Skip to content

Chapter 46

Chapter 46

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

bata a hayyacin ta kamar wadda ta zare, ta tsaya ta k'urawa waje d'aya idanu se kuma hawayen dake sauka akan fuskar ta. Babu dad'ewa aka turo k'ofar d'akin, bata damu dame shigowar ba dan ita wannan sam ba damuwar ta bace, wadda ta shigo ta k'arasa ta ajiye abincin data shigo dashi, duk da ganin abincin data kawo jiya duk suna ajiye bata ce komae ba ta fice daga d'akin tunda dae ta gama aekin ta. .... Wajen k'arfe 1pm aka sake shigowa d'akin, har lokacin dae tana zaune a wajen yanzu kam ko hawayen ma sun gaji da zuba, tayi shiru kawae tana jiran taga yadda Allah zeyi da ita, yanzu wata matar ce ta shigo daban ta kalle ta sannan tace "Baba na kira!" sam bata ji ta ba dan kuwa bata tare da ita, hankalin ta da tunanin ta gaba d'aya suna ta wani wajen ne, ganin da matar tayi kamar bata tare da ita ne ya sanya ta k'arasawa gaban Ayrah ta tsuguna sannan tace "Baba na kiran ki" firgigit ta lumshe idanun ta sannan ta bud'e da sauri lokaci d'aya kuma k'irjin ta na bugawa, seta kalli matar dan har lokacin bata san aenahin abinda ta fad'a d'in ba, seda ta sake maemaetawa sannan kawae ta mik'e tana gyara zaman hijab d'in ta kan doguwar rigar da aka bata ta saka wadda take over size dan kuwa yawo take a cikin ta, lumshe idanun ta tayi bayan ta mik'e d'in sanda taji wani irin jiri na neman kada ta, a hankali ta kama kan ta tana sake rufe idanun ta, a haka dae suka cigaba da tafiya ba dan tana gane inda suke zuwa d'in ba. Cikin wani d'aki me madaedaecin kyau, ehh zamu iya kiran sa madaedaeci musamman idan muka yi duba da gidajen cikin k'auyen, dan kuwa wannan d'in shimfid'e yake da manyan tabarmi masu kyau, da kuma wata k'aramar kujera wadda Me gari ke zaune a kae, sam bata san wad'anda ke cikin d'akin ba dan idanun ta da kan su suke lumshewa ga kan ta daya cigaba da sarawa, Me gari yayi gyaran murya sannan ya fara magana a nutse "Kin yanke hukuncin wanda kika za6a a matsayin mijin ki?" ya jefawa Ayrah tambayar, seda matar nan ta d'an ta6a ta dae_dae lokacin da kan ta ya sake sarawa, a hankali ta sanya k'aramin red lips d'in ta na k'asa cikin bakin ta ta cija tana jin yadda ya bushe musamman saboda ruwan daya dad'e be shiga cikin bakin ba, d'aga ido Alhaji Mato yayi ya kalli inda Ayrah ke zaune, be ta6a tunanin tun yanzu Me gari ze kira su yayi tambayar k'arshe ba, gashi yayi sake saurayin na nan be kae gayi masa komae ba, meya kamata yayi a yanzu? "Ranka ya dad'e ina ganin kawae a bani ita zan maeda ta gidan su!" Alhaji Mato ya fad'a yana kallan Me gari, d'aga kyawawan idanun sa Rk yayi ya sauke su kan Alhaji Mato, kafin a hankali ya saki wani miskilin murmushi, dama seda yayi tunanin hakan zata kasance, shiyasa ya maza yayi wa tufkar hanci, girgiza kae Me gari yayi yana tuna maganar da suka yi da Rk, lallae shima yayi wannan tunanin, ze iya yiwuwa Alhaji Maton be yadda da wannan hukuncin ba ya d'auki Ayrah su tafi wani wajen a d'aura musu aure "Kace kuma ba anan garin iyayen ta suke ba?" cikin in'ina Alhaji Mato yace cike da danasanin abinda ya fad'a d'in "Ehh.. Ehh.. Ranka ya dad'e" jinjina kae Me gari yayi kana yace a nutse "Yanzu ba matar ka bace, shima ba matar sa bace saboda haka baze yiwu a had'a ku ku tafi a haka ba, dan haka kamar yanda muka saba, zan d'aura mata aure da wanda ta za6a, shi seya d'auke ta su koma gidan... Kae sake gwada layin nan muji" Me gari ya k'arasa maganar yana kallan wani dake gefen sa, seya fiddo da waya daga cikin aljihun sa ya sake danna wata number ya kira, kira wajen 3 number daya kira bata shiga ba, ya kalli Me gari yace "Yalla6ae kamar jiyan dae yau ma bata shiga" ya fad'a cike da ladabi, gyaran murya Me gari yayi sannan yace "Babu matsala, zamu yi abinda ya dace.. Cikin su biyun wa kika za6a?" Me gari ya k'are maganar yana kallan Ayrah "Raj!" ta furta ba tare data kalli kowa ba, ba kuma tare data bud'e idanun ta ba, har kuma lokacin hannun ta na dafe da kan ta ne daya cigaba da sara mata, daga inda yake ya lumshe idanun sa yana cigaba da kallan inda take kan ta a k'asa haka zalika idanun ta a rufe "Toh madallah, idan an idar da Sallahr azahar ni da kae na zan d'aura auren nan, Allah yasa albarka" Me gari ya fad'a, huci Alhaji Mato ke fitarwa daga bakin sa zuciyar sa na cigaba da tafarfasa, shi kad'ae yasan abinda ze yiwa Rk, dan ya riga yaci alwashin baze ta6a barin sa yaci bulus ba, baze ta6a k'yale shi ba, baze ta6a rangwanta masa ba. Matar nan ce dae ta kamata ta mata jagora zuwa cikin gidan, a lokacin kawae zubewa tayi akan gadon, daga kukan har hawayen yanzu babu ko d'aya dake fita, kawae ta cigaba da kwanciyar ne cikin rashin sanin abinyi, kuma cikin rashin sanin mafita, se a lokacin ta tsaya tayi tunani, shin wanene wannan mutumin? Meyasa ya sato ta daga gidan su? Meyasa yake son auren ta bayan ita ko sanin sa bata yi ba? Meyasa ya rabo ta da gidan su? Meyasa beje ya nemi auren ta wajen Abban ta ba kamar yanda Addini ya tanadar? Meyasa yake son neman auren ta ta wannan sigar? So take ta tabbatarwa da kan ta amincewa auren Rk da tayi ba kuskure bane amma hakan ya citira, kawae ji take kamar ta tafka wani babban kuskure ne auren sa data amince zata yi, nan take kuma wani tunanin ya fad'o mata "Auren kwangila ne ae, kwangilar ma ta yini d'aya, daga zarar ya sawwak'e miki babu wanda ze san kin aure shi, taemakon ki yayi ba komae ba..." abinda zuciyar ta keta sak'a mata kenan amma har yanzu ta kasa yafewa kan ta, musamman idan ta tuna Abban ta, ta tuna irin amincewar da yayi wa su Raj amma suka ci amanar sa, ta tuna yanda yace ba zata auri Rk d'in ba amma yanzu idan suka ji labarin ta aure shi na yini d'aya fa? "In har kin so baza suji labarin ba" abinda ta sake sak'awa kenan a cikin ran ta, se kawae ta lumshe idanun ta tana sake dafe kan ta da dukkan hannayen ta. ... Har aka idar da Sallah yana cikin masallaci, ya kasa motsawa ko nan da can ne, idanun sa a lumshe suke tunani barkatae na yawo cikin k'wak'walwar sa, tun jiyan nan daya kashe wayar sa be sake kunnawa ba dan baya son a kira shi ko kad'an. K'arfe 2:25 mutanen dake cikin masallacin suka shaeda d'aurin auren RAJ KABEER da AYRAH IBRAHEEM KHALEEL akan sadaki mafi k'ank'anta wato mafi alkhaeri.. Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 032 ___Wani irin sanyi ne ya shiga ratsa

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70