Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

kallan d'an uwa, kamar d'an uwan da suka fito ciki d'aya, yana ganin kamar ya samu wanda ze iya kular masa da dukiya koda baya wajen, wanda ze rik'e masa amana ko da a bayan idanun sa ne, se dae kashh ashe be sani ba duk wannan a banza ne, ashe Abbun ya yaudare shi ne da halayen bogi, yayi amfani da yaddar daya bashi ya yanke shi son ransa, ashe tun farko akwae k'udurin da yake son cikawa shiyasa ya kwantar da kae, ya nuna kamar shi na Allah ne "Meyasa zaka min haka Kabeeru?" Abba ya fad'a a fili yana dafe da k'irjin sa da har lokacin yake jin ya masa wani irin nauyi. ... Bin Abban tayi da kallo sanda ya shigo cikin gidan, a hankali ta bud'e baki ta amsa sallamar sa da taji yayi ta a hankali, seta mik'e tana goge hannayen ta daga cikin ruwan d'aurayar wanke wanke ta k'araso tana kallan sa tace "Sannu da zuwa Abban su" "Yawwah.." ya fad'a yana yin gaba, haka nan kawae taji zuciyar ta ta buga, seta lumshe idanun ta a ranta tana fatan Allah yasa ba wani mummunan abun ne ya faru ba, a hankali ta yaye labulen d'akin ta shiga da sallama seta nemi gefen gadon ta zauna tana cigaba da kallan sa tace "Ko na had'a maka ruwan wanka ne?" girgiza kae Abba yayi kafin yace "A'ah" cike da damuwa ta furta "Abban su lafiya dae koh?" Abba ya runtse idanun sa yana jin zafin abinda ze fito daga bakin sa "Kabeeru.." tun kafin Umma taji k'arshen maganar ta dafe k'irjin ta dan ita ta d'auka ko wani abun ne ya samu Kabeerun, se dae sa6anin abinda tayi tsammani se taji Abban yace "Kabeeru yaci amana ta, ya tattara kayan sa ya gudu da kud'ad'en nan da kuma takaddu na.." runtse idanun ta Umma tayi a ranta tana fatan ta bud'e idanu taga ba gaskiya bane abinda take ji a kunnuwan ta ko kuma ya kasance mafarki ne take yi, se dae har zuwa sanda ta bud'e idanun ta se taga Abban a yadda ta barshi "Anya kuwa Abban su?" ta fad'a cikin k'arfin gwuiwa, murmurshin takaeci Abba yayi wanda ake cewa yafi kuka ciwo kana yace "Tabbas haka ne, ban dawo gidan nan ba seda na bincika, har unguwar su naje aka tabbatar min a jiyan shima ya bar garin shi da iyalin sa" "Inna lillahi wa inna ilaehi rajiun" Umma ta shiga nanatawa tana kallan Abban tana jin da wani ne ya fad'a mata wannan zancen har abada ba zata ta6a yarda ba "Abban su.. Abbun Raj fa kake magana, mutumin da kullum zancen sa a bakin ka baya wuce na alkhaeri kirkin sa da kuma rik'on amanar sa, koda sau d'aya ban ta6a jin ka fad'i aebun sa ba, se dae gashi yau ina jin wata magana mara dad'i akansa tana fitowa daga bakin ka, Abban su kana nufin duka kud'ad'en nan ya gudu dasu don Allah.." "Toh ina suke Ruk'ayya? ae yanzu kinga irin sakayyar da yayi min na d'aukar amana ta da nayi na bashi koh?" wani numfashi me zafi Umma taja ta fesar sannan ta sake yin salati, daga nan kuma tayi shiru ta kasa cewa komae, dan kwata kwata ma bata san me za tace ba, mamakin ta d'aya yadda Abban da kansa yake fad'in Abbu ya gudu da kud'in sa, abin kamar almara, gaba d'aya k'wak'walwar ta ta tafi can tana mata bitar alak'ar Abban da kuma Abbu.... Sanda Yah Sadeeq yaji zancen nan seda yayi kuka sosae cikin tausayin Abban nasa, yana tuna irin gwagwarmayar da Abban yasha kafin ya samu wannan damar amma lokaci d'aya wani yazo yayi masa awon gaba da komae nasa, ya kuma yi alawadae da hali irin na Abbu, ya kalli Umma dake zaune ta jinginar da kanta kan kujera kamar me tunani "Umma bansan meyasa ba ni gaba d'aya daga shi Raj d'in har mahaefin sa ba suyi min ba Umma, Umma mutumin nan ya cuci Abba ya cuce mu, Allah ya isar mana wallahi" kallan sa Umma tayi, bata jin komae idan ta tattauna magana da Yah Sadeeq d'in dan k'ananun shekarun sa basu hana shi hankali ba, idan yayi wani abun kamar wani babban mutum tace "Bama seka fad'a ba Sadeeq, sakayya kam se Allah yayi mana ita, shi kuma yaje ya gani idan haram wata abace" dae_dae lokacin da Ayrah ta shigo d'akin ta k'arasa ta kwanta akan cinyar Umma kamar zata fashe da kuka ta furta "Umma Raj.." Yah Sadeeq dake zaune kujerar kusa da Umma ne ya janyo ta da k'arfi cikin fad'a yace "Wallahi idan kika sake mana maganar Raj a cikin gidan nan sena miki duka kinji na fad'a miki" ya fad'a yana d'aga hannu kamar ze mare ta, kuka ta fashe dashi kamar wadda ya ida dukan nata, Umma ta kae hannu ta rik'o ta ta d'auke ta zuwa kan cinyar ta ta kwantar sannan ta kalli Yah Sadeeq tace "Ita me ta sani? Wannan fad'an babu abinda ze janyo se rigimar ta kasan hali dae" "Umma ba duk itace ta janyo ba, da bata san Raj d'in bama ta yaya Abba ze had'u da baban sa ballantana har ya cuce shi" Umma na cigaba da rarrashin Ayrah tace a nutse "Ya zamu yi da k'addara Sadeeq?" ... Sau wajen 3 Umman na farkawa daga baccin da babu dad'i cikin sa se tarin damuwa da tunanun nuka tana ganin Abban zaune babu alamar zeyi bacci, se daga k'arshe dae ta kasa shiru tace "Kayi hak'uri Abban su don Allah kayi bacci, kada damuwa ta maka yawa.." Abba ya lumshe idanun sa, baya tunanin ko awa nawa zeyi zae iya yin wani bacci, amma dan ya kwantar mata da hankali ya sanya shi fad'in yana gyara zaman sa "Toh shikenan, yanzu zan kwanta kiyi baccin ki.." ... Wasa wasa wajen kwana 3 kenan Abban baya samun yin bacci, shi kansa besan dalili ba dan ko yayi niyyar yin baccin baya samu yazo masa, se dae kawae ya kwanta yayi ta tunani, zuwa lokacin tunani ya zama kamar wani mahad'in rayuwar sa ne dan kuwa in dae ze zauna toh fa zeyi tunanin nan ne, har kuma zuwa lokacin mamaki yak'i sakar shi, ga Kabeerun da kullum da shi yake kwana yake tashi, duk da guduwa da kud'in da Abbu yayi ya masa zafi amma be kae zafin yadda ya d'auki duk wata yadda tasa ya dank'awa Abbun ba amma daga k'arshe yaci amanar sa, ya yaudare shi, gefe guda kuma tunanin halin da zasu shiga a yanzun yake, yana ganin kamar rayuwa na gab da juya musu baya, babu sana'a, babu takaddar da ze iya zuwa ya nemi aeki, ga kud'in da Alhaji mato yake bin sa, duka tunanin sa yafi karkata nan 6arin ne "Allah ka bani ikon cinye wad'annan jarabobin" Abban ya fad'a akan la66an sa, yana jin wani irin rauni a tattare dashi.... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 007_008 ___Washe gari wajen k'arfe 8 na safe Abba na zaune cikin parlourn yana yin iya bakin k'ok'arin sa dan kada iyalan nasa su fahimci damuwar da yake ciki se ga kiran Alhaji

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70