Chapter 50
Chapter 50
mota na tafi.." tayi maganar tana saka hannun ta kan fuskar ta tana goge hawayen dake ta sintiri akan kuncin ta, dakatawa yayi daga inda yake ba tare daya juyo ba har wajen second 20, seda kukan nata ya fara raguwa sannan ya juyo a nutse ta fara takawa zuwa cikin d'akin, har ga Allah ya gaji da jin kukan nan nata, d'aga masa hankali yake yi, kuma babu damar rarrashi kada yaje ta koma zargin sa ko ta hasaso wani abun nan gaba, dan haka yanzu ma be kalle ta ba yaja wata kujera sannan ya janyo abincin ya d'ora akan kujerar kana yace "Ba zaki koma gida a haka ba, dan haka ki tsaya kici abincin kawae" yayi maganar lokacin daya ida bud'e abincin, ya ajje cokali a gefe sannan yaja gefe ya tsaya yana fiddo da wayar sa daga aljihu ya shiga dannawa, seda ta gama sheshshek'ar ta ran ta na cigaba da suya, tasan taemakon ta yayi amma kuma ita bata buk'atar wani abinci dan gaba d'aya hankalin ta da nutsuwar ta sun tafi gida ne, amma kuma daga yadda yayi maganar tasan idan ba taci abincin ba ba mayar da ita zeyi ba dan haka ta k'arasa ta zauna kan gadon kana taja kujerar, ruwa ta fara d'auka ta 6alle murfin robar ta kae bakin ta, se yanzu ta tuna rabon ta da shan ruwa har ta man ta, wata irin k'ishirwa ta taso mata dan haka bata sauke robar ba seda ta shanye shi tass, sannan ta ajje tana sauke ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma jikin ta na d'aukar rawa, lumshe idanu tayi dan gaba d'aya bakin ta babu taste amma yaza tayi? Janyo abincin tayi a hankali ta fara kaewa bakin ta tana 6ata rae, spoon na farko data fara kaewa sega hawaye sharr akan fuskar ta, haka dae ta cigaba da ci lokaci d'aya tana kae d'ayan hannun ta tana d'auke hawayen, daga inda yake yake d'an satar kallan ta gaba d'aya wani tausayin ta yazo ya lullu6e shi, seya maeda wayar cikin aljihu sannan ya k'arasa cikin Office d'in ya fara wani abun, ita sam bata lura dashi ba seda yazo dab da ita hannun sa d'auke da allura, beyi tunanin ta lura da ita ba seda yaga tayi sauri ta koma kan gadon manyan idanun ta da suka yi ja sun sake cika taff da hawaye "Idan kana k'aunar Allah kada kamin allura, naci abincin fa, ka k'yale ni don Allah" ta k'arasa fad'a tana sakin kukan gaba d'aya, lumshe idanu yayi na tsawon sakanni kafin ya bud'e su still dae a kan ta, a hankali ya shiga takawa zuwa bakin gadon, ita kuma tana cigaba da komawa baya tana girgiza kae gami dayin kukan ta kamar wadda aka riga aka yiwa allurar "Oh god" ya furta sanda ya dakata yana d'an murza goshin sa "Wannan wace irin yarinya ce?" ya furta a k'asan ran sa kafin ya sake maeda duban sa kan ta har lokacin dae ba tayi shirun ba "Ina yi miki allurar zan maeda ki gida bayan na baki takaddar ki" yayi maganar a nutse kuma cikin lallashi, ita sam ba fahimtar sa take ba wannan allurar kad'ae data gani ta gama rikita ta dan kuwa zata iya cewa tunda take da girman ta ba'a ta6a mata allura ba, ganin da yayi zata cigaba da 6ata masa lokaci ne ya sanya shi tamke fuskar sa sannan ya hau kan gadon ya zauna kana ya sanya tattausan hannun sa yana k'ok'arin rik'o ta, wani sabon kukan ta sake fashewa dashi tana cigaba da komawa baya, hannu biyu ya saka ya janyo ta gaba d'ayan ta cikin jikin sa, duk da yanda take cigaba da k'ok'arin k'wacewa tana kukan ta hakan be hana shi zagaye ta da d'ayan hannun sa ba sannan ya fara k'ok'arin zame hijab d'in jikin ta, lokaci d'aya bugun zuciyar sa ya k'aru, wani irin kasala na saukar masa, d'an lumshe idanun sa yayi kafin ya bud'e har lokacin yana jin yanda take cigaba da kici kicin k'wace kan ta, be bi ta kan ta ba kawae ya saka hannun nasa ya zame hijab d'in zuwa kan kafad'ar ta, sannan babu 6ata lokaci yayi mata allurar, k'ara ta saka sanda taji tsinin allurar ya shige ta bata san sanda ta ruk'unk'ume shi ba lokaci d'aya gaba d'aya jikin ta ya wani saki, wata k'atuwar ajiyar zuciya ya saki sanda ta ruk'unk'ume shin, idanun sa a lumshe ya sake rik'e ta gam yana sauke taggwan ajiyar zuciya, sun kae wajen minti 1 a hakan har lokacin tana kuka a hankali, se a lokacin ta fara tuna a'ina take kuma a jikin wa take, da sauri ta saka hannun ta ta ture shi sannan ta tashi da sauri k'irjin ta na bugawa, se a lokacin ya bud'e idanun sa da suka sake lumshewa ba tare daya kalle ta ba ya mik'e ya k'arasa ya jefar da allurar cikin dustbin sannan ya juyo ya d'an kalle ta k'asa k'asa "Tashi mu tafi" tun d'azun bata kalle shi ba se yanzu da taji yayi maganar nan da saurin da bata san tana dashi ba ta diro daga kan gadon duk da har yanzun tana d'an jin jiri amma tama manta da hakan, murmushin da tun kafin tasan wanene Abbun Raj rabon ta dayi ya su6uce akan fuskar ta lokaci d'aya kuma tana sake goge fuskar ta, wannan d'an murmushin da tayi seda yasa ya d'an ji sanyi har cikin ran sa, ganin tana k'ok'arin riga shi fita ma ya sanya shi fad'in "Je ki wanke fuskar ki" yayi maganar yana tattara abinda ze fita dasu daga cikin asibitin dan so yake ya chanja mata asibiti idan bata samu sauk'i ba, kamar zata yi musu se kuma kawae ta juya ta fad'a inda taga yayi mata kama da toilet, babu jimawa ta fito tana sake sharce ruwan dake kan fuskar ta, ba tace komae ba haka zalika shima bece komae ba yayi gaba ita kuma tabi bayan sa, seda ya kulle Office d'in sannan ya cigaba da tafiya a nutse, ita kuma tana bin bayan sa, duk haka kurum take jin ta a wani irin takure, d'an jiri jirin da take ji ya sanya tafiyar ta ta ta sake zama very slow, se kuma idan taga ya mata nisa sannan ta saka iya k'arfin ta ta kusa cimmasa, yadda ake d'an satar kallan su ne ya sanya shi sake tattaro girar sama data k'asa ya had'e su waje d'aya, dan haka yawanci mutane se suka shiga hayyacin su, seda ya tsaya a pharmacy ya kar6ar mata magunguna har lokacin tana bayan sa kamar wata munafuka se bin wajen take yi da kallo har zuwa sanda suka fita harabar asibitin, yana shirin bud'e mata k'ofar wajen me zaman banza kamar wanda aka tsikara kuma seya fasa, ya sake kicin kicin da rae dan abinda yake k'ok'arin aekatawa yanzun yasan wata rigimar ce ze kuma 6allowa, seya zagaya ya shiga driver seat ya zauna, ganin da tayi bece da ita komae ba ya sanya itama ta sake had'e ta ta fuskar kana ta bud'e ta shiga, babu 6ata lokaci yaja motar ya fice daga asibitin, sanda suka hau titin seta samu kan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70