Skip to content

Chapter 57

Chapter 57

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

matsananincin tausayin ta ya mamaye shi, Allah sarki baewar Allah, ashe dae Ayrahn er halak ce, ta haefu cikin Umma da Abba, tana k'aunar farin cikin Abban ta dana Umman ta haka zalika kuma tana k'in abinda basa so, tunda gashi nan duk irin yawan k'aunar da take wa Raj daga ji iyayen ta basa son shi itama ta sauya masa "Amma pls ko zan iya sanin dalilin Abba na cewa bazan auri Ayrah ba?" tambayar data katsewa Yah Sadeeq tunani kenan, seya d'aga ido ya kalli Rk sannan ya girgiza kae yana kallan sa har lokacin yace "Kada ka nuna kamar wani baka sani ba mana!" iska Rk ya fesar daga bakin sa sannan yace "Wallahi ban sani ba!" ya fad'a dan ya cire duk wani kokwanto dake tattare da Yah Sadeeq d'in, shiru Yah Sadeeq yayi na en wasu sakanni, sam bega amfanin 6oyewar ba gwara ma ya fad'a masa ya sani d'in kada ya zaci haka kurum za'a hana shi auren ta ne bayan tana son shi yana son ta "Mahaefin ka.." Yah Sadeeq ya fad'a masa duk abinda ya faru kamar yadda ya sani, tun daga lokacin da suka zo hawa mota da kuma sanda suka dawo Kano, daskarewa Rk yayi akan kujerar da yake zaune yana cigaba da kallan Yah Sadeeq kamar wani sak'ago ko kuma wani mara wayo, anya kuwa Yah Sadeeq d'in yasan abinda ke fitowa daga cikin bakin sa? Shin me yake k'ok'arin cewa Abbun sa ya aekata? Anya kuwa ba ya fad'i hakan bane dan ya kawar dashi daga kan k'anwar tasa ba? A hankali ya shiga tariyo abinda Abbu ya fad'a masa da kuma wannan maganar da Yah Sadeeq d'in ke fad'a masa, seya shiga had'a su waje d'aya yaga ko iri d'aya ce, shin zasu zauna a mizani d'aya? Se dae ina, kwata kwata ba iri d'aya bace, sam babu ma ta inda suka had'u ko kad'an, toh kenan me yake faruwa?? Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 036 ___Ya d'auki wajen mintina 2 a haka, zuciyar sa a matuk'ar cunkushe, gaba d'aya ya rasa meke masa dad'i, duka tunanin sa ya tafi ne wajen tunanin menene gaskiyar abinda yake fitowa daga bakin Yah Sadeeq, shin me ya kamata ya amince da shi? Maganar Abbun sa ko kuma maganar Yah Sadeeq d'in? Iska me zafi ya fesar daga cikin bakin sa lokaci d'aya yana lumshe idanun sa, har lokacin kuma yana jin yanda zuciyar sa ke ta azalzalar sa "Yah Sadeeq ka tashi muje wajen su Abba" shine abinda Ayrah ta fad'a tana d'an jan hannun Yah Sadeeq d'in, kallan ta yayi sannan yace a nutse "Ina zuwa, yanzun zamu tafi.." ya k'are maganar yana maeda duban sa kan Rk da har lokacin ya gaza furta ko kalma d'aya, shi dae Yah Sadeeq abinda be fahimta ba shine..tsananin mamakin abinda Abbun nasa ya aekata ne ya sanya shi kasa furta komae ko kuma maganar ce tazo masa a bazata "Are u ohk?" Yah Sadeeq ya tambaya yana kallan yanda har lokacin idanun sa ke a lumshe, se a lokacin ya shiga bud'e manyan idanun sa a nutse wad'anda lokaci d'aya colour d'in su ya chanja, akan Yah Sadeeq d'in ya sauke su se dae har lokacin bece ko uffan ba in ban da jinjina kae kawae da yayi "Can i just go with her pls?" Yah Sadeeq ya fad'a har lokacin yana kallan Rk, a nutse ya d'aga kan sa ya kalli Ayrah dake zaune gefen Yah Sadeeq kamar bata san da zaman sa a wajen ba, dan kuwa har cikin ran ta tana ji in dae har Abba da Umma basu yafe mata ba ba zata ta6a yafewa Rk ba "Yeah" ya furta a hankali kamar wanda akawa dole, daga haka ya mik'e ba tare daya sake cewa komae ba ya fara barin wajen zuwa wajen motar sa, bin sa da kallo Yah Sadeeq yayi sanda yake barin wajen, gaba d'aya yanayin sa ya chanja cikin k'ank'anin lokaci wanda har hakan seda ya bawa Yah Sadeeq d'in mamaki, se dae hakan kad'ae ya isa ya nuna masa halin su ze iya kasancewa mabanbanta ne da shi da mahaefin sa. "Auta.." Yah Sadeeq ya fad'a yana kallan ta da murmushi saman fuskar sa, dan so yake ya d'an kawar mata da wata damuwar kamin su k'arasa gida, aekuwa yaci nasara dan kuwa seda tayi murmushin itama kafin ta sanya hannun ta akan fuskar ta ta goge hawayen fuskar ta still dae tana cigaba da murmushin "Tashi mu tafi.." ya fad'a bayan ya mik'e, babu musu ta mik'e suka bar wajen zuwa titi, suka samu abin hawa. A 6angaren Rk kuwa a nutse ya k'arasa wajen motar sa ya bud'e ya fad'a ciki, babu 6ata lokaci ya tayar da motar, sam gudu ba d'abi'ar sa bace amma yau seya tsinci kan sa da yin gudun sosae dan so yake ya samu nutsuwar da ze zauna yayi tunani akan wannan maganar, a haka har ya k'arasa gida. A compound d'in gidan yayi parking motar ta sa, ya sauka ya soma takawa zuwa part d'in sa, dae_dae lokacin da yake k'ok'arin sanya mukulli dan bud'ewa ya jiyo muryar Ummee na fad'in "Yanzu kake dawowa ne?" seya d'an dakata kad'an sannan ya d'aga idanun sa ya kalli Ummeen kana yace "Ehh.." kawae dan a yadda yake jin sa baya jin ze iya doguwar magana haka nan, kallan sa Ummee ta cigaba da yi tana nazarin yanayin sa "Kana lafiya kuwa?" Ummeen ta tambaya, nan ma da "Ehh" kawae ya amsa yana k'arasa saka key d'in ya bud'e ya tura kan sa cikin d'akin, bin sa da kallo Ummee tayi, se kuma ta juya itama da nufin shiga cikin d'akin nasa se kuma ta dakata ta girgiza kae kamin ta wuce part d'in ta. .. A hankali ya kwanta kan kujerar d'akin, sannan ya d'auki hannun sa d'aya ya d'ora a kan sa dake cigaba da masa ciwo, idanun sa a lumshe suke yana sake tuna maganganun Yah Sadeeq, be san dalilin da yasa ya kasa k'arya ta Yah Sadeeq d'in ba a lokacin da yake fad'a masa ga abinda mahaefin sa yayi, ya rasa dalilin hakan, haka kawae yake ganin babu abinda ze sa Yah Sadeeq d'in ya zauna ya d'irka k'arya akan mahaefin sa kuma yazo yana fad'a masa, abu ne me kamar wuya hakan ya faru, amma kuma ta yaya zeyi gaggawar amincewa ba tare da wata hujja ba? Duk da yana buk'atar bincike ko da akan takaddun Abba ne da Yah Sadeeq d'in yace Abbu ya tafi har dasu, amma kuma akwae abubuwa da dama da ke ta masa dirar mikiya cikin k'wak'walwar sa, tunda Abbu ya fita da niyyar raka Abba Kano, dawowar sa gida cikin gaggawa suka bar garin, tun daga lokacin be sake ganin Ayrah ko wani daga cikin dangin su ba, ko kuma wani abu daya shafe su ba, kenan me hakan ke nufi? Lokaci guda bugun numfashin sa ya k'aru, baya fatan ace haka d'in ne dan idan hakan ya tabbata gaskiya ne be san da wane ido ze kalli Ayrah da shi kan sa Abba ba, mutum me hallaci a gare shi, mutum me kirki da dattako, wanda tun a

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70