Chapter 30
Chapter 30
dae ba taga alama ba dan kuwa hirar su suke kamar yadda suka saba kullum se sunyi ta kamar farilla, se juyi take kawae akan gadon tana tuna kyakykyawar fuskar sa, ada sanda yake a Doctor Rk bata ta6a tsayawa ta k'are masa kallo ba ballantana har ta gano wannan kyan na musamman da matan ajin nasu kan kod'a shi akan sa ba, se yau ta kalle shi ta tabbatar da hakan, ta kuma ga zalla kuma aenahin kyau daga Raj d'in. .. Sanda ya koma gida kae tsaye d'akin sa ya wuce yau ko sashen Mummy be je ba, dan so yake kawae ya gama abinda yake ya kira ta yaji abubuwa da dama daga wajen ta, toilet ya fad'a ya watsa ruwa a jikin sa sannan ya fito ya shirya cikin wata brown d'in had'ad'd'iyar jallabiyya, ya zauna yayi karatun qur'an kamar yadda ya saba sannan yayi addu'o'i ya mik'e daga kan abin sallah, yana shirin ninkewa yaji ana knocking k'afar d'akin, d'an tsaki yaja sam be san wani ya kula da shigowar sa cikin gidan ba, kamar ba zeje ya bud'e ba se kuma ya ajje daddumar kan gado sannan ya fito parlourn ya k'arasa ya bud'e k'ofar, kawae seta sanya kae cikin d'akin ta shigo hannun ta d'auke da warmers d'in abinci guda 2 ta ajje a tsakiyar parlourn, sanye take cikin doguwar rigar shadda wadda tasha aeki ta fito tayi kyau da ita, fuskar nan kamar koda yaushe ta k'ara fari, tsaki ne ya su6uce masa akan bakin sa yana lumshe ido, ya akae tasan ya shigo gidan? "Baby yau baka shigo kaci abinci ba, yasa nace bari na kawo maka d'aki, ina fatan ban yi laefi ba?" tayi maganar tana matsowa kusa dashi, bece komae ba ya k'arasa ya zauna kan kujera sannan yace har lokacin be kalle ta ba "Sannun ki" seta saki murmushi tana dawowa itama ta zauna kan kujera tana shak'ar k'amshin turaren jikin sa daya cakud'e dana sassanyan k'amshin sabulun sa, ko second 5 ba tayi kan kujerar ba ta zame zuwa k'asa tana fad'in "Bari nayi serving naka" shi bema jita ba dan gaba d'aya hankalin sa ya tafi kan Ayrah ne, tunda ya baro makarantar ya kasa dena tuno kyakykyawar fuskar ta, gaba d'aya ta chanja, duk da dama tun tana yarinya kyakykyawa ce amma yanzu ta k'ara wani shahararren kyau kamar ita tayi kan ta, se dae har yanzu halin ta na nan, ga6untar nan da shagwa6ar nan har yanzu babu abinda ya ragu, tilas abinda ya tuna d'in ya sanya shi sakin sassanyan murmushi yana gyara zaman sa kan kujerar da yake, Muneerah data d'aga kae ta kalle shi taga murmushin da yayi, abinda yake da tsada a wajen sa, se gashi yau kusan zata iya cewa babu dalili yayi shi, seta samu kan ta da gyara zaman ta tana murmushi dan ita ta d'auka da ita yake "Yaya Daddy ya maka magana kuwa?" ta katse masa tunanin tana fatan Daddyn ya masa magana kuma ya kar6i zancen hannu bibbiyu, da mamaki ya d'an kalle ta sannan ya d'auke kae "Magana? Anya kuwa!" ya fad'a cikin er basarwa, seta yamutsa fuska sannan tace "Ohk toh ka sauko kaci abincin mana" ta fad'a tana cigaba da satar kallan sa ganin da tayi yanzu babu wannan murmushin akan fuskar ta sa, iska ya furzar daga bakin sa dan shi kam kwata kwata baya jin wata yunwa, toh wata ma yunwa zeji bayan gaba d'aya hankalin sa da tunanin sa na wajen Ayrah ne "Ban jin yunwa fa" ya fad'a yana zuba mata idanun sa, cikin er rawar murya ta furta "Haba mana Baby, pls kaci kada ka kwana da yunwa!" ta fad'a cike da kulawa kamar itace zata kwana da yunwar bashi ba, baya son dogon zance kuma ya k'agu ta fita dan yana jin idan har ta k'ara wasu mintuna bata fita ba toh ze tashi ne ya bar mata d'akin ita d'aya, dan haka ya furta "Ohk.. zaki iya tafiya, se da safe.." kallan sa ta cigaba dayi dan ita kam sam bata gajiya da kallan sa, jin shiru ya sanya shi sake fad'in "Ko na bar miki d'akin ne?" yayi maganar in a serious tune, da sauri ta mik'e sannan tace "Ohk bye luv, kayi bacci lafiya.." ta fad'a tana cigaba da kallan sa, ba tare daya kalle ta ba ya furta "Ohk" ya k'arasa maganar yana janyo wayar sa dake gefen sa, babu yadda ta iya haka ta fice daga d'akin zuciyar ta a cunkushe, ita ta k'agu kawae ayi auren nan kowa ma ya huta. Number ta ta ya lalubo ya danna kira, a 6angaren ta tana kwance kan gadon ta hannun ta rik'e da wayar ta ta tana jiran kiran sa tun d'azun, ganin kira da wata sabuwar number ya sanya ta tashi zaune da sauri tana kallan jerin gwanon numbobin dake shimfid'e reras akan wayar ta ta, kamar yadda yake special haka number sa ma take special, haka kawae taji a jikin ta shi d'in ne dan haka ta sake kallan gadon su Jidda taga duk bacci suke sannan ta d'aga tana karawa a kunnen ta, kafin yace komae tace bayan ta tura bakin ta daga inda take "Se yanzu ma zaka kira?" murmushi yayi daga inda yake yana kishingid'a a inda yake kwance sannan yace "Am sorry.." "Naqi ni dae, Allah kuwa tun d'azu fa nake jira ka kira" wani murmushin ya sake yi mara sauti yana karanto zallahr k'uruciyar dake tattare cikin maganar ta, da alama ko soyayya za'ayi da ita ba zata zama cikin mak'aryata ba, cikin k'asa da murya ya furta "Amin afuwa Uhmm? Raj ne fa" ya fad'a da er tsokana a maganar sa, se tayi murmushi kawae "Ina Umma? ina Abba? Ina Yah Sadeeq?" yayi maganar kamar ba Rk ba, seta sake gyara zama sannan tace "Alhamdulillah kowa lafiya k'alau, ina Abbun ku" "Abbu yana lafiya.." "Raj!" ta fad'a dan ta k'agu ta masa tambayar data tsaya mata arae sosae "Na'am" ya fad'a a nutse "Kae likita ne?" murmushi yayi daga inda yake sannan yace bayan ya d'an lumshe idanun sa kad'an "Yeah! likita ne, ki gyara zama na baki labarin rayuwa ta tun bayan rabuwar mu" kamar tana kusa dashi ta shiga gyara zama, dae_dae lokacin da Bahijja ta farka daga bacci saboda wani fitsari daya matso ta, ta kalli Ayrah dake zaune kan gadon ta sannan ta furta "Ayrah" cike da mamakin ganin ta, da sauri Ayrahn ta juyo tana kallan ta, se dae ba tace komae ba har Bahijjan ta shige toilet d'in, babu dad'ewa ta fito memakon ta nemi waje ta kwanta seta zauna tana cigaba da kallan Ayrah, haushi ya kama Ayrah ta had'e face d'in ta tsaff, sannan cikin had'e ran dae ta furta "Gobe zamu yi wayar" bata jira yace komae ba ta katse wayar sannan ta juya ta kwanta tana jin kamar ta tashi ta rufe Bahijja ta duka, cigaba da zama Bahijjan tayi dan so take ta gane da wanda take waya saboda abu ne da basu ta6a gani ba a wajen Ayrahn tunda tazo ba, kamar wadda aka tsikara ta janyo wayar data wulla gefe ta lalubo number Yah Sadeeq ta danna kira, se dae
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70