Chapter 66
Chapter 66
kuma ya dakata saboda yanda yaji jikin sa ya sake yin wani mugun sanyi, se kawae yace cikin d'an k'arfin hali "Toh cika ni Madam" se a lokacin ta d'an rage kaefin rungumar data masa, amma duk da haka bata sake shi ba "Is ohk, na kulle ido na, bazan kalle ki ba shikenan?" "Tsakanin ka dawa?" ta fad'a cike da sakarci, duk da yanda rungumar data masa ta shige shi sosae har ta sanyaya duk wata ga6a ta jikin sa hakan be hana shi yin murmushi ba sannan ya furta "Da Allah" ya fad'a yana kulle idanun nasa da gaske, se a lokacin ta sake shi a hankali sannan ta mik'e tana kallan fuskar sa, da gasken idanun sa a rufe yake hakan ne ya sanya ta saurin saka hijab d'in ta har lokacin jikin ta na wani irin rawa dae_dae lokacin da shi kuma ya fice daga band'akin, bin sa tayi da harara kamin tace kamar zata yi kuka "Wannan ae iskanci ne" ta fad'a tana murgud'a baki gami da sake harara kamar yana gaban ta. Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya fito daga toilet d'in ya nemi waje ya zauna idanun sa a kulle har lokacin jikin sa a sanyaye, yana nan zaune ta fito kamar wata munafuka se sussunne kae take, seda ta saci kallan sa sannan ta k'arasa wajen kayan ta ta fidda wata riga kana ta koma toilet d'in ta saka sannan ta fito, babu 6ata lokaci ta tayar da sallah, har lokacin data idar idanun sa na a rufe ne, seta sake kallan sa kafin ta d'auke kae kawae. .. Wajen k'arfe 9pm ne, yana zaune kan kujerar d'akin yayin da take zaune akan gado tayi shiru kamar me tunanin wani abu, so yake ya kawar da wannan bak'untar data shiga tsakanin sa da Ayrahn amma kuma yanzu yana cikin wata matsalar ne yasan ba lallae ta saki jikin ta a yanzu ba kam, amma duk da haka ya gaji da ganin ta shiru haka nan, ba kuma yaso ya tuna mata da maganar da zata 6ata mata rae amma yanzu kuma ya zama dole ya mata d'in in dae yana son zaman lafiya, gwara ya fara gamawa da wannan matsalar kafin yazo yaji da waccan d'in. A hankali ya mik'e ya k'arasa kan gadon gefen ta, ya d'aga kae ya saci kallan ta yadda take zaune kan ta akan gwuiwar ta tayi shiru, hannu ya mik'a a nutse ya kamo tattausan hannun ta cikin nasa, janyewa ta soma yi, shi kuma ya sake rik'e hannun gam lokaci d'aya yana girgiza mata kae fuskar sa a narke, kallan sa tayi kafin ta d'auke kan ta tana jin kamar tayi kuka idan ta tuna wani abun "Ayrah don Allah kiyi hak'uri kin ji? Ki dena fushi da ni haka nan, yana ta6a zuciya ta, kin san yadda nake k'aunar ki, bana son ganin ki cikin damuwa, bansan da wane baki zan yi amfani wajen baki hak'uri ba, amma ni dae don Allah ki yafe min ki dena fushi da ni, ina so ne ki koma asalin Ayrahn ki, me so na, me yawan fara'a a gare ni, wadda bata son gani na cikin damuwa.." ya k'arasa maganar yana lumshe idanu, d'aga narkakkun idanun ta tayi ta kalle shi k'irjin ta na d'an bugawa, se taji tausayin sa ya kamata, ita kan ta zata so ta koma waccan Ayrahn amma bata san yanda zata yi hakan ba "Na dad'e banga murmushin ki ba, pls ki min ko da hakan ze faranta min.." yayi maganar har lokacin muryar sa a k'asa yana d'an murza hannun ta dake cikin nasa, bata san sanda tayi murmushin ba wanda ya taho da wani hawaye, seta saka hannu ta d'auke hawayen tana jan ajiyar zuciya, k'awataccen murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa kana yace "Dats my beauty.." seda ya d'an yi shiru yana tunanin ta inda ze fara mata magana, baya so ya sake 6ata mata mood amma wannan lokacin ne ya dace yayi maganar dan haka yace "Babe kina so ranar lahira na tashi da 6ari d'aya a shanye?" cikin rashin fahimta ta d'aga dara_daran idanun ta ta kalle shi, seda ya lumshe idanun sa saboda yanda yaji kallan nata har cikin jikin sa kana yace bayan ya jinjina kan sa "Kiyi hak'uri inaso naje wajen Muneerah in duba halin da take ciki" ya fad'a yana kallan cikin idanun ta, duk da yanda idanun nasu ke cikin na juna hakan be sanya ta janye nata ba "Muneerah!" ta maemaeta akan la66an ta cike da rashin fahimta "Ya ilahee kasa kada ta d'auka da zafi" ya fad'a cikin zuciyar sa har lokacin yana kallan ta "Matar da aka aura min yau nake nufi" cikin sauri ta fizge hannun ta daga cikin nasa wata k'walla na taruwa cikin manyan fararan idanun ta, ba ita taso kukan ya fito ba kawae seta fara kuka wani irin zafi cikin k'irjin ta, runtse idanun sa yayi yana jin babu dad'i har cikin ran sa, a hankali ya saka hannu ya jata cikin jikin sa, babu musu yanzu kam ta cigaba da rera kukan ta a hankali, seda tayi me isar ta sannan ta koma sauke ajiyar zuciya, se a lokacin ya cigaba da magana "Kiyi hak'uri..." ya fad'a, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyar su daya had'u waje d'aya, ita wani lokacin har mamaki yake bata musamman yadda kalmar hak'uri bata masa wahala a bakin sa kamar ba Rk ba, cikin raunanniyar murya tace "Ka tafi toh" ta fad'a bayan ta tashi daga jikin nasa, shiru yayi yana bin ta da kallo cike da tausayawa "Kin amince naje?" seta jinjina kae tana saka hannu ta d'auke hawayen da suka k'i tsaya mata "I love u.." ya fad'a a nutse da tattausar muryar sa, bata iya cewa komae ba se bugun zuciyar ta daya k'aru, shikenan itama waccan d'in k'ila haka zeje ya fad'a mata yana son ta, wani kukan taji ya sake taho mata, se tayi saurin jan ajiyar zuciya dan bata so kukan ya fito, cigaba yayi da bin ta da kallo kamar me son gano wani abu, yana son watsa ruwa a jikin sa amma baya son ta zargi wani abun a ran ta dan haka kawae ya mik'e ya d'auki wayar sa ya fice daga cikin d'akin jikin sa a matuk'ar sanyaye lokaci d'aya kuma 6acin rae na taso masa daya tuna wannan k'ak'ababben aure da aka lak'aba masa. Bin sa tayi da kallo sanda ya fice daga d'akin zuciyar ta na sake karyewa, bata ta6a tunanin zata ta6a raba Raj ita da wata ba, se gashi k'addara tasa hakan ta faru, a hankali ta lumshe idanun ta tana bawa kukan daya taho mata damar fitowa ko zata samu sassaucin abinda take ji a cikin zuciyar ta. ... Kae tsaye gidan nasa ya wuce har lokacin fuskar sa a cunkushe, sosae yake jin takaecin zuwa gidan da zeyi wajen wata matar, amma haka dae ya cije kawae ya tafi gidan. Gida ne me girma wanda ke d'auke da part 2, nashi da kuma nata, gidan ya ginu ya had'u kuma iya had'uwa, yana parking motar ya sauka, baya son 6ata lokaci dan haka ya d'auki ledar daya shigo da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70