Chapter 21
Chapter 21
janyo ta nemo number Yah Sadeeq ta danna kira, bugu 1_2 ya d'aga dan lokacin be kae ga yin bacci ba "Yah Sadeeq.." tayi maganar tana fashewa da wani marayan kuka a hankali, daga can 6angaren Yah Sadeeq ya girgiza kae yana murmushi dan yasan wannan kukan nata bana komae bane sena shagwa6ar data zame mata jiki "Auta rigima" ya fad'a yana murmushi, dae_dae sannan wayar Jidda tayi k'ara, taja tsaki daga inda take kwance tana amsa wayar ba tare da tasan me kiran ba, daga can 6angaren akace "Jidda don Allah kimin snapping aekin nan zanyi copying kafin gobe.." "Don Allah kiyi hak'uri Abeedah, ki koma kije kiyi bacci ko dan gobe ki samu shiga class d'in" banji me akace daga can 6angaren ba amma naji Jidda tayi dariya tace "Doctor RK fa.." daga inda Ayrah ke kwance ta d'an lumshe idanun ta tana jin yadda ta gaji da jin sunan da suke ta ambata tun d'azu, sunan da kusan duk hirar da suke tun d'azu a kansa ne suke yin ta, seta gyara kwanciyar ta ta kawae duk da tasan yau dae ba zata iya baccin ba... _*Yanzu wasan ze soma*_🥲 Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 013_014 ___Washe_gari tun asuba ta tashi tayi wanka ta gabatar da sallah sannan ta cigaba da zama kan carpet d'in da tayi Sallahr akae tana addu'a, bata dad'e da zama ba su Jidda ma suka farka kusan a tare, Jidda ce ta fara shigewa toilet yayin da Ruks da Bahijja suka tsaya a bakin toilet d'in kowacce na jira Jidda ta fito itama ta shiga. Tana nan zaune haka suka dinga sauri suna shiryawa kafin wajen k'arfe 7:30 dukkan su suka gama shiryawa kusan duk cikin dogayen riguna da k'ananan mayafae, Bahijja dake saka boot a k'afar ta tace "Kin gama shiryawa ne, ko har yanzu addu'ar ce ba'a gama ba?" tayi maganar tana kallan Ayrah, seta girgiza kae kafin tace "A'ah ku jira ni yanzu zan shirya" "Ayrah mun yi gaba, kiyi sauri ki shirya ki taho kafin 8 tayi" Ruks ta fad'a sanda take d'aukar jakar ta, jinjina kae kawae tayi ba tare da ta sake cewa komae ba, ta bisu da kallo sanda suke ficewa daga d'akin. A hankali ta mik'e ta sake fad'awa toilet ta wanko fuskar ta sannan ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atamfa kana ta saka hijab, ta d'auki sabuwar jakar da Yah Sadeeq ya siya mata wadda ta zuba littafan ta a ciki ta fito daga d'akin. A hankali take takawa a cikin filin makarantar cikin nutsuwar ta, duk da babu abinda ta shafa akan fuskar ta amma tayi kyau sosae, bayan ta d'auke da jakar goyo yayin da ta rungume wasu text books guda 2 wanda suma duk Yah Sadeeq ne ya siya mata saboda ta samu sauk'in karatu. Tun kafin ta k'arasa inda ze sada ta da ajin nasu taji shiru kamar babu mutane cikin ajin, har seda ta fara tantamar anya kuwa ba tayi 6atan kae ba?, dab da zata isa wajen ajin sassanya kuma daddad'ar muryar sa ce ta fara dakar mata kunnen ta, ba'a iya jiyo abinda yake fad'a d'in amma tana iya jiyo sautin yadda nutsatstsiyar muryar tasa ke fita, haka kurum taji k'irjin ta ya buga da wani irin k'arfi har seda ta dakata daga inda take tafe na wasu en mintuna kafin ta lumshe manyan idanun ta kana ta bud'e su tana mamakin yadda bugun zuciyar ta ya sauya cikin k'ank'anin lokaci. Da sallama akan la66an ta ta sanya k'afa cikin ajin nasu ba tare data kalli kowa ba, dan bata jin zata iya kallan kafatanin en ajin dan tasan duk idanun su na kanta ne "Hey!" nutsatstsiya, sanyayyiya kuma daddad'ar muryar sa me dad'in saurara ta daki dodon kunnen ta, a take kuma a lokaci guda k'afar ta ta d'auki rawa wanda har yanzun ta kasa gane dalilin wannan rawar da jikin nata ke yi "Ko dae da ita ake?" ta tambayi kan ta, gudun kada taje tayi laefi ya sanya ta dakatawa daga inda take, a hankali kuma ta shiga juyowa zuwa inda yake tsaye sannan ta d'aga raunannun idanun ta ta aza su inda ta tabbatar yana tsaye, ba ita yake kalla ba idanun sa na kan wani littafi dake gaban sa ne, kyakykyawa ajin farko, fari me kyakykyawan jiki kuma cikin kyakykyawar shiga, sanye yake cikin wasu riga da wando da suka dace da k'irar jikin sa, a saman kayan kuma suit ce itama me kyau, kansa babu komae se kwantacciyar bak'ar suma da tasha gyara na musamman, kamar yadda take a gyare haka kyakykyawan bak'in sajen sa ma yake a gyare kuma a kwance wanda hakan ba k'aramin k'arawa kyakykyawar fuskar sa kyau yayi ba, ganin da tayi ba ita yake kalla ba dan ita kanta bata ganin fuskar sa se gefen fuskar ta sa, seta d'an lumshe idanun ta kafin a hankali ta fara k'ok'arin juyawa "Hey, go out!" ya sake fad'a har lokacin be kalle ta ba, kawae se tayi shahada ta tabbatar da ita yake, har lokacin bata kalli kowa ba taja k'afafun ta ta fice daga ajin. Kae tsaye hostel ta koma har lokacin tana tuna sautin muryar sa a cikin kwanyar ta sannan kuma tana hana k'wallar data tarar mata a idanu zubowa, tana shiga ta ajjiye jakar ta ta haye kan gadon ta jinginar da kanta a jikin gado, iska ta fesar daga cikin bakin ta tana d'an jan numfashi kafin ta sanya hannu ta goge hawayen da suka fara sakkowa akan fuskar ta, a hankali ta cigaba da jan sheshshek'a tana jin wani irin zafi wanda da farko bata ji shi ba se yanzun, ta tsani yarfi, ta tsani dizgi, se gashi her first day in University wani yayi embarrassing na ta a baenar nasi, d'an mitsitsin bakin ta ta murgud'a kamar wani na kallan ta sannan tace akan la66an ta "Bashi da kirki". Tafi awa 1 a cikin hostel d'in seda ta kitanci lokacin da tasan ya fita sannan ta mik'e ta fita zuwa ajin nasu, cikin sa'a kuwa babu kowa cikin ajin a lokacin, se students kawae da kowa ke harkar gaban sa, koda ta shiga cikin ajin duk seta ji ta a takure musamman da taji a jikin ta idanun mutane da dama na yawo ne a kan ta, se take ganin kamar kowa kallan ta yake da wadda aka kora d'azu, duk se ta ji tana neman sark'ewa a tafiyar da take, gaba d'aya ma ta rasa inda za taje ta zauna, tsintsiyar hannun ta taji an kama se ta juya da sauri ta d'aga idanun ta ta kalli wadda ta rik'e mata hannun, Jidda ce, seta sauke ajiyar zuciya hadda lumshe idanun ta tana bud'ewa lokaci guda "Muje ki zauna" Jiddan ta fad'a tana cigaba da jan ta zuwa cikin ajin, babu musu kuwa kamar wata doluwa ta bita cike da sassarfa, wani dake zaune kan wani bench yace yana kallan Jidda "Hajiya Jidda an samu wata kenan?" seta juya ta watsa masa harara sannan tace "Shishshigi ba kwarjini" dariya yayi hadda dukan bench yace bayan ta wuce wajen "Yoh shishshigi kuma ya kae wanda kika
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70