idan za'ayi test se duk su dawo gaban ko dan ta taemaka musu saboda yadda suka fahimci yanda kwanyar ta ke ja. Cikin takun nutsuwa yayi parking motar sa a bakin ajin, a hankali ya saka hannu ya zare bluetooth d'in dake kunnen sa ya ajje shi kan d'aya kujerar sannan ya cigaba da danna wayar sa, seda 8:00 ta buga sannan ya bud'e k'ofar ya fito bayan ya d'auki wasu books dake a back seat, sanye cikin k'ananan kaya kamar koda yaushe, kayan dake matuk'ar yi masa kyau, su sake fito da zalla kuma aenahin kyan sa, cikin nutsuwa ya cigaba da takawa zuwa ajin, kafin ya shiga wad'anda zuwan su kenan suka yi wani irin sauri suka shige ajin dan kada ya riga su shiga, yana shiga kuwa gaba d'aya en ajin suka nutsu "Wow! Kamar ko yaushe dae" taji Ruks dake gefen ta ta fad'a, shiru tayi dan tasan da wanda take, ita kuwa haka kawae take gujewa kallan inda yake, saboda yadda kallan nasa ke yawan haefar mata da fad'uwar gaban data rasa dalilin sa, ita har yanzu dukan su mamaki suke bata idan ta kalli yadda dukkan su suke crushing akan abu d'aya, kuma a gaban juna zasu zauna suna kod'a shi kowacce ta kawo nata point d'in, seta ta6e baki kawae a ranta tana ayyana "Meya shafeni ni?" kafin a fara test d'in abinda be yiwa su Bahijja dad'i ba shine yadda ya tarwatsa kan en ajin ta hanyar bawa monitorn su umarni, cikin lokaci k'ank'ani kowannen su aka tarwatsa shi zuwa wani wajen, sannan ya bada minti 20 kawae kowa yayi submitting test d'in sa duk da uban tambayar da yayi musu, duk da tambayar guda 2 ce amma idan baka nutsu ka fahimce ta ba yanzun nan zaka yi kwa6a, saboda haka daga wajen mutane da dama basu wani tsaya sunyi nazari ba kawae suka shiga amsa ta, se kuma wani 6angaren da suka tsaya suka yi nazari sosae akae, cikin su ne hadda Ayrah a ciki wadda seda ta shafe wajen minti 5 tana nazarin questions d'in kafin tayi bismilllah ta fara rubutu cikin k'warewa "Time taken" ya furta a nutse bayan cika mintuna 20 d'in daya bayar, mik'ewa Monitorn nasu

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70