Skip to content

Chapter 36

Chapter 36

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

Abbu ya fad'a yana bud'a hannun sa, Rk ya k'arasa yayi hugging mahaefin nasa sannan yace "Barka da wannan lokacin Abbu" "Barka dae Raj, ka dawo ashe? Mu wuce masallaci dae tukunna" babu 6ata lokaci suka wuce masallacin dake jikin gidan su, ana Sallahr Isha'i Rk ya koma gida saboda yadda yake so ya watsa ruwa a jikin sa yayin da ya bar Abbun a masallaci. Cigaban nan wajen yana page 1, yanzu haka mun ji TUSHEN LABARIN MU dan haka zamu d'ora ne da CIGABAN LABARI.... ... "Shin yanzu kin san wanene Raj d'in da kike magana a kan sa? Waye mahaefin sa? Meya aekatawa rayuwar ku? Mahaefin ku ya amince masa ya bashi amanar da be ta6a bawa wani ba amma daga k'arshe ya wulak'antashi ya tozarta shi yayi wancakali da duk wannan amanar, mahaefin ki ya d'auko shi daga rana ya sanya shi a inuwa amma daya tashi dame ya saka mishi? Seya d'auki mahaefin ki ya jefa shi cikin ranar shi kuma ya cigaba da rayuwar sa ba tare da tunanin halin da zamu iya shiga mu dukan mu ba, Yanzu haka Sadeeq na kwance ne a d'aki sakamakon karayar daya samu ana buk'atar a masa aeki amma babu kud'in aekin, mahaefin Raj ya cuci Abban ku, ya raba shi da dukiyar sa, takaddun sa masu muhimmanci, uwa uba kuma shine silar shigar mu cikin kowanne hali, silar abinda ya aekatawa mahaefin ku ne ya janyo masa hawan jini, ya cuce mu mu kan mu akan son zuciyar sa, ta yaya zan miki wannan bayanin a wancan lokacin ki fahimta? Ina k'wak'walwar ki take ta k'arfin fahimtar wannan zancen?" Umma ta k'arashe maganar tana kallan Ayrah da tunda ta fara maganar ba tace komae ba, idanun ta gaba d'aya Umma suke kalla har lokacin tana cigaba da tuno maganar Umman cikin kunnuwan ta wanda take jin su kamar amsa kuwwa suke mata a kunnen ta, dan kuwa duk da Umman tayi shiru hakan be hana ta cigaba da jiyo sautin muryar Umman a kunnen ta ba, kunnen nata ya mata wani duumm kamar wadda ta kurumce banda sautin muryar Umman babu abinda take ji har yanzun, bata ma sani ba ko Umman ta cigaba da fad'a mata magana ko tayi shiru ne ita dae bata sani ba, abinda kawae ta sani maganganun nan da suka sanya ta cikin sani irin shock da kuma hutun da k'wak'walwar ta ta tafi na wucin gadi su kad'ae keta dawo mata, jikin ta wani irin rawa yake yi kamar me jin sanyi, duk da idanun ta ba'a rufe suke ba amma se take so ta sake bud'e su tarr ko dan ta cigaba da kallan Umman da yanzun take ganin ta dishi dishi, gaba d'aya ta kasa koda bud'e bakin ta ne ballantana ta furta wani abun, koda yake idan ta bud'e d'in ma menene za tace?? Mhiz Innocent......✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 027_028 ___Ganin da Umma tayi har lokacin Ayrah ta gaza furta komae ya sanya ta sanya hannu ta share idanun ta itama da k'wallar ta gama tarar mata, kawae seta juya a hankali ta fice daga d'akin dan ta bar Ayrahn ta dawo daga shock d'in data shiga, ta san dole abin ya ta6a ta aenun, bata ta6a zata ba ba kuma ta ta6a tsammani ba se gashi rana tsaka taji dalilin rabuwar Abba da Abbun Raj. Ko d'aga ido ta kalli Umman ta kasa yi sanda Umman ta fice daga d'akin, ita bama ta lura ta fita ba dan kuwa har zuwa lokacin ta kasa gasgata duk maganganun nan da Umma take fad'a ba mafarki bane "Abbun Raj fa" shine abinda ta dinga maemaetawa a cikin ran ta tana so ta hasaso fuskar sa amma ta kasa dan shekarun nada yawa, ga kuma yanayin shekarun ta a lokacin, amma tabbas idan har bata manta ba mutumin ya zo wa Abban ta a matsayin mutumin kirki, bata san menene ya had'a su ba se gashi yau Umma ta bankad'a mata komae taji dalilin Abba na cewa ba zata auri Raj ba, tabbas in dae kuwa haka ne dalilin Abban yana da gaskiya, a hankali ta shiga sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin zafi a cikin zuciyar ta, sosae zuciyar ta ke zafi wanda har ta numfashin ta seda ya koma fita da zafi, se a lokacin taji wani kuka ya taho mata, bata hana fitowar kukan ba se kawae ta jefar da jikin ta kan gadon ta fashe da wani irin kuka, a hankali take dukan kan ta akan pillown kan gadon tana jin wata iriyar nadama da danasani na lullu6e ta, kunyar abinda ta fad'awa Abba d'azu na sake k'arawa yanayin da take ciki k'aemi, wani irin kuka take wanda ke fitowa daga can k'asan ran ta, kukan nadama, kukan danasani, kukan rashin sanin mafita, a yau d'aya taji tayi danasanin sanin Rk a rayuwar ta, meyasa ma ta san shi? Meyasa tayi silar zuwan sa wajen Abba? Meyasa ta zamo silar da Abba ya janyo mahaefin sa cikin jikin sa? Yanzu kenan itace silar komae? Itace ta janyo komae? Meyasa tayi hakan? Gani take kamar komae ya faru itace me laefi tunda ita ta kawo Rk d'in "Nice silar komae!" ta fad'a sanda take sake sakin wani kukan me cin rae "Tabbas nice sila, dan da ban san Raj ba Abba baze ta6a sanin Abbun sa ba, ni na janyo Abba ya jawo Abbu a jikin sa har me faruwa ta faru, nayi danasanin sanin ka a rayuwa ta Raj!" ta k'arashe maganar tana cigaba da kukan da har muryar ta ta fara dashewa, yau mamaki na neman kashe ta, wae Abbu ne ya cuci Abba, Abbu ne sanadiyyar tarwatsewar farin cikin su, Abbu ne sanadiyyar saka damuwa a zukatan iyayen ta, Abbu ne sanadiyyar abubuwa da dama da suka faru a rayuwar su, shi kam yanzu menene zece musu su yafe masa? A hankali ta sake komawa ta kwanta har lokacin ta kasa tsaeda kukan da take, haka zalika zafin da zuciyar ta yake yak'i raguwa sema k'aruwa da yake yi, ta rasa yadda za tayi, ji take dama zata iya janyo abinda ya faru ada ta goge komae akan alak'ar ta da Rk, da kuma ana iya tariyo baya data hana kan ta had'uwa da Rk, Yah Sadeeq ne ya fad'o mata, se taji wata sabuwar k'walla ta zubo mata, ta sanya hannu ta d'auke ta lokaci d'aya tana lumshe idanun ta, bata da k'arfin da zata iya tashi yanzu haka taje ta duba jikin sa, amma ita kad'ae tasan abinda take ji a cikin jiki rae da kuma zuciyar ta. ... "Don Allah Alhaji kayi hak'uri ka bari ko zuwa gobe ne, kaga ko hutawa ba kayi ba" Muttala ya fad'a yana kallan Alhajin daya fito daga d'akin sa cikin wata bugaggiyar shadda d'inkin babbar riga, juyawa yayi ya kalli Muttala sannan yace har lokacin be tsaya ba "Wallahi bazan iya hak'ura se gobe ba, gwara ma ka k'yale ni kawae" yayi maganar sanda ya isa motar sa, ya bud'e ya shiga sannan ya kalli Muttala yace "Zaka raka ni ne ko kuma in nemi wani?" seya girgiza kae sannan ya k'arasa

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70