Chapter 16
Chapter 16
hankali tace "Yah Sadeeq, Yah Sadeeq.." a hankali ya shiga bud'e idanun sa da suka masa nauyi saboda wani azababben ciwon kae daya rik'e masa kae, kallan sa su duka suka yi sanda yake k'ok'arin tashi zaune kan kujerar, Yah Sadeeq ba gwanin raki bane dan haka kana ganin sa kasan da gaske rashin lafiya ce ta kama shi "Yah Sadeeq baka da lafiya?" Ayrah ta fad'a tana kallan sa da idanun ta da suka yi rau rau, seya jinjina kae kawae yana lumshe idanun sa "Kayi wanka se kazo kaci abinci ko zaka ji d'adin jikin ka" Umma ta fad'a tana kallan Yah Sadeeq, seya mik'e a hankali ya fita daga d'akin hannun sa dafe da k'irjin sa ya wuce toilet d'in yayi wanka sannan ya fito.. Tare suka ci ramar cikin kwano d'aya, yana ci Umma na lura da yadda yake ta 6ata rae alamar kawae ci yake babu taste a bakin sa, wani iri da yaji a k'irjin sa ya sanya shi d'aukar ruwan da Ayrah ta kawo yanzu ta ajiye ya kafa bakin sa ya fara sha, se dae kafin ya ida shan ruwan wani irin amae ya taso masa, dan haka babu 6ata lokaci kuma cikin hanzari ya jefar da cup d'in yayi waje, aekuwa ya dinga kwara aman kamar ransa ze fita, dukkan su biyo shi suka yi wajen cike da tausayawa babu ma Ayrah data fara matse k'walla saboda tausayin d'an uwan nata "Sannu" suka dinga jefa masa sanda Umma ta taemaka masa ya tashi ta k'arasa dashi zuwa parlourn nata, Abba ya kalle ta yace "Ina ga ki shirya kawae mu wuce asibiti.." Yah Sadeeq dafe da k'irjin sa yace yana d'an girgiza kansa dan shi kad'ae yasan yadda yake ji a cikin jikin sa "Abba bacci nake ji, a bari na tashi tukunna se muje don Allah" "Abba don Allah a barshi yayi bacci" Ayrah dake rik'e da hannun Yah Sadeeq ta fad'a, jinjina kae Abba yayi kana yace "Shikenan, kayi baccin.." babu musu Yah Sadeeq ya koma ya kwanta yana lumshe idanun sa k'irjin sa na bugawa da k'arfin gaske, cikin en mintuna kad'an wani nannauyan bacci yayi awon gaba dashi, duk da kuma baccin daya d'auke shi hakan be sanya ya d'auke hannun sa dake kan k'irjin sa ba, ita kuma Ayrah na zaune gefen sa har lokacin hannun sa cikin nata tana jin tausayin d'an uwan nata rabin jikin ta......... Mhiz Innocent.... ✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 009_010 ___Sosae jikin Yah Sadeeq yayi tsanani a daren ta yadda dole seda suka mik'a shi asibiti, da kud'ad'en da suka ragewa Abba a hannu dasu yayi amfani wajen bada kud'in gwaje gwaje da sauran abubuwan da ba za'a rasa ba, tashin farko aka tabbatar da Yah Sadeeq d'in na d'auke da chronic ulcer ne, ga kuma matsananincin zazza6in daya sake rufe shi a ranar, dan haka asibitin suka rik'e shi ya kwana acan d'in, magunguna sosae aka had'a masa wad'anda suka janyo k'arewar kud'in daya rage a hannun Abba tass, sosae Yah Sadeeq d'in yaji jiki ya rame dama ba wani jiki gare shi ba, kamar wanda ya shekara a kwance, seda yayi sati 1 sannan aka sallame shi, zuwa lokacin kam tuni Abba ya fara tunanin mafitar daze samar musu wadda zasu dinga samun abincin da zasu dinga ci da sauran kayan amfani na yau da kullum. Sanda suka dawo gidan ma seya zama na basu da komae na dangane da abinci, dan haka Abba beyi k'asa a gwuiwa ba ya nemi bashi a wajen ogan su na company kuma cikin ikon Allah ya bashi, da wannan kud'in suka yi amfani har zuwa k'arshen wata, sedae fa a cikin watan dama Ayrah ce kad'ae ke zuwa makaranta saboda Yah Sadeeq har lokacin be gama warkewa ba, itama kuma babu kud'in da za'a dinga bata na mota dan haka Abba da kansa ke raka Ayrahn har makaranta a k'afa sannan ya wuce company shi kuma. A cikin wannan d'an tsukun ne Ayrah tayi k'awa Zaenab a makarantar bokon nasu, wadda take cikin unguwar su d'an nesa kad'an da gidan su, sosae suka k'ulla k'awance wanda har hakan ya janyo Abba yasan mahaefin ta ya zamana suna gaesawa sosae kamar abokae, sanda Baban Zaenab d'in ya fahimci yadda Ayrahn ke zuwa makaranta a k'afa se be cewa Abba komae ba washe gari kawae yazo k'ofar gidan su Ayrahn ya d'auke ta da yake yana da babur wanda a shi yake d'aukar Zaenab ya kae ta makaranta, sosae Abba yaji dad'in hakan ya yiwa Baban Zaenab d'in godiya. Tun daga ranar ya kasance kullum Baban Zaenab d'in ke zuwa ya d'auki Ayrah su wuce makaranta tare.. Sanda Yah Sadeeq ya warke bayan doguwar rashin lafiyar da yayi Abba da kansa yaje wajen Baban Zaenab d'in ya sake masa godiya sannan ya fad'a masa zancen warkewar Yah Sadeeq d'in kuma shine ze cigaba da tafiya da Ayrah makaranta, dan zuwa lokacin abubuwa sun d'an yiwa Abba kyau ba kamar da ba, da farko Baban Zaenab d'in ya nuna k'in amincewar sa akan hakan, ya nuna ze cigaba da kae Ayrah tare da Zaenab makaranta, se da Abba ya ganar dashi sosae kafin ya hak'ura... Haka rayuwar tasu ta cigaba da kasancewa wataran su samu suci abinci wataran kuma se dae suyi hak'uri, ko kuma su samu suci abincin sau 2 a rana, harkokin yau da kullum kuma wasu se dae ayi hak'uri, idan kuma abu ya zama dole toh Abba kanyi iya k'ok'arin sa wajen samar da abun... _BAYAN WASU SHEKARU_ __A cikin shekarun da suka shud'e sosae abubuwa suka cigaba da faruwa, ta 6angaren su Ayrah dae babu wani chanji dan kuwa har zuwa lokacin Abba aekin Companyn nan yake yi, yayin da Yah Sadeeq ya gama Secondary School har da shekara 3 da wani abun ma amma saboda yanayin rayuwa yasa har lokacin be cigaba ba, se dae wani lokacin ya kan bi Abba Company ya d'an taemaka masa da wasu auyukan.. .. Shigowar ta gidan kenan da sallama sanye cikin Uniform riga da wando blue da kuma hijab me d'an girma fari, k'afar ta tana saye cikin wani takalmi sau ciki bak'i me d'an madaedaecin kyau, matashiyar budurwa er kimanin shekaru 15, fara k'all da ita, zuwa lokacin data fara zama budurwa sosae kyawun ta ya k'ara fitowa sosae, haka zalika hasken fatar ta ya k'aru, Umma dake zaune cikin d'aki tana cigaba da sak'ar wata hula da yanzun take yi tana d'an samun kud'i, ta amsa sallamar Ayrahn, k'arasawa Ayrah tayi zuwa cikin d'akin sannan ta zube akan ledar tsakar d'akin hannun ta kan k'afar ta tana k'ok'arin cire takalmin k'afar ta tace bayan ta d'an tura k'aramin bakin ta gaba "Washh Allah na" ta fad'a tana cigaba da cire takalmin ta, Umma da take kallan ta ta girgiza kae tace "Sannu malalaciya" dae_dae lokacin data gama cire takalmin ta juyo tana kallan Umma seta sake maraeraece fuska tana fad'in "Allah kuwa Umma na gaji da gaske" ta fad'a tana d'ora kanta akan cinyar Umman, ajjiye sak'ar hannun ta Umma tayi sannan tace bayan ta d'ora hannun ta akan Ayrah "Qualifying d'in ta fito?" seta tashi da sauri wani murmushi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70