Skip to content

Chapter 38

Chapter 38

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

kallan Abban "Kin san wanene yazo neman auren nata?" Abba ya fad'a yana sake tuna fuskar Alhaji Maton, girgiza kae kawae Umma tayi sannan Abba yace "Alhaji Mato!" da mamaki Umma ta cigaba da kallan Abba har wajen second 30 ba tace komae ba se kuma can tace "Alhaji Mato kuma? D'an sa ko kuma shi kan sa?" "Shi dae kae.." Inji Abba "Wae Alhaji Maton dana sani Abban su?" "Ko shakka babu" Abba ya fad'a a gajarce, jinjina kae Umma ta shiga yi tana sake tuna waye Alhaji Mato, neman auren Ayrah yazo yi? Toh a'ina ma ya san ta? "Lallae mutanen duniya babu kunya" "Wallahi kuwa, ya d'auka wani banzan kud'in sa ze rud'e ni ne, in manta wane ne shi, Mutumin da be san k'addara ba, toh na d'auki 'yata kuma na bashi duk abinda ya same shi ae cewa zeyi itace" Abba ya fad'a yana sake jin takaecin Alhaji Maton "Allah ma ya kyauta Abban su" Umma ta fad'a tana sake jinjina wannan al'amari "Kamar fa har yanzu bata daena kuka ba, kije ki rarrashe ta mana" Abba ya fad'a bayan ya sake jiyo sheshshek'ar Ayrah daga cikin d'akin ta, Umma ta girgiza kae kana tace "Bar ta Abban su, bar ta tayi kukan, dole ne dama tayi, babu amfanin rarrashin yanzu dan koma nayi ba denawa za tayi ba, tun d'azun ta kasa furta komae tun bayan dana gama fad'a mata abinda Baban Raj ya aekata mana" "Allah ya kyauta" shine kawae abinda Abba ya fad'a kawae. ... A 6angaren Rk kuwa koda ya mik'e kae tsaye d'akin Abbu ya wuce yana jin yadda kan sa ya masa wani irin nauyi, haka zalika manyan k'wayar idanun nan nasa ta d'an lumshe kamar me jin bacci, ko sallama be iya yi ba ya fad'a cikin d'akin, dukan su suka kalle shi se dae babu wanda ya tanka masa har ya k'araso ya nemi waje ya zauna yana kallan su su duka, ganin basu da niyyar cewa komae ne ya sanya shi d'aga idanun sa da suka d'an lumshe yace "Abbu ko zan iya sanin dalilin ku na cewa bazan auri Ayrah ba?" yayi maganar yana jin zafin ta har cikin ran sa, dan ko maganar ma baya son furta ta dan kawae ya zama dole ne yayi ta dan sanin aenahin abinda ke faruwa, Abbu be kalle shi ba dan haka kawae yake jin kamar idan ya bari suka had'a idanu da Rk d'in nan take ze fahimto rashin gaskiyar dake tattare cikin idanun sa, Ummee tace cikin zafi "Ka tashi ka bamu waje Malam, idan kuma kana so a fad'a maka abinda ya faru ne mutuncin Baban Ayrahn ya zube a wajen ka toh se kayi magana" ta k'arashe maganar tana d'auke kan ta daga kallan sa, da sauri Abbu ya d'aga ido ya kalle ta cikin mamakin jin furucin ta, ita kam tak'i yadda ta kalli kowa dan bata so k'warin gwuiwar data tattaro su tashi a banza, da mamakin dae ya maeda idanun sa kan Ummee sannan murya a cunkushe yace "Mutunci kuma Ummee?" "Ehh mana, toh kasan abinda ya aekatawa mahaefin ka kuwa? Ina tunanin ae baka manta sanda mahaefin ka ke k'ark'ashin mahaefin Ayrah ba koh?" ta fad'a tana tsare shi da idanun ta, be iya cewa komae ba kawae ya cigaba da kallan Ummeen da lumsassun idanun sa, Ummee ta gyara zama tace "Toh duk uban aekin da mahaefin ka keyi masa cewa yake yi ze biya shi k'arshen shekara, amma da yake Abbun ka me hak'uri ne be ta6a nuna gajiyar sa ba koda kuwa a fuska ne, haka mahaefin ka ya duk'ufa yana masa aeki tuk'uru har zuwa sanda k'arshen shekarar tayi, amma kasan me mahaefin nata ya masa daga k'arshe? Guduwa yayi ba tare daya sallami Abbun kud'in aekin wahalar daya dinga masa kwana da kwanaki wata da watanni ba, ina ganin ko dan wannan abun ae yaci ace ka k'auracewa er mutumin daya yaudare ku koh?" Abba ya d'aga kae da sauri ya kalli Ummee da wani irin kallo irin kallan nan na "Meyasa zaki aekata haka?" se ita kuma ta d'auke kae bayan ta jinjina kae har lokacin fuskar ta a had'e, cigaba da kallan ta Rk yayi yana rarrabe maganar data fad'a d'in, shi sam yama kasa gane alk'iblar wannan magana "Amma kaga da yake Allah ba azzalimin bawan sa bane ae gashi nan yanzu mahaefin ka yayi arzik'in da ba'a so yayi" Ummee ta sake fad'a tana kallan Rk, lumshe idanun sa yayi yana cigaba da sauraron bugun zuciyar sa da yanayin fitar sa ya sauya cikin k'ank'anin lokaci, se a lokacin Abbu ya iya bud'e baki dan yin magana, dan shima ya tabbatar idan ba hakan suka yiwa d'an nasu ba baze ta6a hak'ura ya bar zancen ba, kuma yana ganin lokaci yayi da zasu sake yiwa tufkar hanci dan haka yace "Saboda haka ka bud'e kunnen ka da kyau kaji, ni na riga na yafewa Abban Sadeeq amma fa bazan iya had'a alak'a dashi ba.." Abbu ya fad'a yana jin maganar tasa wani banbarakwae da ita, ganin har I zuwa lokacin Rk be bud'e idanun sa ba ya sanya shi fad'in "Dan haka ina me farin cikin sanar da kae na nema maka auren er uwar ka Muneerah.. kuma an baka, yanzu abinda ya rage kawae shine tsaeda lokacin d'aurin aure!" idanun sa ya bud'e da wani irin sauri, wanda saboda jimawar da suka yi a rufe ya sanya suka sake lumshewa suka kuma chanja colour daga aenahin colour d'in su zuwa ja, wani irin kallo yake bin Abbun dashi ido cikin ido wanda shi kan sa Abbun ze iya cewa tunda yake be ta6a ganin Rk d'in ya masa irin wannan kallon ba, saboda ya sani Rk d'in yaro ne me tarbiyya da sanin ya kamata amma yau shine ke kallan sa ido cikin ido duk kuma da Abbun ma shima kallan sa yake amma hakan be sanya shi ya janye k'wayar idanun sa ba, cikin murya me kauri kuma a d'an fusace ya furta bayan ya sake k'ank'ance idanun sa "Muneerah!!?" Hhh jama'a ina tunanin kamar yanzu wasan ze soma fa, nasan kan ku ya kulle sosae 🤧🥱 toh babu damuwa ku dae kawae ku cigaba da kasancewa da alk'alami na zaku ji yanda komae ze tafi..🌚😌 Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 029_030 ___Kallan sa Abbu har ma da Ummeen suka yi jin yadda yayi maganar kamar ba shi ba haka zalika idanun sa sunyi jawur fuskar sa babu annuri ko kad'an "Raj!" Abbu ya kira sunan sa ganin har lokacin idanun sa na kan su ne, se a lokacin ya lumshe idanun sa zuciyar sa na wani irin tafasa, haka jijiyoyin kan sa sun firfito saboda tsananin 6acin rae, a hankali ya bud'e idanun nasa da suka sake lumshewa sannan cikin k'arfin hali ya furta "Abbu Muneerah fa kace" "Ehh ko nayi sa6o ne bansani ba?" Abbu ya fad'a yana kafe shi da idanun sa, be sake bi takan kowa ba dan a yadda yake jin ran sa na suya komae ze iya faruwa ya mik'e duk da yadda yake jin d'an jiri jiri na d'ibar sa amma

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70