Skip to content

Chapter 64

Chapter 64

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

sa yana sak'a gwara ya bar ta tayi kukan dan yasan kuka dole ne musamman gare ta data shak'u da iyayen ta haka, bugu da k'ari kuma ga wannan maganar da itama ta sake tada mata da hankali. ... A cikin wani k'ayataccen Hotel yayi parking, a nutse ya juya ya kalli inda take kwance kan kujerar tayi shiru kamar me tunani, haka kawae yaji wani tausayin ta ya lullu6e shi, ya lumshe idanu lokaci d'aya wani haushi na taso masa tunawar da yayi yanzu haka akwae auran wata a kan sa "Ayrah!" ya fad'a a nutse kuma cikin tausashshiyar murya, a hankali ta bud'e lumsassun idanun ta ta watsa su a kan sa wanda har seda hakan ya sanya shi lumshe idanun sa, se kuma data ga hakan sannan tayi maza ya janye nata idanun tana iya bakin k'ok'arin ta wajen ganin ta dena ganin laefin sa albarkacin maganar daya fad'awa Abba cewar bashi ita akayi amma har zuwa lokacin ta kasa, ta kuma k'i dena ganin laefin sa, se dae an samu ragin kaso me d'an yawa daga laefin sa data fara gani a farko. "Ki goge idanun ki pls, zamu sauka.." ya fad'a yana mik'a mata handkerchief d'in hannun sa, kamar ba zata kar6a ba se kuma a hankali ta saka hannun ta ta kar6a kana ta goge hawayen da ba dan kan ta suke fitowa ba da kan su kawae suke fitowa. Seda suka k'ara wajen minti 2 a haka sannan ya fita ya bud'e mata k'ofa ta fito kana ya koma ya d'auki kayan ta sannan suka wuce, yana gaba tana bin sa a baya kamar wata mara laka saboda yanda tafiyar ta ta ta k'ara sanyi, be damu da hakan ba ya cigaba da tafiya har zuwa sanda ya gama komae ya kar6i mukulli sannan suka wuce cikin d'akin. Madaedaecin bedroom ne me d'auke da babban gado, wardrobe da kuma mirror da sauran abubuwa dae da aka san bedroom na d'auke da, a hankali ya saci kallan yanda ta tsaya daga k'ofar wajen kamar me tsoron wani abun, bece mata komae ba ya k'arasa ya ajje jakar hannun sa sannan ya dawo cikin d'akin, tana nan dae inda ya bar ta, ya kalle ta bayan ya karyar da kae yace "Don Allah ki shigo ki zauna" ba tace komae ba kuma bata motsa daga inda take ba, a hankali ya sanya hannun sa d'aya saman goshin sa ya murza kana ya juya, wayar sa ya ajje kan k'aramar kujerar d'akin sannan ya soma takawa da niyyar juyawa, kamar jira wayar take ya ajiye ta ta soma ringing, kamar wadda aka tsikara ko kuma ake ja ta sauke idanun ta akan wayar "Muneerah!" taga ya bayyana akan wayar, dama kukan be ishe ta ba dan haka nan take idanun ta suka sake tara k'walla, dawowa yayi da baya dae_dae lokacin da kiran ya katse, ya k'araso ya d'auki wayar yana kallan kiran waye? Ganin me kiran ya sanya shi d'aga kae ya kalli Ayrah dake tsaye yanayin ta ya sake chanjawa daga d'azun, bata iya kallan fuskar sa ba se cigaba da rik'e kukan daya taho mata take yi, idan har bata man ta ba waccan d'in da aka d'aura musu aure ae sunan ta Muneerah, d'an runtse idanun sa yayi kafin ya ajje wayar inda ya d'auka sannan ya k'araso inda take beyi wata wata ba ya saka hannu ya d'aga ta gaba d'ayan ta ya d'auke ta kamar Baby, da sauri ta fara hantsilawa da niyyar sauka amma be sauke ta ba har seda ya k'arasa kan gado ya zauna sannan ya jata zuwa cikin jikin sa, kamar jira take yi kuwa ta saki kukan data kasa rik'ewa "Oh god" ya fad'a yana lumshe idanun sa, meyasa ita kuka baya mata kad'an ne? Yana jin ta sanda take cigaba da kukan, shiru yayi yana cigaba da saurarar ta ko zata yi shiru, da yaga dae bata da niyyar yin shirun seya d'auki hannayen sa duka biyun ya d'ago kan ta dake kwance male_male akan k'irjin sa, ya gaji da jin kukan nan na ta, d'an mitsitsin bakin ta red colour kamar wanda aka sakawa jan baki yabi da kallo yanda take motsa shi, ya d'an sake lumshe idanun sa sannan babu 6ata lokaci ya kama bakin nata cikin bakin sa, lokaci d'aya kukan nata ya tsaya saboda yanda taji bak'on al'amarin da tunda take bata ta6a ji ba, cikin sauri ta bud'e idanun ta a razane k'irjin ta na bugawa jin kukan nata yak'i cigaba da fita, fahimtar abinda ke faruwa ya sanya ta soma janye bakin ta da k'arfi lokaci d'aya kuma tana k'ok'arin tashi daga jikin sa cike da tsoro, sam be kula ta ba sema sake rik'o ta da yayi gam cikin jikin sa ya shiga kissing nata a hankali cike da matsananciyar k'aunar ta, idanun sa a lumshe haka zalika yana sake cigaba da shigar da ita cikin jikin sa, kuma yana cigaba da kokawa da numfashin sa daya soma chanjawa, ya d'auki wajen minti 1 yana kissing nata zuwa lokacin jikin sa ya gama yin sanyi, wani bak'on al'amari ya soma ziyartar gangar jikin sa, yanda ya d'an sassauta rik'e bakin nata ne yasa tayi amfani da wannan damar ta k'wace lips d'in ta tana jin yadda k'irjin ta ya cigaba da bugawa, ajiyar zuciya ya sauke sanda ta cire bakin nata daga cikin nasa har lokacin idanun sa na a lumshe ne, hannu ta saka ta dafe bakin ta da kuma iya k'arfin ta ta soma k'ok'arin mik'ewa tana ajje numfashin dake alamta kuka take mara sauti, se kawae ya sake saka hannu ya jata cikin jikin sa ya mata wata kyakykyawar runguma, hannu ya saka ya soma zame hijab d'in jikin ta har lokacin kuma be sake ta ba kuma yak'i bata damar tashi, girgiza kae ta shiga yi kamin cikin k'arfin hali tace cikin raunatacciyar muryar ta "Ni ka k'yale ni" ta fad'a kamar zata fashe da kuka, be kula ta ba kawae ya k'arasa zame hijab d'in gaba d'aya ya jefar gefe sannan a hankali ya shiga shafa bayan ta kamar yarinyar goye, shi kad'ae yasan yadda bugun zuciyar sa ya k'aru, kawae k'arfin hali yake yi yana jan numfashi a hankali, ga mamakin ta se taji kukan na neman tafiya inda ya fito, se dae bata ji zata iya d'aga ido ta kalle shi ba saboda kunyar abinda ya mata yanzun, shi ko kunya ma baya ji? Seta sake kae hannun ta bakin ta data ke ji kamar yanzu ne yake kissing d'in nata, dan haka ta d'an zabura kad'an kamar wadda aka daka tana shirin mik'ewa k'irjin ta na cigaba da bugawa cike da tsoro, gyara mata kwanciyar daya dake yi shine ya tabbatar mata da ba yanzu ne yake kissing d'in nata ba, duk jikin ta a matuk'ar sanyaye ta hak'ura da k'ok'arin tashin ta koma kawae tayi shiru se dae har lokacin akwae ragowar k'walla manne cikin manyan idanun ta. A hankali kuma taji wani irin bacci na sakad'ar ta, so take ya cika ta ta mik'e amma yak'i sakin ta dan haka kawae ta hak'ura ta bada kae bori ya hau, babu dad'ewa bacci me dad'i ya d'auke ta,

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70