Chapter 19
Chapter 19
fad'a bayan ta nemi waje ta zauna akan tabarmar dake shimfid'e a tsakar gida "Yawwah Ayrah.." Abba ya fad'a yana kallan ta, seta cigaba da zama har zuwa sanda Umma ta fito daga kitchen d'auke da plate a hannun ta wanda ta yiwa Abba kwad'on salad a cikin sa "Sannu" ya fad'a yana kallan ta da murmushi kan fuskar sa, Ayrah tace "Abba.." yace "Na'am" ya fad'a yana kallan ta yadda take lumshe manyan fararen idanun ta da alama bacci take ji "Abba dama zuwa nayi na fad'a maka.." seya cigaba da kallan ta sannan yace jin tayi shiru "Ina jin ki" "Wae gobe idan Allah ya kaemu ance muje da wani d'an gidan mu za'a min registration na Jamb" sosae Abban ya cigaba da kallan Ayrah, I zuwa yanzu haka kawae yaji rashin yadda ya d'arsu a ransa, dan haka dole yayi wani abun "Shima cewa suka yi zasu biya miki?" seta jinjina kae kawae "K'arfe nawa?" "Wae kafin k'arfe 2 dae.." seya jinjina kae shima kafin yace yana janyo plate d'in gaban sa "Toh shikenan, Allah ya kaemu gobe inaso naje wajen principal d'in ku" "Toh Abba seda safe.." ta fad'a tana mik'ewa, Umma ta bita da kallo sanda take shigewa d'akin ta bayan ta mata seda safe, seta dawo da kanta wajen Abba tace "Amma gaskiya makarantar nan idan hakane suna da kirki, kuma hakan ba k'aramin k'arawa d'alibae k'warin gwuiwa zeyi ba" "Sosae kuwa" Abba ya fad'a a ransa dae yana tunani ne. Washe_gari Abba tare suka fita da Ayrah zuwa makarantar tasu, sanda suka shigo cikin makarantar da k'afar su suke takawa zuwa ciki, jefi jefi Abba kan d'an yi mata tambaya ita kuma ta amsa masa, har zuwa sanda suka k'arasa inda office d'in principal yake, a dae_dae lokacin da Alhaji ke fitowa daga cikin office d'in principal d'in nasu yayi dae_dae da lokacin da wayar Abba ta fara ringing, seya zaro ta daga cikin aljihu yana barin wajen zuwa baya dan amsa wayar saboda hayaniya, yana juyawar shi kuma Alhajin ya ida fitowa, a take idanun sa suka yi tozali da kyakykyawar fuskar ta sanda take tsaye a wajen tana jiran Abba ya dawo su shiga Office d'in tare, seya bita da wani mayattacen kallo da idanun nasa yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa saboda k'aunar yarinyar "Yalla6ae.." wani dake gefen sa ya fad'a, se ya d'an yi firgigit ya juya yana kallan mutumin sannan ya rufe idanun sa ya bud'e kana ya saki murmushi yace a hankali "Idan na ganta wallahi ina loosing control d'ina ne.." yayi maganar sanda suke barin wajen zuwa inda motocin su ke ajjiye, suna wucewar Abba kuma ya ida wayar sa ya k'araso yana kallan Ayrah yace "Muje..".... Da sallama suka shiga Office d'in, principal dake zaune ya kalle su sannan yayi murmushi ganin Abba fad'i yake "A'ah sannun ku da zuwa" ya fad'a kamar wanda yaga wani hamshak'in mutumin, shi kansa Abba seda abin ya d'an so bashi mamaki amma ya fuske ya nemi waje ya zauna yayin da Ayrah ta zauna a k'asa, seda suka gaesa sannan Abba yace "Dama magana ce akan yarinyar nan" yayi maganar yana nuna Ayrah da kanta ke k'asa, sannan ya cigaba da fad'in "Abubuwa da dama sun faru se dae ban samu damar zuwa wajen ku ba, toh shiyasa a wannan karon nace bari nazo naji daga bakin ku.. Naji yau ma ance wae za'a biya mata kud'in registration na Jamb?" murmushi Principal yayi kana yace bayan ya had'e hannayen sa cikin juna "Ae wato Alhaji Ibraheem ka godewa Allah, Allah ya baka yarinya me hazak'a, saboda haka dan mun d'auki nauyin ta wannan ba komae bane, In Sha Allah ma zamu d'auki nauyin ta ne har ta gama karatu.." dukkan su se suka kalle shi suna jin wani irin farin ciki na ratsa ilahirin jikkunan su "Toh Alhamdulillah, Masha Allah, muna godiya sosae Principal, Allah ya k'ara arzik'i" Inji Abba "Ameen_Ameen.." .... A kwanakin da suka biyo ne Ayrah suka zana jarabawar Jamb d'in, babu wani dad'ewa kuma result d'in ya fito, cikin ikon Allah kuma ta doko point dae_dae da course d'in data ke so dama kuma a Neco ma ta fito da 9 credit, dan haka komae yazo cikin sauk'i, wani malamin su ne ya shige mata gaba bayan fitowar result d'in nasu wanda shima Alhaji ne ya sanya shi yin hakan, sosae suka yi fafutuka wajen sama mata admission har Allah yasa ta samu Medicine a A.B.U Zaria. Ba k'aramin farin ciki Abba, Umma, Yah Sadeeq har ma ita kanta Ayrahn suka yi ba sanda suka ji an sama mata Admission d'in ta hanyar wannan malamin nasu, amma sanda duk suka ji a inda ta samu Admission d'in se duk jikin su yayi sanyi. Umma dake zaune kan tabarma ta kalli Abba dake fad'in "Duk da naji dad'in wannan Admission d'in da aka samu, amma bana tunanin zan yadda Ayrah ta tafi har Zaria karatu, ina tunanin kawae a bashshi.." Yah Sadeeq da shima yake kusa da Abba yace "Abba ni ina ganin kawae a batta d'in ta tafi, tunda duk da k'arancin shekarun Ayrah tana da hankali.." ya k'arasa maganar yana kallan Ayrah gami da sakar mata murmushi, itama murmushin ta saki tana jin dad'in wannan yabon na Yah Sadeeq duk da dae ita kanta ji take kamar ta hak'ura da makarantar, dan bata masan yadda rayuwar ta zata kasance acan wani waje babu Umman ta, ba Abban ta sannan kuma ba Yah Sadeeq d'in ta ba, Umma taja doguwar ajiyar zuciya sannan tace "Abban su barin wannan Admission d'in kamar mun saka k'afa ne munyi fatali da damar mu, ina ganin meze hana tunda mun yadda da d'iyar mu, mu barta taje d'in idan yaso mu dinga binta da addu'a kuma mu dinga kae mata ziyara..?" shiru Abba yayi na wasu en dak'ik'u kana yace "Zan sake tunani.." daga haka be sake cewa komae ba.. A cikin satin Abba ya amince da zuwa makarantar Ayrahn, dan haka daga shi har Yah Sadeeq suka tashi tsaye sosae wajen fara siya mata abubuwan da zata tafi dasu, duk da ba wasu kaya ne na azo a gani ba amma dae sun samu sun siya mata abubuwan da suka san zata buk'ata.. Cikin d'an k'ank'anin lokaci aka gama komae, duk wasu abubuwa da suka kamata aka gama su daga 6angaren Abban har daga can 6angaren Alhaji.. ..... Zubewa yayi a k'asan carpet kansa a k'asa yana jira Alhajin ya gama wayar da yake yi, seda ya shafe wajen rabin awa yana wayar da duk da ganin wani ya shigo besa ya katse ta ba "Muttala ina jin ka" yayi maganar sanda yake aje wayar akan kujerar gefen sa "Yalla6ae jibi ne tafiyar tasu fa" murmushi yayi kana yace "Toh madallah, yanzu abinda za'ayi.. ga kud'i nan kaje duk inda ya dace ka siyo duk wani abu da kasan yarinya budurwa nada buk'ata idan zata je makarantar kwana.." ya fad'a yana ajje masa wasu uban kud'i a gaban sa "Toh shikenan, amma bana tunanin a had'a da kayan lokacin da zasu tafi can makarantar, inaga gwara daga baya kayan su bita.." jinjina kae Alhajin yayi sannan yace "Hakan ma yayi.." ya d'an dakata kana ya d'ora
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70